Shugaban Faransa Ya Fara Kokarin Shawo kan Kasar Iran domin Tsayar da Yaki

Shugaban Faransa Ya Fara Kokarin Shawo kan Kasar Iran domin Tsayar da Yaki

  • Shugaban Faransa, Emmanuel Macron ya yi waya da shugaban Iran a kokarin ganin an dakatar da yakin da ya barke a karshen Fabrairun 2026
  • Ya bayyana haka yana mai cewa dole ne a samu mafita ta hanyar diflomasiyya wajen kawo karshen yakin da ake ta yi a Gabas ta Tsakiya
  • Rahotanni sun nuna cewa Emmanuel Macron ne shugaba a kasashen Yamma na farko da ya yi magana da Shugaban Iran tun bayan fara yakin

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Faransa - Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya kira takwaransa na Iran Massoud Pezeshkian a ranar Lahadi, inda ya bukaci a dakatar da hare-haren da ake kai wa kasashen yankin Gabas ta Tsakiya.

Macron ya bukaci a bude mashigar ruwa ta Hormuz domin zirga-zirgar jiragen ruwa. Ya kuma nuna damuwa kan shirin nukiliyar Iran yayin tattaunawar da suka yi da shugaban Tehran.

Kara karanta wannan

Iran ta fusata, ta kai hare hare Dubai, Saudiyya, mutane sun mutu

Massoud Pezeshkian da Emmanuel Macron
Shugaban Iran, Massoud Pezeshkian a hagu da Emmanuel Macron a dama. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Abin da Faransa ta fadawa kasar Iran

Bayan shafe sama da mako daya ana gwabza yaki tsakanin Iran da Amurka/Isra'ila, WIO News ta wallafa cewa Emmanuel Macron ya ce ya kira Massoud Pezeshkian sun tattauna.

“Na jaddada bukatar Iran ta dakatar da hare-haren da take kai wa kasashen yankin nan take,”

- Inji Macron a wani sako da ya fitar.

Ya kuma bukaci Iran ta tabbatar da ’yancin zirga-zirgar jiragen ruwa ta hanyar:

“Kawo karshen rufewar da aka yi wa mashigar Hormuz.”

An sako 'yan Faransa a kasar Iran

Macron ya kuma ambaci batun ’yan kasar Faransa biyu, Cécile Kohler da Jacques Paris, wadanda aka sako su daga gidan yarin Iran a watan Nuwamban 2025 sannan aka kai su ofishin jakadancin Faransa a Tehran.

Rahotanni sun nuna cewa an sake 'yan Faransan ne bayan fiye da shekaru uku da aka tsare su bisa zargin leken asiri, ya kuma bukaci a mayar da su kasarsu ta haihuwa.

Kara karanta wannan

Lamari ya rincabe: Saudiyya ta gaji da shiru, ta gargadi Iran kan hare-harenta

Kokarin Macron wajen tsayar da yaki

Macron ya kuma sake bayyana matukar damuwa kan ci gaban shirye-shiryen nukiliya da makamai masu linzami na Iran, yana mai cewa mafitar diflomasiyya kadai ake bukata.

Times of Israel ta ce Macron shi ne shugaban kasa daga kasashen Yamma na farko da ya yi magana da shugaban Iran tun bayan fara yakin da Amurka da Isra'ila suka kaddamar.

Biyo bayan wayar tarho da suka yi, Emmanuel Macron ya tabbatar da cewa dukkan shugabannin Faransa da Iran sun amince su ci gaba da tuntubar juna.

Emmanuel Macron da Donald Trump
Shugaban Faransa, Emmanuel Macron da Shugaba Donald Trump. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Ofishin Macron ya kuma bayyana cewa baya ga tattaunawa daban-daban da sarakunan Qatar da Kuwait da kuma shugabannin Masar da Azerbaijan a ranar Lahadi, Shugaban Faransa ya kuma yi magana da na Amurka Donald Trump.

Sojan Amurka ya mutu a Saudiyya

A wani labarin, kun ji cewa sojan Amurka ya mutu sakamakon raunukan da ya samu yayin hare-haren ramuwar gayya na farko da Iran ta kai.

Kara karanta wannan

Bayan kwanaki 7, Iran ta sauya salon yaki da Amurka, ta sassautawa Larabawa

Amurka ta ce sojan ya samu munanan raunuka ne yayin wani hari da aka kai a kasar Saudiyya a ranar 1 ga Maris kuma za a bayyana sunansa bayan an sanar da danginsa.

Wannan shi ne sojan Amurka na bakwai da ya mutu a yankin Gabas ta Tsakiya tun bayan fara yaki da Iran a ranar Asabar, 28 ga Fabrairun 2026.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng