Iran Ta Yanke Shawara kan Batun Mika Wuya, Ta Aika Sako Mai Zafi ga Amurka da Isra'ila

Iran Ta Yanke Shawara kan Batun Mika Wuya, Ta Aika Sako Mai Zafi ga Amurka da Isra'ila

  • Shugaban Iran, Masoud Pezeshkian, ya maida martani ga Shugaban Amurka, Donald Trump, wanda ya nemi su mika wuya ba tare da sharadi ba
  • Masoud Pezeshkian ya yi ikirarin cewa ba za su taba mika wuya ba, sai dai makiyan Iran su mutu da wannan burin
  • Wannan na zuwa ne yayin da aka shiga rana ta takwas da fara yaki tsakanin Iran da hadin gwiwar kasashen Amurka da Isra'ila

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Iran - Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta bayyana cewa ba za ta taba mika wuya ga Amurka ko Isra'ila ba.

Wannan matsaya na zuwa ne sa'o'i 24 bayan shugaban kasar Amurka, Donald Trump ya nemi Iran ta mika wuya ba tare da wani sharadi ba domin kawo karshen yakin da ya barke.

Masoud Pezeshkian.
Shugaban kasar Iran, Masoud Pezeshkian yana jawabi Hoto: Karim Jaafar
Source: Twitter

Iran za ta mika wuya ga Amurka/Isra'ila?

Kara karanta wannan

Bayan kwanaki 7, Iran ta sauya salon yaki da Amurka, ta sassautawa Larabawa

Tashar Al-Jazeera ta tattaro cewa da yake jawabi a ranar Asabar, 7 ga watan Maris, 2026, shugaban Iran, Masoud Pezeshkian, ya bayyana cewa Iraniyawa ba za su taba mika wuya ga Amurka ko Isra'ila ba.

A cikin wani jawabi da aka watsa a gidan talabijin na ƙasa, Pezeshkian ya ce maƙiyan Iran su tattara burinsu na ganin al’ummar Iran sun miƙa wuya su tafi da shi kabari.

"Makiyan Iran, sai dai ku mutu da burin Iraniyawa za su mika wuya ba tare da sharadi ba, hakan ba zai taba yiwuwa ba," in ji shi.

Yaƙin dai ya fara ne bayan da Isra’ila da Amurka suka kai hare-hare kan Iran a ranar 28 ga Fabrairu, lamarin da ya yi sanadin mutuwar jagoran addinin ƙasar, Ali Khamenei, tare da tayar da rikicin da ya bazu a yankin.

Kasar Iran na mayar da martani ga Amurka

Tun bayan harin, Iran ta mayar da martani ta hanyar harba makamai masu linzami da jirage marasa matuƙi kan Isra’ila da kuma wasu wuraren Amurka a ƙasashen yankin, musamman a ƙasashen Tekun Fasha.

Pezeshkian na cikin mambobi uku na majalisar shugabanci ta rikon ƙwarya da ke jagorantar Iran tun bayan kashe Khamenei, cewar Channels tv.

Kara karanta wannan

Amurka ta shiga uku, Shugaban Rasha, Putin ya kira Shugaban Iran ta wayar tarho

Netanyahu da Trump.
Firaministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu da Shugaban Amurka, Donald Trump Hoto: Anadolu, @DonaldJTrump
Source: Twitter

Masoud Pezeshkian ya nemi afuwar ƙasashen maƙwabta

A yayin jawabin, shugaban Iran ya kuma nemi afuwa ga ƙasashen maƙwabta da hare-haren Iran suka shafa a yankin.

Ya ce:

“Ina neman afuwa a madadina da kuma madadin Iran ga ƙasashen maƙwabta da aka kai wa hari.”

Sai dai ya jaddada cewa Iran ba za ta kai sababbin hare-hare kan ƙasashen maƙwabta ba, sai dai idan hare-hare kan Iran sun fito daga ƙasashensu.

Putin ya yi magana da Shugaban Iran a tarho

A wani rahoton, kun ji cewa Shugaba Vladimir Putin na kasar Rasha ya tattauna da takwaransa na Iran, Masoud Pezeshkian ta wayar tarho.

Rahoto ya nuna cewa Putin da takwaransa na Jamhuriyar Musulunci ta Iran sun tattauna kan yaƙin da ya barke tsakanin AmurkaNda Isra’ila da Iran.

Shugaban kasar ya kuma mika ta’aziyyarsa kan kashe tsohon jagoran addinin Iran, Ayatollah Ali Khamenei, wanda ya rasu a hare-haren da Amurka da Isra’ila suka kai.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262