Iran Ta Kada Hantar Isra’ila, Ta Fadi Tsawon Lokacin da Za Ta Yi Tana Yakarta
- Sojojin rundunar juyin juya hali na Iran sun bayyana shirinsu na yin yaki mai tsanani da Isra'ila da ke samun goyon bayan Amurka
- Firaministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu, ya yi alkawarin ci gaba da yakin domin kawar da shugabannin Iran bayan harin haɗin gwiwa da Amurka
- A Beirut, harin Isra’ila a wani otel ya kashe akalla mutane 4, yayin da wasu suka ji rauni, kuma hotel ɗin na daukar ‘yan gudun hijira
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Tehran, Iran - Sojojin Juyin Juya Halin Iran, IRGC sun yi magana kan ci gaba da yaki da ake yi tsakanin kasar da Isra'ila mai samun goyon bayan Amurka.
Rundunar ta ce a ranar Lahadi 8 ga watan Maris, 2026 ƙasar na iya yin yaki mai tsanani har tsawon watanni shida da Amurka da Isra’ila.

Source: Twitter
Mai magana da yawun rundunar IRGC, Ali Mohammad Naini shi ya tabbatar da haka a cikin wata sanarwa wanda Al Jazeera ta samu.
Barazanar da Iran ta yi ga Amurka, Isra'ila
Duk da wannan barazana, Gwardiyar Juyin Juya Halin ta ce a yanzu ƙasar na iya ci gaba da “yaki mai tsanani” har tsawon watanni shida a wannan yanayin.
Ali Mohammad Naini ya ce Iran ta yi amfani da makaman “farko da na biyu,” amma za ta yi amfani da makaman zamani masu nisa da ba a fi amfani da su ba a gaba.
Shugaban tsaro na Iran Ali Larijani ya zargi gwamnatin Trump da ƙoƙarin yin koyi da abin da ya faru a Venezuela inda aka kawar da shugaban Nicolás Maduro.
Ya ce:
“Sun yi tsammanin zai zama kamar Venezuela, za su kai hari, su karɓi iko kuma zai ƙare amma yanzu an makale su.”

Source: Twitter
Gargadin da Iran ta yi ga kasashen Larabawa
Shugaban hukuma mai tsauri Gholamhossein Mohseni Ejei ya kuma yi gargaɗi ga makwabtansu “a fili ko a ɓoye da ke bin umarnin abokin gaba” cewa “hari mai tsanani kan waɗannan wurare zai ci gaba.”
Shugaban ƙasa Masoud Pezeshkian ya ce Tehran “za ta tilasta mayar da martani” idan wata ƙasa makwabta za ta yi amfani da shi a matsayin tashar kai hari ko yunkurin mamaye ƙasar.
A Beirut, harin Isra’ila a wani otel ya kashe mutane akalla 4, yayin da wasu 10 suka ji rauni, cewar rahoton Times of Israel.
Hotel ɗin na ɗaukar ‘yan gudun hijira daga yakin kudu da Beirut da birnin gaba ɗaya, kuma wasu sun bar ginin don tsoron karin hare-hare.
Wannan shi ne karo na farko harin ya kai tsakiyar birnin tun bayan da rikicin Isra’ila da Iran ya sake barkewa makon da ya gabata.
Matan gwamnatin Najeriya kan yakin Iran/Isra'ila
An ji cewa Gwamnatin tarayyar Najeriya ta yi magana game da matakan da take dauka kan yakin da ke faruwa tsakanin kasar Iran da Isra'ila.
Gwamnatin ta bayyana cewa tana yin haka ne domin kare ‘yan Najeriya da ke Gabas ta Tsakiya sakamakon rikicin da ake yi a yau.
Ma’aikatar harkokin waje ta ce jakadun Najeriya a ƙasashen yankin an saka su cikin shiri na musamman domin sa ido kan halin da ake ciki.
Asali: Legit.ng


