Iran Ta Gigita Yahudawa, Ta Jefa Makami da ake Zargi Ya Tarwatse Isra'ila

Iran Ta Gigita Yahudawa, Ta Jefa Makami da ake Zargi Ya Tarwatse Isra'ila

  • Kasar Isra’ila ta fara binciken wani makami mai linzami daga Iran da ake zargin ya rabu gida-gida kafin ya fāɗi a Tel Aviv
  • Rahotanni sun nuna makamin na iya kasancewa nau’in da ke fitar da ƙananan bama-bamai bayan ya rabu a sama
  • Masu bincike na kokarin gano ko wannan alama ce ta sabon ci gaba a fasahar makaman Iran da su ke adawa da ita

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Tel Aviv, Israel – Hukumomin Isra’ila sun fara bincike kan wani harin makami mai linzami da ya afku a tsakiyar birnin Tel Aviv.

Ana zargin cewa makamin da ya zo daga Iran ya zo da sabon salo inda ya rarrabu zuwa sassa da dama kafin ya sauka a ƙasa.

Kara karanta wannan

Babbar magana: Ana tsaka da yaki da Iran, 'dan Majalisar Amurka ya dauko batun Najeriya

Isra'ila ta shiga bincike kan makamin Iran
Ana harba makami a yakin Amurka, Isra'ila da Iran, Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu
Source: Getty Images

The Times of Israel ta wallafa cewa ofishin yada labarai na gwamnatin Isra’ila ya bayyana cewa sun fara zargin ne bayan Iran ta harba masu wani makami mai linzami.

Isra'ila ta firgice bayan harin Iran

The Nation ta wallafa cewa wani kwamandan ‘yan sanda a yankin Tel Aviv ce abin da ya suna zargin wani makami mai linzami da aka aika kasar ya rabu gida-gida.

Ya ce:

” Sassan makamin na iya watsewa a sama kafin su sauka ƙasa."

Bayanin da jami’an suka bayar ya sa wasu masana ke ganin cewa makamin na iya kasancewa cikin nau’in makaman masu zuwa a daya sannan su rarrabu.

An fara bincike a kan makamin da Iran ta harba
Firaministan Isra'la Benjamin Netanyahu Hoto: Benjamin Netanyahu
Source: Facebook

Irin wannan makami na ɗauke da ƙananan bama-bamai da ke rabuwa daga babban makamin a sama, sannan su watse bayan fashewar farko.

A baya ma Isra’ila ta zargi Iran da amfani da irin waɗannan makamai a farkon rikicin da kuma lokacin yaƙin kwanaki 12 da ya faru a watan Yunin da ya gabata.

Kara karanta wannan

Akwai yiwuwar tsohon ministan Tinubu ya yake shi, yana kus kus da kusoshin adawa

Ana da shakku kan makaman Iran

Makaman 'cluster munition' sun haramta a ƙasashe fiye da 100 na duniya ta yarjejeniyar haramta amfani da su. Sai dai Iran, Isra’ila da Amurka ba su sanya hannu a yarjejeniyar ba.

A wurin da fashewar da ta faru a Tel Aviv, an ce masu bincike suna nazarin wasu tarkace da ake kyautata zaton sassan makamin ne.

Ya ce har yanzu ana ganin tarkace na sauka a tsakiyar Tel Aviv duk da cewa tsarin kariyar sararin samaniyar Isra’ila ya yi nasarar tare wasu makamai.

Ana ganin cewa ko da an harbo makamai da yawa, makami guda kaɗai na iya haifar da barna.

Gargadin Amurka ga kasar Iran

A baya, mun wallafa cewa Shugaba Donald Trump ya ce sabon jagoran addinin Iran ba zai daɗe a mulki ba idan bai samu amincewa daga kasar Amurka ba.

ShugabaTrump ya yi zargin cewa Iran na shirin mamaye Gabas ta Tsakiya baki ɗaya yayin da ƙasarsa da Isra'ila suka fara kai mata hari a makon da ya gabata.

Ya kuma ce Amurka ba ta cire yiwuwar tura sojoji na musamman domin kwace sinadarin uranium da ya dade yana tsone masu ido yayin da aka kaddamar da hari makon da ya gabata.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng