Iran Ta Fusata, Ta Kai Hare Hare Dubai, Saudiyya, Mutane Sun Mutu

Iran Ta Fusata, Ta Kai Hare Hare Dubai, Saudiyya, Mutane Sun Mutu

  • Kasar Iran ta kai hare-haren makamai masu linzami da jiragen yaki marasa matuki a kasashen Gulf kamar UAE da Qatar
  • A Dubai wani mutum ya mutu bayan tarkacen makami da aka harbo daga sama ya fadi kan mota a yankin Al Barsha yayin da UAE ke dakile hare-haren Iran
  • Iran ta ce hare-haren na nufin sansanonin sojin Amurka ne kawai, amma ta gargadi cewa duk kasar da ta bari a yi amfani da sararinta za ta zama hari

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Tehran, Iran - Kasar Iran ta ci gaba da kai hare-haren makamai masu linzami da jiragen yaki marasa matuki a wasu kasashen Larabawa.

Hakan na zuwa duk da alkawarin da shugabanta Masoud Pezeshkian ya yi cewa za ta kauce wa kasashe makwabta.

Iran ta sake kai hari kasashen Larabawa
Wakiliyar Qatar a Majalisar Dinkin Duniya, Sheikha Alia Ahmed bin Saif Al Thani Hoto: Mahmud Hams.
Source: Getty Images

Iran ta kai hare-haren ƙasashen Larabawa

Kara karanta wannan

Lamari ya rincabe: Saudiyya ta gaji da shiru, ta gargadi Iran kan hare-harenta

Shugaban Iran Masoud Pezeshkian ya bayyana cewa an umarci sojojin kasar su guji kai hari kan kasashe makwabta sai idan an fara kai hari daga yankunansu, cewar Al Jazeera.

Sai dai duk da wannan bayani, wani mutum ya mutu a Dubai ranar Asabar bayan tarkacen makami da aka harbo daga sama ya fadi kan wata mota.

Hukumomin Dubai sun ce lamarin ya faru ne a yankin Al Barsha, inda suka bayyana cewa mutumin da ya rasu direban mota ne daga wata kasa ta Asiya.

Lamarin ya faru da yamma ne lokacin da Hadaddiyar Daular Larabawa ta ce tana mayar da martani kan makamai masu linzami da jiragen yaki marasa matuki.

Iran ta kai hare-haren ramuwar gayya kan sansanonin sojin Amurka da ke kasashen Gulf ciki har da Bahrain, Qatar, UAE da Kuwait.

Kasashen Larabawa sun sha wuta daga Iran
Marigayi jagoran addini a Iran, Ali Khamenei. Hoto: @khamenei_ir.
Source: Twitter

Shugaban Iran ya ba makwabta hakuri

Bayan hare-haren, Pezeshkian ya ba kasashen makwabta hakuri, yana cewa manufar Iran ita ce kai hari kan sansanonin Amurka ne kawai.

Sai dai ma’aikatar tsaron Qatar ta ce rundunarta ta samu nasarar dakile wani hari da makami mai linzami da aka harba zuwa kasar, cewar CNBC.

Kara karanta wannan

Iran ta gamu da gagarumar matsala tana tsakiyar musayar wuta da Amurka/Isra'ila

A UAE kuma jami’ai sun ce na’urorin kariya daga makamai masu linzami suna dakile makamai yayin da jiragen yaki ke lalata jiragen marasa matuki.

A Saudiyya ma ma’aikatar tsaro ta ce an harba makami mai linzami zuwa sansanin sojin Prince Sultan kusa da Al-Kharj amma ya fadi a wurin da babu mutane.

Iran ta jaddada cewa hare-haren nata ba sa nufin take ikon kasashen Gulf, domin tana mai cewa sansanonin Amurka a yankin tamkar yankin Amurka ne.

Alaeddin Boroujerdi, dan majalisar Iran, ya ce tun kafin fara abin da ya kira “yakin Ramadan” Iran ta gargadi kasashen yankin kan yiwuwar kai hari.

Ya ce idan Amurka ta dauki matakin soja kan Iran, to sansanoninta a yankin za su zama makasudin hare-haren Iran.

Sai dai wasu kasashe kamar Qatar sun koka cewa hare-haren sun shafi matatun mai, otal-otal da filayen jiragen sama.

An kai karar kasar Iran kan hare-hare

An ji cewa Qatar ta tura wasiku biyu zuwa Majalisar Dinkin Duniya kan hare-haren da Iran ta kai kasarta musamman wurin da fararen hula ke zaune.

Kara karanta wannan

Akwai matsala: Kasar Qatar ta samu sabani da Iran a yakin da ya barke da Amurka da Isra'ila

Wakiliyar Qatar a Majalisar Dinkin Duniya ce ta mika wasikun, wadanda ke kunshe da korafin kasarta kan rikicin da ya barke tsakanin Iran, Amurka da Isra'ila

Ta yi ikirarin cewa Iran ta harba makamai masu linzami 83 da jirage marasa matuƙi 12 zuwa Qatar a jiya Asabar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com