Trump na Maganar Kawo Karshen Yaki, Iran Ta Sake Harba Makamai Masu Hadari cikin Isra'ila

Trump na Maganar Kawo Karshen Yaki, Iran Ta Sake Harba Makamai Masu Hadari cikin Isra'ila

  • Sojojin Isra'ila sun tabbatar da cewa Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta sake harbo makamai masu linzami zuwa kasar
  • Rundunar sojojin ta bayyana cewa tuni tsarin kariya na sararin samaniya ya fara aiki domin kakkabo makaman da Iran ta harbo zuwa Isra'ila
  • Wasu rahotanni sun nuna cewa sojojin sun kakkbo daya daga cikin makaman Iran, yayin da wani ya kubuce ya fada teku a birnin Tel Aviv

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Isra'ila - Da safiyar yau Talata, 10 ga watan Maris, 2026, an gano cewa Iran ta sake harba makamai masu linzami zuwa kasar Isra'ila.

Wannan lamari na zuwa ne yayin da aka shiga rana ta 11 da fara musayar wuta tsakanin Iran da kuma hadin guiwar Amurka da Isra'ila.

Harin makami.
Yadda sojoji ke harba makami mai linzami a yakin Gabas ta Tsakiya Hoto: US Navy
Source: Getty Images

A wani rahoto da tashar Al-Jazeera ta wallafa yau Talata, an ji dakarun sojojin Isra'ila sun tabbatar da cewa sun hango makaman da Iran ta harbo zuwa kasar ta Yahudawa.

Kara karanta wannan

Iran ta sake harba makamai, ta yi wa yahudawa mummunar barna a Isra'ila cikin awanni 24

Isra'ila ta fara kokarin kare kanta

A wata sanarwa da rundunar sojojin Isra'ila (IDF) ta fitar, ta ce tsarin kariya na Isra’ila ya fara aiki domin kakkabo makaman kafin su kai hari.

"Mun gano cewa an harbo wasu makamai masu linzami daga Iran zuwa yankin kasar Isra’ila. Tsarin kariya na aiki domin dakile barazanar," in ji sanarwar.

Harin ya haddasa ƙararrawar gargadi a wasu sassan Isra’ila, inda aka umarci mutane su shiga wuraren kariya da mafaka.

Kafafen yada labaran Isra'ila sun ruwaito cewa kasar ta yi nasarar kakkabo daya daga cikin makamai masu linzami da aka harba daga Iran, yayin da wani ya fada cikin teku a Tel Aviv.

Sojojin Isra'ila sun maida martani

Rahotanni sun nuna cewa rundunar Isra’ila ta kuma kai hari kan na’urar harba makamai a Iran da ake zargin ita ce ta harba makaman da suka nufi Isra’ila.

Wannan sabon harin na daga cikin hare-hare da martani da Iran ke ci gaba da kai wa Isra’ila tun bayan da Amurka da Isra’ila suka fara kai hare-hare kan Iran a ranar 28 ga Fabrairu, wanda ya janyo rikici mai girma a yankin Gabas ta Tsakiya.

Kara karanta wannan

Babu sauki: Mayakan Hezbollah sun yi wa sojojin Isra'ila kwanton bauna, sun yi masu illa

Firaministan Isra'ila.
Firaministan kasar Isra'ila, Benjamin Netanyahu yana jawabi a taro Hoto: Gil Cohen-Magen
Source: Facebook

Wannan yaki ya dauki hankalin duniya musamman saboda yadda ya fara taba tattalin arziki da jefa mutane cikin wahala da kuncin rayuwa, kamar yadda NBC News ta kawo.

Yakin Iran da Amurka/Isra'ila ya jawo tashin danyen mai a kasuwannin duniya, lamarin da masana ke ganin farashin fetur zai ci gaba da hauhawa idan ba a dauki mataki ba.

Iran ta jikkata mutane a Isra'ila

A wani rahoton, kun ji cewa Ma'aikatar Lafiya ta Isra'ila ta bayyana irin barnar da hare-haren Iran suka haifar cikin awanni 24 da suka gabata a kasar ta Yahudawa.

Ma’aikatar ta ce mutum daya yana cikin mawuyacin hali yayin da mutane uku suka ji mummunan rauni sakamakon luguden wutar Iran.

Ta ce akalla mutane 191 ciki har da dakarun sojoji ne Iran ta jikkata a hare-haren da take ci gaba da kai wa cikin Isra'ila cikin sa'o'i 24 da suka wuce.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262