Kalaman Trump kan Iran Sun Girgiza Kasuwar Danyen Mai Ta Duniya

Kalaman Trump kan Iran Sun Girgiza Kasuwar Danyen Mai Ta Duniya

  • Kasuwannin duniya sun fara ganin sauki ta fuskar farashin danyen mai biyo bayan saukar da ya yi a ranar Talata, 10 ga watan Maris, 2026
  • A ranar Litinin dai farashin danyen man ya kai farashi mafi kololuwa da aka taba gani a duniya tun watan Yulin shekarar 2026
  • Sai dai, bayan barazanar Shugaba Donald Trump da matakin da Ministocin kasashen Turai suka dauka, farashin danyen man ya fara sauka

​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Farashin danyen mai ya sauko zuwa $90 a kan kowace ganga a ranar Talata, 10 ga watan Maris 2026

Raguwar kudin danyen man fetur din ya kasance karon farko da farashin ya ragu tun bayan fara yakin Gabas ta Tsakiya.

Farashin danyen mai ya sauka a kasuwannin duniya
Wata rijiyar hakar mai a cikin teku Hoto: Ian Forsyth
Source: Getty Images

Jaridar The Cable ta ce danyen mai na Brent, wanda shi ne ma'aunin farashin mai na duniya, ya ragu da kashi 8.45% zuwa $90 kan kowace ganga.

Kara karanta wannan

Yakin Amurka da Iran zai rikita duniya, farashin litar fetur zai doshi N2000 a Najeriya

Shi ma danyen mai na Amurka (WTI) ya fadi da kashi 8.58% zuwa $86.77 kan kowace ganga.

A ranar Litinin, 9 ga watan Maris 2026 farashin danyen man a duniya ya haura $100 kan kowace ganga, matsayi mafi girma da aka taba gani tun watan Yulin shekarar 2022.

Dalilan saukar farashin fetur

Wannan raguwar farashin ta zo ne bayan da Ministocin kasashen Turai suka tattauna kan fitar da man da suke da shi a ajiye a matsayin wani mataki na dakile tashin farashin da aka gani kwanan nan a kasuwar duniya.

Haka kuma, saukar farashin ta biyo bayan wasu kalamai na Shugaban Amurka, Donald Trump, wadanda ke nuna cewa yaƙin Gabas ta Tsakiya na iya ƙarewa nan ba da jimawa ba.

Kalaman na sa sun rage fargabar katsewar hanyoyin samar da mai a duniya na tsawon lokaci.

Duk da haka, Trump ya yi gargaɗin cewa "mutuwa, wuta, da fushi za su auka a kansu (Iran)" idan suka kuskura suka dakatar da zirga-zirgar mai a mashigar ruwa ta Strait of Hormuz.

Kara karanta wannan

Wata sabuwa: Sanatocin Amurka sun kunnowa Trump wata wuta kan yaki da Iram

Martanin Iran kan barazanar Trump

Tashar Aljazeera ta ce a ranar Talata, rundunar dakarun kare juyin juya halin Iran (IRGC) ta mayar da martani ga Trump, inda ta ce ita ce za ta "yanke shawarar ranar da yaƙin zai ƙare.

Ta kuma bayyana cewa Tehran ba za ta bari a fitar da "lita ɗaya ta mai" daga yankin ba idan har Amurka da Isra'ila suka ci gaba da kai hare-hare.

Trump ya yi wa Iran barazana
Shugaban kasar Amurka, Donald Trump Hoto: Donald J. Trump
Source: Facebook

Tashin fetur ya yi tasiri a Najeriya

Yaƙin da ya haɗa da Amurka, Iran, da Isra'ila ya yi sanadiyyar tashin farashin mai a duniya, wanda hakan ya janyo karin farashin man fetur a Najeriya.

A sabon sauyin farashin da aka samu, matatar man Dangote ta ƙara farashin fetur ɗinta da N180, inda ya koma N1,175 kan kowace lita.

A ranar Litinin, 9 ga Maris 2026, David Bird, shugaban matatar, ya bayyana cewa matatar ba za ta iya tsira daga girgizar kasuwar duniya ba, domin tana sayen danyen man ta ne bisa farashin da ake sayar da shi a kasuwannin duniya.

Kara karanta wannan

Yakin Iran da Amurka ya kara taba Dangote, ya canza farashin fetur karo na 3 a Najeriya

Matatar Dangote ta kara farashin fetur

A wani labarin kuma, kun ji cewa matatar Dangote ta kara farashin da take sayar da man fetur ga 'yan kasuwa.

Matatar man Dangote ta kara farashin man fetur da Naira 101, inda ta kara farashin sayarwa daga N774 zuwa N875 kan kowace lita.

Karin farashi ya zo ne jim kaɗan bayan da matatar ta dakatar da loda man fetur tun tsakar daren 1 ga Maris, 2026, sakamakon tashin farashin ɗanyen mai a duniya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng