Ana tsaka da Yaki da Iran, an Jefa Abubuwan Fashewa a Kasar Amurka
- 'Yan sanda sun tabbatar da tarwatsewar wasu abubuwan fashewa a kusa da gidan magajin garin New York a Amurka, Zohran Mamdani
- An bayyana cewa an kai harin ne yayin da ake zanga-zangar adawa da kin jinin Musulmi a yankin, amma 'yan sanda sun kama wasu
- Mamdani ya yi magana da kakkausar murya yana tabbatar da cewa Birnin New York ba zai lamunci haka ba, yana cewa za a dauki mataki
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
America - Rundunar ‘yan sandan birnin New York (NYPD) ta ce an jefa wani abin fashewa yayin wata zanga-zanga a kusa da gidan magajin garin birnin New York, Zohran Mamdani, inda aka kama maza biyu.
Sanarwar da aka fitar a ranar Lahadi, 8 ga Maris, 2026 ta zo ne kwana guda bayan lamarin da ya faru a wajen gidan magajin garin.

Source: Getty Images
Al-Jazeera ta ce masu tsattsauran ra’ayi da ke nuna adawa da Musulmai, karkashin jagorancin Jake Lang ne suka yi arangama da wasu masu zanga-zangar adawa da su.
Bayanin 'yan sandan Amurka
Kwamishinar 'yan sandan New York, Jessica Tisch ta ce binciken farko ya nuna cewa abin da wani mutum ya jefa a wajen zanga-zangar abubuwan fashewa ne.
“Haƙiƙa abubuwan fashewa ne da aka kera ta hanyar gargajiya wadda za su iya haddasa munanan raunuka ko mutuwa,”
Inji ta, inda ta ƙara da cewa za a ci gaba da bincike kan na’urar da aka jefa, da kuma wata na’ura ta biyu da aka bari kusa da wurin.
Tisch ta ce an kama maza biyu a wurin, waɗanda aka bayyana sunayensu da Emir Balat da Ibrahim Kayumi kuma hukumar binciken manyan laifuka ta Amurka (FBI) ma ta shiga binciken.
Martanin Mandani kan harin Amurka
A cikin wata sanarwa da ya fitar a shafinsa na X, Mamdani ya yi Allah-wadai da zanga-zangar Lang, amma ya ce tashin hankalin da ya biyo baya ya fi muni.
“Rikici a zanga-zanga ba abin yarda ba ne,”
Inji shi.
“Yunkurin amfani da abubuwan fashewa domin cutar da wasu abin ƙyama ne kuma ya saba da abin da mu ka tsaya a kai.”
Wane ne Lang da ya shirya zanga-zangar?
Lang wani mai tsattsauran ra’ayi ne da aka kama a 2021 amma daga baya shugaba Donald Trump ya yi masa afuwa a bara, ya ce zanga-zangar da ya yi tana adawa da abin da ya kira maida New York birnin Musulunci.

Source: Getty Images
Mamdani shi ne magajin gari Musulmi na farko a tarihin birnin, wanda ake kiyasta yana da Musulmai kusan miliyan 1 a cikinsa.
Sojan Amurka ya mutu a harin Iran
A wani labarin, kun ji cewa wani sojan Amurka da har yanzu ba a bayyana sunan shi ba ya mutu a kasar Saudiyya bayan harin Iran.
Amurka ta bayyana cewa wasu makamai da Iran ta harba kan sansanin da ya ke ne ya jikkata shi sosai, wanda ya jawo mutuwarsa.
Rundunar sojin Amurka ta sanar da cewa a nan gaba kadan za ta sanar da duniya sunan sojan bayan magana da 'yan uwansa na jini.
Asali: Legit.ng

