Da Alama Amurka Ta Ji Wuta, Shugaba Trump Ya Hango Karshen Yaki da Kasar Iran

Da Alama Amurka Ta Ji Wuta, Shugaba Trump Ya Hango Karshen Yaki da Kasar Iran

  • Shugaban Amurka, Donald Trump ya yi ikirarin cewa sun kusa gama yaki da Iran saboda sun lalata wa kasar duk wani abu da take takama da shi
  • Trump ya bayyana haka yayin da ake ci gaba da musayar wuta tsakanin Amurka/Isra'ila da Jamhuriyar Musulunci ta Iran
  • Wannan kalamai ja Shugaba Trump sun saba wa ma'aikatar tsaron Amurka, wacce ta bayyana cewa yaki da Iran yanzu aka fara

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

America - Shugaban kasar Amurka, Donald Trump ya yi ikirarin cewa yakin Iran ya kuaa karewa saboda sun yi riga sun murkushe duk wani karfin sojin Jamhuriyar Musulunci ta Iran.

Trump ya jaddada cewa yakin da ake yi da Iran ya kusa karewa, yana mai cewa duk wani abu da Iran kw takama da shi na kargi ya lalace sakamakon hare-haren hadin gwiwar Amurka da Isra'ila.

Kara karanta wannan

Trump ya yi maganar tsayar da yaki da Iran bayan zaben magajin Khamenei

Shugaban Amurka.
Shugaban kasar Amurka, Donald Trump a fadar White House Hoto: @RealDonaldTrump
Source: Getty Images

A wata hira da tashar CBS News a ranar Litinin, Trump ya bayyana cewa:

“Ina ganin yakin ya kusan karewa. A yanzu ba su da rundunar sojin ruwa, ba su da sadarwa, kuma ba su da rundunar sojin sama, duk mun murkushe su."

Trump ya yi ikirarin samun nasara kan Iran

Ya kara da cewa makamai masu linzamin Iran sun kusa karewa, kuma Amurka da Isra'ila sun lalata jiragen yaki marasa matuka da kasar ke takama da su a ko’ina, har ma da wuraren kera su.

“Idan ka duba sosai, a yanzu ba su da komai a bangaren karfin soja,” in ji Trump.

Sai dai a lokaci guda, ma’aikatar tsaron Amurka, Pentagon, ta bayyana cewa duk hare-haren da kasar ta kai somin tabi ne, "yanzu Amurka ta fara wannan yaki,”

Wannan ya nuna yadda bangarorin gwamnatin Amurka suka yi sabani yayin da ake ci gaba da musayar wuta, kamar yadda Vanguard ta jawo.

Kara karanta wannan

Shugaba Trump ya bayyana sharadi 1 tak da zai iya kawo karshen yakin Amurka da Iran

Barazana kan mashigar Hormuz

Trump ya kuma yi gargadi ga Iran kan kokarin rufe mashigar mai ta duniya, wato Strait of Hormuz, inda jiragen dakon man fetur ke wucewa.

Ya ce yana tunanin karbe ikon mashigar daga hannun Iran, duk da cewa zirga-zirgar jiragen mai ta fara komawa a hankali a hankali.

Rufe mashigar zai iya jefa kasuwannin makamashi cikin gagarumar matsala domin kaso mai yawa na man fetur na duniya na wucewa ta nan.

Iran.
Marigayi tsohon jagoran addini na kasar Iran, Ayatollah Ali Khamenei Hoto; Jaafaru Sam
Source: Getty Images

Abin da Trump ya ce kan jagoran Iran

Trump ya kuma ce ba shi da wani sako ga sabon jagoran addinin Iran, Mojtaba Khamenei, wanda aka zaba bayan kashe mahaifinsa, Ali Khamenei.

“Ba ni da wani sako gare shi. Ko kadan,” in ji Trump.

A baya ma Trump ya bayyana rashin jin dadinsa da nadin Mojtaba Khamenei, yana mai cewa yana da wani daban a zuciyarsa wanda zai iya jagorantar Iran.

China ta yi gargadi kan jagoran Iran

Kara karanta wannan

Kasar Iran ta farmaki wani jirgin yaki, ta kara yi wa Amurka da Isra'ila babbar illa

A wani rahoton, kun ji cewa kasar China ta yi gargadi kan masu yunkurin farmakar sabon jagoran addini na Jamhuriyar Musulunci ta Iran, Mojtaba Khamenei.

China ta bayyana cewa nadin Mojtaba Khamenei a matsayin Jagoran Addini na Iran bayan kashe mahaifinsa lamari ne na cikin gida, bai kamata wani dan waje ya ji ba.

Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen China, Guo Jiakun, ya shaida wa manema labarai ranar Litinin cewa nadin Mojtaba Khamenei ya yi daidai da kundin tsarin mulkin Iran.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262