Iran Ta Fadi Illar da Ta Yi wa Amurka cikin Sa'o'i 24 a Yaki da Isra'ila

Iran Ta Fadi Illar da Ta Yi wa Amurka cikin Sa'o'i 24 a Yaki da Isra'ila

  • Rundunar IRGC ta Iran ta ce ta lalata na’urorin radar guda hudu da ke da alaka da tsarin kariyar makamai masu linzami
  • An ruwaito cewa an kai harin ne da makamai masu linzami masu bin diddigi wajen kai farmaki kan cibiyoyin kariyar makaman Amurka
  • Cibiyar THAAD na Amurka na daga cikin manyan na’urorin kare kai da ake amfani da su wajen gano da kuma dakile makamai masu linzami

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Tehran, Iran - Kasar Iran ta bayyana nasarar da samu a ci gaba da yaki tsakanin kasar da Isra'ila mai samun goyon bayan Amurka.

Ta ce rundunar Islamic Revolutionary Guard Corps (IRGC) ta lalata wasu na’urorin radar guda hudu da ke da alaka da tsarin kariyar makamai masu linzami na Amurka.

Iran ta fadi illar da ta yi wa Amurka
Marigayi jagoran addini a Iran, Ali Khamenei. Hoto: @khamenei_ir.
Source: Twitter

Rahoton A Jazeera, ya ce an lalata na’urorin ne cikin sa’o’i 24 bayan harba makamai masu linzami masu bin diddigi.

Kara karanta wannan

Bakin hayaki ya turnuke Tehran, Amurka ta yi wa Iran mummunar barna a karon farko

Iran ta razana Amurka da Isra'ila

Sojojin rundunar juyin juya hali na Iran sun bayyana shirinsu na yin yaki mai tsanani da Isra'ila da ke samun goyon bayan Amurka.

Firaministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu, ya yi alkawarin ci gaba da yakin domin kawar da shugabannin Iran bayan harin haɗin gwiwa da Amurka

A Beirut, harin Isra’ila a wani otel ya kashe akalla mutane 4, yayin da wasu suka ji rauni, kuma hotel ɗin na daukar ‘yan gudun hijira.

Illar da harin Iran ya yi ga Amurka

An bayyana cewa harin ya nufi muhimman cibiyoyin kariyar makamai na Amurka da ke amfani da tsarin THAAD a yankin, cewar Jerusalem Post.

Cibiyar THAAD, wato Terminal High Altitude Area Defense, na daga cikin muhimman tsarin kariyar Amurka wajen gano da kuma dakile makamai masu linzami masu nisan zango.

Wannan hari ya illata kasar Amurka duba wa tana amfani da cibiyar domin leko makamai masu linzami da ake harbawa daga ko ina lamarin da ya jawo suka daga ƙasashen.

Kara karanta wannan

Iran ta kada hantar Isra'ila, ta fadi tsawon lokacin da za ta yi tana yakarta

Iran ta raunana karfin Amurka
Jagoran addini a Iran da aka hallaka, Ali Khamenei. Hoto: @khamenei_ir.
Source: Twitter

Harin da ya hallaka Khamenei a Iran

Hakan na zuwa ne yayin da ake ci gaba kai munanan hare-hare tsakanin Iran da Isra'ila da ke samun goyon bayan Amurka.

Hare-haren Isra'ila sun yi wa Iran barna wanda har ya yi ajalin jagoran addinin Musulunci a kasar, Ayatollah Ali Khamenei a birnin Tehran.

Daga bisani, Iran ta mayar da martani inda ta farmaki wasu sansanonin sojin Amurka da ke kasashen Larabawa makwabtanta.

Amurka ta yi wa kasar Iran illa

A wani labarin, Amurka da Isra'ila sun farmaki rumbunan man fetur na Iran a karon farko inda aka kashe ma'aikata hudu tare da haddasa gobara.

Benjamin Netanyahu ya lashi takobin ci gaba da kai farmaki kan shugabannin Iran ba tare da jin kai ba domin ruguza tsarin mulkin kasar.

Zuwa yau, yaƙin ya yi sanadiyyar mutuwar mutane fiye da 1,300 a Iran, 300 sun mutu a Lebanon, sannan wasu mutane 12 sun mutu a kasar Isra'ila.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com