Iran Ta Sake Harba Makamai, Ta Yi Wa Yahudawa Mummunar Barna a Isra'ila cikin Awanni 24

Iran Ta Sake Harba Makamai, Ta Yi Wa Yahudawa Mummunar Barna a Isra'ila cikin Awanni 24

  • Ma'aikatar Lafiya ta Isra'ila ta bayyana irin barnar da hare-haren Iran suka haifar cikin awanni 24 da suka gabata a kasar ta Yahudawa
  • Bayanai sun nuna cewa Iran ta jikkata akalla mutane 191 a sababbin hare-haren da ta kai, kula cikinsu har da wasu sojojin Isra'ila
  • A baya an ruwaito cewa wani hari da makami mai linzami daga Iran ya kai ga mutuwar mutum guda tare da jikkata wasu biyu a birnin Yehud

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Isra'ila - Bayanai daga gwamnatin Isra'ila na nuna cewa Jamhuriyar Musulunci ta Iran na ci gaba da kai wa kasar Yahudawa manyan hare-hare da makamai masu linzami.

Wannan na zuwa ne yayin da aka shiga rana ta 11 da barkewar yaki tsakanin Amurka, Isra'ila da kuma Iran, lamarin da ya yi sanadin mutuwar daruruwan mutane.

Kara karanta wannan

Trump na maganar kawo karshen yaki, Iran ta sake harba makamai masu hadari cikin Isra'ila

Netanyahu.
Firaministan kasar Isra'ila, Benjamin Netanyahu Hoto: Anadolu
Source: Getty Images

Iran ta jikkata mutane 191 a Isra'ila

Tashar Al-Jazeera ta dauko rahoton cewa akalla mutane 191 ciki har da dakarun sojoji ne Iran ta jikkata a hare-haren da take ci gaba da kai wa cikin Isra'ila cikin sa'o'i 24 da suka wuce.

Ma’aikatar lafiya ta Isra'ila ce ta tabbatar da haka, inda ta sanar cewa mutane 191 na kwance a asibitoci daban-daban cikin awanni 24 da suka gabata sakamakon yakin da ake yi da Iran.

Jaridar The Times of Israel ta ruwaito cewa daga cikin wadanda aka kai asibiti akwai sojoji da fararen hula.

Ma’aikatar ta ce mutum daya yana cikin mawuyacin hali yayin da mutane uku suka ji mummunan rauni sakamakon luguden wutar Iran.

Jimillar wadanda aka raunata a yakin

Ma’aikatar lafiyar ta Isra'ila ta kuma kara da cewa mutane 2,339 ne aka kai asibitoci tun bayan fara yakin.

A cewarta, daga cikinsu akwai mutane 95 da har yanzu suna kwance a asibiti, yayin da 11 ke cikin mummunan hali.

Kara karanta wannan

Tofa: Rigima ta barke tsakanin Amurka da Isra'ila kan yaki da Iran, an ji dalilin sabanin

Iran.
Yadda ake musayar wuta tsakanin Iran da Isra'ila Hoto: Adadolu
Source: Twitter

Harin makami mai linzami a Yehud

A baya an ruwaito cewa wani hari da makami mai linzami daga Iran ya kai ga mutuwar mutum guda tare da jikkata wasu biyu a birnin Yehud da ke tsakiyar Isra’ila a ranar Litinin.

Harin na daga cikin jerin hare-haren makamai masu linzami da jirage marasa matuki da kasar Iran ke kaiwa Isra’ila a yayin rikicin da ke kara zafi a yankin Gabas ta Tsakiya.

Iran ta shirya yakin watanni 6

A wani rahoton, kun ji cewa sojojin rundunar juyin juya hali na Iran sun bayyana shirinsu na yin yaki mai tsanani da Isra'ila da ke samun goyon bayan Amurka.

Sojojin Jamhuriyar Musulunci ta Iran sun bayyana cewa a shirye su ke a ci gaba da fafata yaki mai tsanani da Amurka da Isra'ila har na tsawon watanni shida.

Wannan na zuwa ne bayan Firaministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu ya yi ikirarin cewa zai ci gaba da farmakar Iran da dukkan karfin kasarsa har sai ya kawar da shugabanninta.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262