Trump na tsakiyar Yaki da Iran: Bam Ya Tarwatse a Wani Ofishin Jakadancin Amurka
- An kai harin bam ofishin jakadancin Amurka dake birnin Oslo wanda hakan ya jawo hayaki mai kauri ya turnuke yankin da dan barna a ginin
- Rundunar yan sanda ta bayyana cewa tana bincikar harin a matsayin aikin ta'addanci domin taba Amurka sakamakon yakin da take yi da Iran
- Norway ta karfafa tsaro ga al'ummar Yahudawa a fadin kasar domin kauce wa karin wasu hare-hare a kan sansanonin kasashen waje
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Norway - An kai hari ofishin jakadancin Amurka dake birnin Oslo, babban birnin ƙasar Norway, inda wani abun fashewa ya tarwatse a daren jiya.
Fashewar ta haddasa baƙin hayaki mai kauri da ya mamaye titunan yankin ofishin da misalin ƙarfe 1:00 na dare, lamarin da ya tsoratar da mutanen wurin.

Source: Getty Images
An farmaki ofishin jakadancin Amurka

Kara karanta wannan
Bakin hayaki ya turnuke Tehran, Amurka ta yi wa Iran mummunar barna a karon farko
Kodayake harin bai yi sanadiyyar jikkatar kowa ba, amma ya jawo lalacewar wani bangare na ginin ofishin, yayin da jami'an tsaro suka kewaye yankin baki ɗaya domin gudanar da binciken gaggawa, in ji rahoton Aljazeera.
Rundunar ƴan sandan ƙasar ta bayyana cewa wannan fashewa na iya zama harin ta'addanci ne da aka tsara.
Shugaban sashen bincike na ƴan sandan Oslo, Frode Larsen, ya bayyana a wani taron manema labarai cewa babban zarginsu shi ne cewa wannan harin ganganci ne aka kai shi domin taɓa Amurka, la'akari da yanayin tsaron duniya a halin yanzu.
Sai dai ya ƙara da cewa suna bincikar wasu manufofin daban kafin su yanke hukunci na ƙarshe, kamar yadda rahoton CNN ya nuna.
An fara binciken harin ofishin Amurka
Larsen ya bayyana cewa dole ne su kasance a shirye don gano duk wata hanyar da ta kai ga faruwar wannan lamari, ko da kuwa ba ta da alaƙa da ta'addanci kai-tsaye.
Gwamnatin Norway ta tuntuɓi jami'an ofishin jakadancin inda ta bayyana harin a matsayin "abin da ba za a amince da shi ba".
Ministar Shari'a da Tsaron Jama'a ta Norway, Astri Aas-Hansen, ta tabbatar da cewa ana amfani da dukkan manyan jami'an tsaro da kwararru wajen binciken abubuwa masu fashewa domin gano waɗanda suka kitsa wannan harin.

Kara karanta wannan
Iran/Isra'ila: Matakan da gwamnatin Tinubu ke dauka kan 'yar Najeriya da suka makale
Kodayake ba a riga an kama kowa ba, hukumar tsaron sirri ta Norway (PST) ta ƙara yawan jami'anta yau don tabbatar da cewa ba a sake samun wani hari makamancin wannan ba.

Source: Getty Images
Norway ta tsaurara tsaro kan Yahudawa
Wani muhimmin mataki da ƴan sandan suka ɗauka shi ne ƙarfafa tsaro ga al'ummar Yahudawa dake cikin ƙasar Norway sakamakon wannan lamari.
Wannan hari na zuwa ne a daidai lokacin da dakarun Amurka da Isra'ila ke ci gaba da kai farmaki kan ƙasar Iran, rikicin da ya riga ya shafi ƙasashe da dama a yankin Gabas ta Tsakiya da ma duniya baki ɗaya.
Hukumomi sun tabbatar wa jama'a cewa komai yana ƙarƙashin iko, amma suna buƙatar kowa ya kasance cikin shiri da lura da duk wani abu da ba a saba gani ba a yankunansu.
Wuta ta tashi a ofishin jakadancin Amurka
A wani labari, mun ruwaito cewa, jirgi marar matuki ya daki ofishin jakadancin Amurka a Dubai inda aka samu tashin gobara kodayake babu asarar rayuka.
Sakataren harkokin wajen Amurka Marco Rubio ya tabbatar da cewa an kwashe kusan Amurkawa 9,000 daga Gabas ta Tsakiya.
A harin da Iran ta kai ofishin jakadancin Amurka, an ga bidiyon yadda wuta ke ci gadan gadan yayin da yakin ya shiga rana ta hudu.
Asali: Legit.ng