Tofa: Ana cikin Yaki da Iran, Amurka Ta Tsallake Majalisa don Faranta Ran Isra'ila

Tofa: Ana cikin Yaki da Iran, Amurka Ta Tsallake Majalisa don Faranta Ran Isra'ila

  • Gwamnatin Amurka ta yi abin da zai faranta ran Isra'ila yayin da ake ci gaba da gwabza fada a yankin Gabas ta Tsakiya
  • An tsallaka bukatar neman amincewar majalisa domin ganin Isra'ila ta ci gaba da yakin da take yi ta hanyar samun makamai
  • Amincewar dai na zuwa ne yayin da Amurka da Isra'ila ke fafatawa da Iran bayan sun kaddamar da hare-hare a kanta

​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Birnin Washington, Amurka - Gwamnatin Amurka karkashin Donald Trump ta amince da yiwuwar sayar wa Isra'ila makaman da darajarsu ta kai $151.8m.

Gwamnatin ta Donald Trump ta yi amfani da ikon "gaggawa" domin kauce wa bukatar amincewar majalisa yayin da Washington da Tel-Aviv ke ci gaba da kai hare-hare kan Iran.

Amurka da amince da sayar da makamai ga Isra'ila
Firaministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu da Shugaban kasar Amurka, Donald Trump Hoto: @netanyahu, @realdonaldtrump
Source: Twitter

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da ofishin harkokin siyasa da soja na ma'aikatar wajen Amurka ya fitar ranar Juma'a, 6 ga watan Maris 2026.

Kara karanta wannan

Yaki ya yi zafi, harin Hezbollah ya rutsa da dan babban Minista a Isra'ila

Wadanne makamai za a sayarwa Isra'ila

Shirin sayar da makaman ya haɗa da manyan bama-bamai na bai-ɗaya guda 12,000 nau'in BLU-110A/B, bama-bamai masu nauyin 1,000 pounds tare da ayyukan injiniya, sufuri, da goyon bayan fasaha.

Wani bangare na sanarwar na cewa:

"Ministan harkokin wajen ya tabbatar kuma ya ba da cikakken dalilin cewa akwai yanayin gaggawa da ke buƙatar sayar wa gwamnatin Isra'ila waɗannan makamai nan take."

An tsallake neman amincewar majalisa

Wannan mataki ya yi watsi da buƙatun amincewar majalisa a karkashin sashe na 36(b) na dokar sarrafa fitar da makamai.

A bisa ga sanarwar babban ɗan kwangilar da zai samar da makaman shi ne kamfanin Repkon USA da ke Garland, Texas.

Wani ɓangare na bama-baman za a kwaso su ne daga rumbun makaman sojojin Amurka da ake da su yanzu.

Ana yaki tsakanin Iran, Amurka da Isra'ila

Tashar TRT World ta ce amincewar ta zo ne a daidai lokacin da rikici ke ƙara tsananta a yankin Gabas ta Tsakiya biyo bayan haɗin gwiwar yaƙin Amurka da Isra'ila kan Iran da aka ƙaddamar ranar 28 ga Fabrairu.

Kara karanta wannan

Tofa: Isra'ila ta fadawa Tinubu kasar da ke daukar nauyin ta'addanci a Najeriya

Yaƙin ya yi sanadin mutuwar fiye da mutane 1,300, ciki har da jagoran Iran Ali Khamenei, fiye da ƴan makaranta mata 150, da manyan jami'an sojoji.

Wannan yaƙin ya haddasa rashin tabbas a faɗin yankin, sannan ya janyo hare-haren ramuwar gayya daga Tehran waɗanda suka nufi wuraren da ke da alaƙa da Amurka.

Wani harin jirgi mara matuƙi a Kuwait ya kashe sojojin Amurka guda shida a wata cibiyar gudanar da ayyukan soja.

Amurka ta amince da sayar da bama-bama ga Isra'ila
Shugaban kasar Amurka, Donald Trump Hoto: Donald J. Trump
Source: Facebook

A baya 'yan majalisa sun yi bore

Amincewar kuma ta zo ne a lokacin da ake samun ƙaruwar suka a majalisar dokokin Amurka game da tura makamai zuwa Isra'ila yayin kisan kiyashin da Isra'ila ke yi a Gaza.

A watan Yuli, wasu sanatocin jam'iyyar Democrat guda 27, adadin da ba a taɓa gani ba, sun kaɗa ƙuri'ar goyon bayan ƙudurin dakatar da wasu saye da sayarwar makamai ga Isra'ila, suna ambaton damuwa kan asarar rayukan fararen hula da kuma halin ƙuncin rayuwa a Gaza.

Rasha na taimakon Iran a yaki da Amurka

A wani labarin kuma, kun ji cewa wata majiya ta nuna cewa Rasha na taimakon Iran a yakin da take yi da Amurka da Isra'ila.

Kara karanta wannan

'Yan Boko Haram sun sace daruruwan mutane bayan kai hari a Borno

Wata majiya ta ce Rasha na bai wa Iran bayanan sirri game da wurare da sojojin Amurka ke yawo da sauransu a yakin da ake a Gabas ta Tsakiya.

Majiyar ta ce Rasha na ba Iran taimako game da bayanan motsin sojoji, jiragen ruwa da jiragen saman Amurka a Gabas ta Tsakiya.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng