An Harba Rokoki kan Dakarun Isra'ila, Sojojin Netanyahu Sun Mutu

An Harba Rokoki kan Dakarun Isra'ila, Sojojin Netanyahu Sun Mutu

  • An kashe sojojin Isra'ila a wani yanki na kasar Lebanon yayin da ake cigaba da gwabza yakin da Amurka ke tallafawa Tel Aviv a kan Iran
  • Sojojin Isra'ila sun shiga Lebanon a baya bayan nan suna kai farmaki wasu yankuna da sunan nemo gawar dan kasarsu da ya rasu a 1986
  • Hakan ya tayar da kura da jawo asarar rayuka da dama, inda mazauna yankunan da suka bayyana halin da suka shiga da fatan da suke

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Lebanon - Sojojin Isra’ila biyu sun mutu yayin sabon farmakin sojin kasar a Lebanon, wanda zuwa yanzu ya yi sanadin mutuwar kusan mutane 400.

An bayyana cewa su ne na farko daga bangaren Isra’ila da suka mutu tun bayan da kasar ta kara tsananta hare-hare kan kungiyar Hezbollah a Lebanon makon da ya gabata.

Kara karanta wannan

Hare haren Iran sun sake zama sanadin ajalin sojan Amurka a kasar Saudiyya

Benjamin Netanyahu a wani taro a Isra'ila
Firaministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu yana jawabi a Tel Aviv. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Yadda aka kashe sojojin Isra'ila

Rahoton Sky News ya ce mutanen biyu sun mutu ne lokacin da rokar da mayakan suka harba ta fadi kan rundunarsu, yayin da ake amfani da buldoza domin kokarin fitar da wata tanki da ta makale.

Rundunar tsaron Isra’ila (IDF) ba ta bayar da karin bayani nan take ba game da yadda lamarin ya faru duk da tabbatar da mutuwar sojojin.

An bayyana daya daga cikin sojojin da suna Maher Khatar mai shekaru 38, daga wani kauye a yankin Golan Heights da Isra’ila ta hade da kasarta, wanda yawancin mazaunansa kabilar Druze ne.

IDF ba ta bayyana sunan soja na biyu ba saboda har yanzu ana kokarin sanar da 'yan uwansa kafin a bayyana hoto da sauran bayanai game da shi.

Sojojin Isra'ila a kasar Lebanon
Yadda aka kaiwa sojojin Isra'ila a kasar Lebanon. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Isra'ila ta kutsa kasar Lebanon

Tashin hankali ya kara tsananta a kan iyakar Isra’ila da Lebanon tun bayan da Amurka ta kaddamar da hare-haren soji kan Iran fiye da mako guda da ya wuce.

Kara karanta wannan

Saudiyya ta shiga duniya neman kariya daga hare haren Iran

Sojojin Isra’ila kuma na gudanar da wani aikin soji a garin Nabi Chat da ke kudancin Lebanon domin neman gawar wani matukin jirgin Isra’ila mai suna Ron Arad, wanda ya bace a yankin tun shekarar 1986.

Maganar mutanen Lebanon

Magajin garin yankin, Saadallah Maatouk, ya ce mutane 14 daga cikin mazauna yankin sun mutu yayin da shida suka jikkata a hare-haren sojin Isra’ila cikin rana guda.

Reuters ta rahoto ya ce:

“Mutane 14 sun mutu sannan shida sun jikkata. Mun saba da hakan; wannan Isra’ila ce, kuma duk abin da ya faru ba zai shafe mu ba.”

Ministan lafiya na Lebanon ya ce yara 83 na cikin mutane 394 da suka mutu tun lokacin da rikicin tsakanin Isra’ila da kungiyar mayakan Hezbollah ya fara sama da mako guda da ya wuce.

Iran ta kashe sojan Amurka a Saudi

A wani labarin, kun ji cewa kasar Amurka ta sanar da mutuwar wani sojanta bayan makaman Iran sun afka masa a Saudiyya.

An kashe sojan Amurka ne 'yan sa'o'i bayan shugaba Donald Trump ya karbi gawar sojojin Amurka shida da Iran ta kashe a baya.

Yaki tsakanin Amurka da Iran ya kara tsananta tun bayan farmakin da Benjamin Netanyahu da Donald Trump suka kaddamar a Tehran.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng