Bayan Iran, Trump Ya Sake Gargadin Kasar Musulmi a Gabas ta Tsakiya
- Gwamnatin Donald Trump ta kara nausawa kasar Afghanistan yayin da ya ke kokarin tsayar da yakin da ya hada kai da Isra'ila ya afkawa Iran
- Ministan harkokin wajen Amurka, Marco Rubio ne ya fitar da sanarwa yana gargadin shugabannin Afghanistan, inda ya jero zarge-zarge
- A yanzu haka dai gwamnatin Amurka ta gargadi 'yan kasarta da zuwa kasar Afghanistan, inda ta ce shugabannin kasar 'yan kama karya ne
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
America - Gwamnatin shugaba Donald Trump ta ayyana Afghanistan a matsayin kasa mai daukar nauyin tsare mutane ba bisa ka’ida ba.
Rahotanni sun nuna cewa Amurka ta dauki matakin ne a ranar Litinin, 9 ga Maris 2026 domin hana kungiyar Taliban kama ‘yan kasarta.

Source: Getty Images
Tashar CNN ta wallafa cewa ministan harkokin wajen Amurka, Marco Rubio ne ya yi bayani game da zargin a madadin shugaba Donald Trump.

Kara karanta wannan
Akwai matsala: Majalisar Dinkin Duniya ta hango abin da zai faru sakamakon yakin Amurka da Iran
Zargin Amurka kan Afghanistan
Yayin da Trump ya fara magana kan kawo karshen yakin Iran, Amurka ta fitar da zarge-zargen kama mutane a kan kasar Afghanistan.
Rahotanni sun nuna cewa Afghanistan ce kasa ta biyu da Amurka ta ayyana da irin wannan zargi, kuma sanarwar ta zo ne a ranar gangamin hana kama mutane ba bisa ka'ida ba.
Gwamnatin Amurka ta ayyana Iran da irin wannan zargi kwana guda kafin ta kaddamar da hare-haren soji a kan kasar a karshen watan Fabrairun 2026.
Rahoton CBS News ya nuna cewa ministan harkokin wajen Amurka Marco Rubio ya ce:
“Taliban na ci gaba da amfani da dabarun ta’addanci, suna sace mutane domin neman kudin fansa ko kuma tilasta sauya manufofi.”
Ya kara da cewa:
“Dole a kawo karshen wadannan munanan hanyoyi.”
An hana Amurkawa zuwa Afghanistan
Rubio ya ce akwai hadari ga ‘yan Amurka su yi tafiya zuwa Afghanistan saboda Taliban na ci gaba da tsare ‘yan Amurka da sauran ‘yan kasashen waje ba bisa ka’ida ba.

Kara karanta wannan
Shugaba Trump ya bayyana sharadi 1 tak da zai iya kawo karshen yakin Amurka da Iran
Ya ce:
“Dole Taliban ta saki Dennis Coyle, Mahmoud Habibi, da dukkan ‘yan Amurka da aka tsare ba bisa ka’ida ba a Afghanistan nan take, kuma su yi alkawarin daina amfani da kama mutane a matsayin hanyar matsin lamba.”
Bincike ya nuna cewa an tsare Habibi ne a watan Agustan 2022 duk da cewa Taliban ba ta taba amincewa cewa tana rike da shi ba.

Source: Getty Images
Ma’aikatar harkokin wajen Amurka ta sanya tukuicin dala miliyan 5 ga duk wanda ya bayar da bayanin da zai kai ga gano inda yake, kubutar da shi da kuma dawo da shi lafiya.
Dan’uwan Habibi mai suna Ahmad Habibi ya ce ya gana wakilan gwamnati a ranar Litinin inda suka ba shi tabbacin cewa shugaba Trump ba zai bar dan’uwansa a tsare ba.
Amurka ta yi gargadi a Najeriya
A wani labarin, kun ji cewa ofishin jakadancin Amurka a Najeriya ya fitar da sanarwar gargadi game da yanayin tsaro a yankunan Najeriya.
Ofishin ya yi kira ga 'yan Amurka da ke Najeriya su tsaurara matakan kariya domin kaucewa afka musu idan wani rikici ya taso a kasar nan.
Gargadin ya zo ne a daidai lokacin da yakin Amurka da Iran ke kara daukar hankali da yadda Boko Haram ke zafafa hare-hare a Arewa maso Gabas.
Asali: Legit.ng
