Yaki da Iran: Rigima Ta Barke tsakanin Amurka da Burtaniya, Trump Ya Nuna Fushi

Yaki da Iran: Rigima Ta Barke tsakanin Amurka da Burtaniya, Trump Ya Nuna Fushi

  • Shugaba Donald Trump ya soki kasar Burtaniya inda ya ce Amurka ba ta bukatar jiragen ruwan yakinsu domin samun nasara kan Iran
  • Rikicin diflomasiyya ya tsananta bayan Burtaniya ta hana Amurka amfani da sansanoninta domin kai hare-haren farko kan kasar Iran
  • Gwamnatin Burtaniya ta bayyana cewa tana duba yiwuwar tura jirgin yaki na Prince of Wales amma za ta dauki mataki bayan nazari

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Amurka - Shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana cewa ƙasar Burtaniya na "tunani mai zurfi" kan tura manyan jiragen ruwan yaƙi guda biyu zuwa yankin Gabas ta Tsakiya.

Sai dai, a cikin wani saƙo da ya wallafa, Trump ya ce Amurka ba ta buƙatar wannan tallafi domin cin yaƙin da take yi da Iran.

Kara karanta wannan

Iran ta gargaɗi Amurka, ta faɗi abin da zai faru da jiragen da Trump zai tura Hormuz

Ana ci gaba da takun saka tsakanin Amurka da Burtaniya kan yaki da Iran
Shugaban kasar Amurka, Donald Trump da Firaministan Burtaniya, Keir Starmer. Hoto: SAUL LOEB, Jonathan Brady / POOL / AFP via Getty Images
Source: Getty Images

Trump ya yi martani ga Burtaniya

Wannan shi ne babban rikici na baya-bayan nan tsakanin ƙasashen biyu waɗanda suka kasance manyan ƙawayen juna a baya, in ji rahoton Reuters.

Trump ya soki Firayim Minista Keir Starmer, inda ya bayyana cewa shugaban na Burtaniya ya taimaka wajen "lalata" kyakkyawar dangantakar dake tsakanin ƙasashen biyu.

Wannan fushi na Trump ya samo asali ne daga matakin da London ta ɗauka na hana Amurka amfani da sansanonin sojin Burtaniya wajen kaddamar da hare-haren farko kan Iran.

"Muna godiya Starmer, amma ba mu buƙatar jiragen ruwan naku kuma. Ba mu buƙatar mutanen da suke shiga yaƙi bayan mun riga mun yi nasara!" in ji Trump.

Burtaniya ta kare matakin da ta dauka

A gefe guda, ma'aikatar tsaron Burtaniya ta tabbatar da cewa tana shirya babban jirgin ruwan yaƙi na Prince of Wales domin yiwuwar tura shi yankin, kodayake ba a riga an yanke shawarar ƙarshe ba.

Kara karanta wannan

An kai wa Amurka dauki da kasar Iran ta matsa da kai hare hare da makamai masu hadari

Firayim Minista Starmer ya kare matakin da ya ɗauka na hana Amurka amfani da sansanonin soji na Burtaniya tun farko, inda ya ce dole ne ya tabbata cewa duk wani matakin soja ya bi ka'idar doka kuma an tsara shi yadda ya kamata.

Firaministan Burtaniya ya dage cewa kasarsa ba za ta iya taimakawa Amurka ba sai ta yi dogon nazari kan abin da ya dace.
Firaministan Burtaniya, Keir Starmer ya na magana a London a ranar 28 ga Fabrairu, 2026 bayan Amurka da ISra'ila sun farmaki Iran. Hoto: Jonathan Brady / POOL / AFP via Getty Images
Source: Getty Images

Tsamin alaka tsakanin Amurka da Burtaniya

Ministar Harkokin Wajen Burtaniya, Yvette Cooper, ta mayar da martani ga kalaman Trump a yau Lahadi, inda ta ce gwamnatinsu ba za ta biye wa kalaman rura wuta na dandalin sada zumunta ba, in ji rahoton The Economic Times.

Ta jaddada cewa Burtaniya za ta ci gaba da daukar matakan da suka shafe ta cikin nutsuwa, nazari, da kuma tsantseni maimakon amfani da kalaman soki-burutsu.

Tun farkon wannan shekarar dai, Starmer da Trump suka fara samun sa-in-sa bayan da Starmer ya soki kalaman Trump kan sojojin Turai da kuma sha'awar sa na siyan yankin Greenland.

Amurka ta fara amfani da sansanonin Birtaniya

A wani labari, mun ruwaito cewa, Amurka ta fara amfani da sansanonin soja na kasar Birtaniya domin kare kanta daga hare-hare a yaƙin da ake yi da Iran a Gabas ta Tsakiya.

Birtaniya ta sanar cewa Amurka ta fara amfani da wadannan wuraren domin ayyukan kariya na musamman da nufin hana Iran harba makamai zuwa wasu ƙasashen yankin.

Gwamnatin Birtaniya ta amince Amurka ta yi amfani da sansanonin soji guda biyu, da suka hada da RAF Fairford da kuma Naval Support Facility Diego Garcia.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com