Ana Musayar Wuta, Trump Ya Fadi Abin da Zai Kawo Karshen Yakin Amurka da Iran
- Shugaban Amurka, Donald Trump, ya ce yaƙin Gabas ta Tsakiya na iya ƙarewa ne kawai idan aka rusa shugabancin Iran
- Shugaban Iran, Masoud Pezeshkian, ya ce wasu ƙasashe sun fara ƙoƙarin shiga tsakani domin sasanta rikicin, amma Trump ya nuna baya so
- Rikicin ya ƙara tsananta yayin da hare-haren Amurka da Isra’ila suka jawo asarar rayuka da lalacewar kayayyaki
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Washington DC - Amurka - Shugaban ƙasar Amurka, Donald Trump, ya yi magana game da yakin Iran da Isra'ila.
Trump ya bayyana cewa yaƙin da ke gudana a Gabas ta Tsakiya na iya ƙarewa ne kawai idan an lalata shugabancin Iran da kuma rundunar sojinta gaba ɗaya.

Source: Twitter
Trump ya magantu kan yakin Iran da Isra'ila
Trump ya bayyana hakan ne yayin da yake magana da manema labarai a cikin jirgin shugaban ƙasa, Air Force One, cewar SBS News.
Ya ce hare-haren sama da ake kai wa Iran na iya sa batun sulhu ya zama mara amfani idan aka kashe dukkan shugabannin da za su iya jagorantar ƙasar.
Ya ce:
“Wata rana ma ba za a sami wanda zai ce ‘mun mika wuya’ ba.”
A baya-bayan nan dai Trump ya bukaci Iran ta mika wuya ba tare da wani sharadi ba, lamarin da ya sa shugaban Iran, Masoud Pezeshkian, ya bayyana cewa wasu ƙasashe sun fara ƙoƙarin shiga tsakani domin kawo ƙarshen rikicin.
Pezeshkian ya ce wasu ƙasashe sun fara kokarin shiga tsakani, sai dai bai bayyana sunayensu ba ko kuma ƙarin bayani.
Trump ya kare babban aikin soji da Amurka ke yi a yankin, mafi girma tun bayan mamayar Iraq a 2003, yana mai cewa Iran na barazana ga tsaron Amurka, duk da cewa bai gabatar da wata hujja ba.

Source: Twitter
Amurka na tattaunawa kan tura sojoji Iran
Rahotanni sun nuna cewa Amurka da Isra’ila suna tattaunawa kan yiwuwar aika rundunar musamman zuwa Iran domin kwace tarin uranium mai matukar ƙarfi a wani mataki na gaba na yaƙin.
Lokacin da aka tambaye shi yiwuwar tura sojojin ƙasa domin kwace wuraren nukiliya, Trump ya ce hakan wani abu ne da za a iya yi a gaba, cewar BBC.
A wani bangaren kuma, shugaban Iran ya neman afuwar ƙasashen makwabta saboda hare-haren da Iran ta kai kan cibiyoyin sojin Amurka da ke cikin ƙasashensu.
Ya bukaci ƙasashen yankin da kada su shiga hare-haren Amurka da Isra’ila kan Iran, sai dai ya ce bukatar Trump na Iran ta mika wuya gaba ɗaya “mafarki ne kawai.”
A yayin da rikicin ke ƙara bazuwa, hare-haren da aka kai sun jawo mutuwar mutane da dama da lalacewar kayayyaki a Iran, Isra’ila da wasu ƙasashen yankin Gulf.
Switzerland ta tsoma baki kan yakin Iran, Isra'ila
Kun ji cewa ministan tsaron Switzerland ya ce hare-haren Amurka da Isra’ila kan Iran sun karya dokokin ƙasa da ƙasa.
Gwamnatin Switzerland ta bayyana cewa irin waɗannan hare-hare sun saɓa da dokar hana amfani da ƙarfi tsakanin ƙasashe.
Wasu manyan jami’an Turai da masana sun nuna shakku kan halaccin wannan yaƙi a dokokin duniya bayan Isra'ila da Amurka sun haɗa kai.
Asali: Legit.ng

