Akwai Matsala: Majalisar Dinkin Duniya Ta Hango Abin da Zai Faru sakamakon Yakin Amurka da Iran

Akwai Matsala: Majalisar Dinkin Duniya Ta Hango Abin da Zai Faru sakamakon Yakin Amurka da Iran

  • Shugaban Majalisar Dinkin Duniya, António Guterres ya bukaci Amurka, Isra'ila da Iran su tsagaita wuta, su koma teburin tattaunawa
  • Guterres ya ce matukar ba a gaggauta magance yakin da ya barke a Gabas ta Tsakiya ba, to zai iya kai wa matakin da zai fi karfin kowa
  • Kasar Iran dai ta sha nanata cewa ba ta neman yaki da rikici da kowa, amma za ta dauki duk matakin da ya dace domin kare 'yancinta

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

America - Shugaban Majalisar Dinkin Duniya, António Guterres, ya yi gargaɗin cewa rikicin da ke faruwa a yankin Gabas ta Tsakiya na iya rikidewa ya fi karfin kowa idan ba a dauki mataki ba.

Wannan gargadi na zuwa ne yayin da yaki ke kara zafi tsakanin hadin gwiwar Amurka da Isra'ila da kuma Jamhuriyar Musulunci ta Iran.

Kara karanta wannan

Yadda Rasha ke taimakon Iran wajen ragargazar dakarun Amurka a fagen yaki

Guterres.
Shugaban Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Guterres a taron kasa da kasa Hoto: Marco Simoncelli
Source: Getty Images

Premium Times ta ce a cikin wata sanarwa, Guterres ya ce hare-haren da ake kai wa juna a yankin da ma sauran wurare na haifar da babbar matsala ga fararen hula, tare da haddasa mummunar illa.

Abin da rikin Iran da Amurka zai haifar

Ya kuma yi gargadin cewa rikicin na iya haifar da babbar barazana ga tattalin arzikin duniya, musamman ga mutanen da suka fi rauni a ƙasashe masu tasowa.

“Lamarin na iya rikidewa ya fi karfin kowa. Lokaci ya yi da za a dakatar da faɗa kuma a koma kan teburin tattaunawar diflomasiyya,” in ji Guterres.

A halin yanzu dai ana ci gaba da musayar wuta tsakanin Amurka, Isra'ila da Iran. Rikicin ya shiga rana ta takwas a yau Asabar, kamar yadda France 24 ta rahoto.

Babban jami’in kula da ayyukan agajin gaggawa na Majalisar Ɗinkin Duniya, Tom Fletcher, ya ce duniya na cikin wani mawuyacin lokaci, wanda ke nuna hadarin da ke tunkarowa.

Kara karanta wannan

Kasar Iran ta farmaki wani jirgin yaki, ta kara yi wa Amurka da Isra'ila babbar illa

Ya bayyana damuwa kan yadda ake kashe kuɗaɗe masu yawa wajen yaƙi, yayin da a lokaci guda wasu ‘yan siyasa ke zaftare kuɗin agaji ga mutanen da suka fi buƙata.

Yadda yakin Iran zai lalata harkokin jin kai

Hukumar kare haƙƙin ɗan Adam ta Majalisar Ɗinkin Duniya, ƙarƙashin jagorancin Volker Türk, ta ayyana rikicin a matsayin babbar matsala ga harkokin jin ƙai, wacce ke buƙatar a magance ta cikin gaggawa.

Türk ya yi gargaɗin cewa rikicin na ci gaba da yaɗuwa zuwa wasu kasashe fiye da waɗanda suka fara musayar wutan tun farko, yana mai kira ga ƙasashe su ɗauki matakan rage tashin hankali.

Netanyahu da Khamenei.
Firaministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu da tsohon Jjagoran addinin Iran, Ayatollah Ali Khamenei Hoto: Ilia Yefimovich
Source: Getty Images

A nasa ɓangaren, wakilin Iran a Majalisar Ɗinkin Duniya, Amir Iravani, ya ce ƙasarsa ba ta neman yaƙi ko ƙara tsananta rikici, amma ba za ta taɓa miƙa wuya ga duk wani hari kan ikon ƙasarta ba.

Trump ya gindaya sharadin zaman lafiya da Iran

A wani rahoton, kun ji cewa Shugaba Donald Trump na kasar Amurka ya bayyana cewa mika wuyan Iran ba tare da sharadi ba ne kadai zai kawo karshen yakin da ya barke.

Kara karanta wannan

Rasha ta fadi dalilin da ya sa ba ta kai dauki ga Iran ba a yakinta da Isra'ila

Wannan furuci na Trump ya zo ne a lokacin da Isra’ila ke ci gaba da kai hare-hare kan wuraren gwamnati a birnin Tehran na Iran.

Trump ya ƙara da cewa idan Iran ta amince da wannan sharadi na mika wuya, Amurka da ƙawayenta za su taimaka wajen farfaɗo da tattalin arzikin ƙasar.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262