Kasar Iran Ta Gamu da Matsala, Isra'ila Ta Farmaki Jirage Sama da 15 a Tehran
- Dakarun rundunar sojojin Isra'ila sun yi ikirarin yi wa kasar Iran babbar barna a wasu hare-hare da suka kai birnin Tehran
- A wata sanarwa da suka fitar yau Asabar, sojojin Isra'ila sun lalata jirage 16 na rundunar juyin juya hali a filin jirgin sama na Mehrabad
- Daga cikin wuraren da Isra'ila ta yi ikirarin kai hari a Iran akwai cibiyar da ake bada umarni ta karkashin kasa da wurin ajiyar makamai masu linzami
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Israel - Sojojin Isra'ila sun sanar, a ranar Asabar, cewa sun kai hare-hare kan jiragen yaƙin Iran guda 16 a filin jirgin sama na Mehrabad International Airport da ke Tehran.
Kasar Isra'ila ta bayyana wannan filin jirgin da ke birnin Tehran a matsayin muhimmin cibiyar aiki ga dakarun juyin juya hali na Jamhuriyar Musulunci ta Iran.

Source: Getty Images
Hakan dai na kunshe ne a cikin wata sanarwa da dakarun sojojin Isra'ila suka fitar yau Asabar, 7 ga watan Maris, 2026, rana ta takwas da fara musayar wuta da Iran, in ji rahoton Channels tv.
Isra'ila ta ragargaji jiragen Iran 16
Sanarwar ta ce rundunar sojojin saman Isra’ila ta kai wani babban hari a daren jiya kan birnin Tehran tare da kai hare-hare kan wasu cibiyoyin soja da ke cikin filin jirgin sama na Mehrabad.
Sojojin Isra’ila sun ce sun lalata jiragen sama 16 na rundunar Quds Force, wani bangare na dakarun juyin juya hali, wadanda ke kula da ayyukan Iran a kasashen waje.
Isra’ila ta zargi Iran da amfani da filin jirgin Mehrabad, daya daga cikin manyan filayen jirgin sama biyu da ke aiki a Tehran, wajen aika kudade da makamai ga kungiyoyi da take goyon baya a Gabas ta Tsakiya.
Daga cikin kungiyoyin da Isra’ila ta ambata akwai kungiyar Hezbollah ta kasar Lebanon, cewar rahoton tashar Al-Jazeera.

Kara karanta wannan
Kasar Iran ta farmaki wani jirgin yaki, ta kara yi wa Amurka da Isra'ila babbar illa
Sanarwar ta kara da cewa hare-haren sun kuma shafi wasu jiragen yaƙin Iran da Isra’ila ta ce suna barazana ga jiragen rundunar sojin samanta masu aiki a sararin samaniyar Iran.
Jirage 80 na Isra'ila sun kai farmaki Iran
Tun da farko, sojojin Isra’ila sun ce fiye da jiragen yaƙi 80 sun kai jerin hare-hare kan sansanonin sojin Iran, makamai da sauran wuraren da ake zargi Iran tana amfani da su wajen kai hari.
Sanarwar ta ce hare-haren sun kuma shafi wata makarantar horas da sojoji mallakin Rundunar Juyun Juya Hali, wadda Isra’ila ta ce ana amfani da ita a matsayin cibiyar aikin gaggawa.

Source: Getty Images
Daga cikin wuraren da Isra'ila ta yi ikirarin kai hari a Iran akwai cibiyar da ake bada umarni ta karkashin kasa, wurin ajiyar makamai masu linzami d quraren harba makamai masu linzami.
Isra’ila ta ce ta kai wadannan hare-hare ne domin dakile yawan martani da lugudeen wutar da Iran take yi a kasarta da kuma sansanonin Amurka.
Qatar ta kai korafi kan hare-haren Iran
A wani rahoton, kun ji cewa Qatar ta tura wasiku biyu zuwa Majalisar Dinkin Duniya kan hare-haren da Iran ta kai kasarta musamman wurin da fararen hula ke zaune.

Kara karanta wannan
Iran ta harba makamai masu linzami kan babban birnin Isra'ila, an ji barnar da suka yi
Wakiliyar Qatar a Majalisar Ɗinkin Duniya, Sheikha Alia Ahmed bin Saif Al Thani, ta bayyana cewa ƙasarta na da haƙƙin mayar da martani kan hare-haren da Iran ke kai wa.
A cewarta, Iran ta harba makamai masu linzami 83 da jirage marasa matuƙi 12 zuwa Qatar a ranar Asabar, bayan hare-haren da Amurka da Isra'ila suka kai Tehran.
Asali: Legit.ng
