Iran Ta Gamu da Gagarumar Matsala Tana tsakiyar Musayar Wuta da Amurka/Isra'ila

Iran Ta Gamu da Gagarumar Matsala Tana tsakiyar Musayar Wuta da Amurka/Isra'ila

  • An samu rarrabuwar kawuna tsakanin shugabannin Iran kan batun ba kasashen Gulf hakuri yayin da yake tsaka da yaki da Amurka
  • Bayan kisan gillar da aka yi wa Ayatollah Khamenei mako daya da ya gabata manyan malamai na gaggawar nada sabon jagora a yanzu
  • Dakarun kare juyin juya hali na IRGC sun yi watsi da kalaman sulhu na Shugaba Pezeshkian inda suka bukaci a ci gaba da yaki kawai

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Iran - Akwai alamun an samu baraka a tsarin mulkin kasar Iran a daidai lokacin da shugabannin kasar ke kallon yakin da ake ciki a matsayin babban kalubale ga rayuwarsu.

Akwai rarrabuwar kawuna mai tsanani tsakanin masu tsattsauran ra'ayi da kuma bangaren masu sassaucin ra'ayi, wanda ya fito fili bayan Shugaba Masoud Pezeshkian ya yi alkawarin daina kai wa kasashen Gulf hari.

Kara karanta wannan

Bayan kwanaki 7, Iran ta sauya salon yaki da Amurka, ta sassautawa Larabawa

An samu baraka a shugabancin Iran

Wannan baraka da aka dade ana dannewa a karkashin mulkin Ayatollah Ali Khamenei ta fito fili bayan kisan gillar da aka yi masa mako guda da ya gabata, in ji rahoton Reuters.

Ruwan harsashai da bama-bamai da Amurka da Isra'ila suke yi wa Tehran ya jefa Jamhuriyar Musulunci ta Iran cikin mawuyacin hali, wanda hakan ya sa dakarun kare juyin juya hali (IRGC) karbar ragamar tsara dabarun yaƙi.

Wannan na faruwa ne duk da cewa hare-haren Amurka da Isra'ila sun yi sanadiyyar mutuwar manyan kwamandojin dakarun da dama.

Majiyoyi daga cikin gidan gwamnati sun tabbatar da cewa, matsin lambar yaƙi ya sa jami'an dake raye sun kasa cimma matsaya ɗaya, inda rashin jituwa ya fara bayyana a tsakaninsu.

Takaddamar nada sabon jagoran Iran

Domin ceto tsarin mulkin ƙasar daga rugujewa, manyan malaman addini na ƙoƙarin gaggauta naɗin sabon Babban Jagora, inda ake sa ran yanke shawara a ranar Lahadi.

Kara karanta wannan

Martanin malaman addini 5 game da yaƙin Iran da Isra'ila a Gabas ta Tsakiya

Duk da cewa ana kallon ɗan Khamenei, Mojtaba Khamenei, a matsayin wanda zai iya gadon mahaifinsa tare da goyon bayan dakarun IRGC, akwai fargabar ko zai iya daidaita sahun ikon ƙasar.

Rashin gogewarsa a harkar mulki da kuma kasancewarsa ƙarami a idon manya na ƙara rura wutar adawa daga ɓangaren masu matsakaicin ra'ayi.

IRGC ta saba da shugaban Iran

Babban abin da ya fi tada ƙura shi ne ban-haƙuri da Shugaba Pezeshkian ya yi wa ƙasashen Gulf kan hare-haren da aka kai musu a makon jiya, in ji rahoton CBC.

Masu tsattsauran ra'ayi a cikin dakarun IRGC da majalisar dokoki sun soki wannan mataki da kakkausan harshe, inda suka siffanta shi a matsayin "rauni da rashin ƙwarewa".

Wannan matsin lamba ya tilasta wa Pezeshkian janye wasu kalaman na sa na haƙuri a cikin wata sanarwa ta baya-bayan nan.

Wannan tawaye ya nuna ƙarara yadda dakarun soja suke juya akalar siyasar ƙasar a halin yanzu, lamarin da ke nuna cewa shugabancin farar hula ya rasa tasirinsa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com