Tirkashi: An Ji Maƙudan Kuɗin da Amurka Ke Kashe wa Kullum a Yaƙi da Iran
- Operation Epic Fury ya lakume wa kasar Amurka fiye da dala biliyan biyar a cikin kwanaki hudu na farkon yaki da kasar Iran
- Amurka ta rasa na'urar radar dake Qatar da darajarta ta haura dala biliyan daya sakamakon harin makami mai linzami daga Iran
- Amurka na kashe kudaden da suka kai dala miliyan 758 a kowace rana domin mayar da makaman da ta yi amfani da su a yakin
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Amurka - Harin "Operation Epic Fury" ya lakume wa rundunar sojin Amurka akalla dala biliyan 5.82 a cikin kwanaki hudu, wanda hakan ke wakiltar 0.69% na daukacin kasafin kudin tsaron kasar na shekarar 2026.
Rahotanni sun nuna cewa, yayin da aka kashe dala biliyan 3.3 wajen kai hare-hare a Iran, Amurka ta yi asarar wasu muhimman makamai da kayayyakin yaki da darajarsu ta kai dala biliyan 2.52.

Kara karanta wannan
Tofa: Ana cikin yaki da Iran, Amurka ta tsallake majalisa don faranta ran Isra'ila

Source: Twitter
Wadannan makudan kudi ne la'akari da cewa Amurka ta kashe kusan dala miliyan 779 a cikin sa'o'i 24 na farkon fara yaki da Iran, in ji rahoton Aljazeera.
Jiragen Amurka da kasar Iran ta lalata
A yayin yakin, Iran ta lalata wa Amurka babban rumbun na’urar radar nan ta zamani mai suna "AN/FPS-132" dake sansanin Al-Udeid a kasar Qatar, wadda darajarta ta kai dala biliyan 1.1 a ranar Asabar.
Haka kuma, a ranar Lahadi, wasu jiragen yaki guda uku samfurin F-15E Strike Eagles sun fado kasa sakamakon kuskuren harbi daga na’urar kariya ta kasar Kuwait, wanda hakan ya lakume dala miliyan 282.
Jami’an Amurka sun kuma tabbatar da cewa an kakkabo jirage mara matuki guda uku samfurin MQ-9 Reaper wadanda kudinsu ya kai dala miliyan 90.
Na'urorin kariyar Amurka da aka lalata
Harin na Iran bai tsaya a nan ba, domin kuwa ta kai farmaki hedkwatar rundunar sojin ruwa ta biyar ta Amurka dake Manama, Bahrain, inda aka lalata na’urorin sadarwa na tauraron dan adam guda biyu.

Kara karanta wannan
Kasar Iran ta farmaki wani jirgin yaki, ta kara yi wa Amurka da Isra'ila babbar illa
Haka kuma, hotunan tauraron dan adam sun nuna barnar da aka yi a sansanin Camp Arifjan dake Kuwait, inda aka lallata wasu na'urorin kariya guda uku.
Akwai kuma rahoton lalata na’urar radar THAAD, wadda duk guda daya ta kai darajar dala miliyan 500 a Hadaddiyar Daular Larabawa da kuma wata makamanciyarta a kasar Jordan.

Source: Twitter
Iran: Dalolin udin da Amurka ta kashe
A bangaren kashe kudaden yaki, cibiyar CSIS ta wallafa a shafinta cewa Amurka na kashe kusan dala miliyan 758.1 a kowace rana domin sayan makaman da aka yi amfani da su, in ji rahoton
Jiragen ruwan yakin nan guda biyu, USS Abraham Lincoln da USS Gerald R. Ford, su ma suna lakume dala miliyan 15 a kowace rana yayin da suke kai hare hare.
Rundunar sojin Amurka ta yi amfani da dimbin makaman kakkabo na’urorin yaki irin su Patriot kusan guda 90 da kuma THAAD guda 40 domin dakile hare-haren Iran.
Wannan asara ta hada da makaman linzami guda 180 na kariya daga sojojin ruwa wadanda aka harba domin dakile farmaki.

Kara karanta wannan
Iran ta harba makamai masu linzami kan babban birnin Isra'ila, an ji barnar da suka yi
Amurka ta nemi taimakon Ukraine
Kun dai ji cewa, Gwamnatin Donald Trump ta nemi taimakon Ukraine don amfani da kwarewarsu wajen kakkabo jiragen Iran dake addabar kasashen Gulf.
Volodymyr Zelensky ya amince da bukatar Donald Trump amma da sharadin Amurka za ta ba Ukraine na'urorin kariya na Patriot domin yaki da Rasha.
Kasashen duniya na fargabar wannan sabon yakin zai dauke hankalin Ukraine yayin da Rasha ke samun kudin shiga daga tashin mai.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng