Rigima Sabuwa: Amurka Ta Yi Martani kan Taimakon da Rasha Ke Ba Iran don Ragargazarta

Rigima Sabuwa: Amurka Ta Yi Martani kan Taimakon da Rasha Ke Ba Iran don Ragargazarta

  • Wasu rahotanni sun fito da ke nuna cewa Rasha na taimakon Iran kan wuraren da za ta farmaka na dakarun sojojin Amurka a yakin da ake yi
  • Ministan tsaron Amurka, Pete Hegseth, ya yi magana kan batun da kuma shirin da Amurka ke yi a lokacin da ake fama da mummunan yaki
  • Pete Hegseth ya bayyana cewa Amurka na sane da komai kuma suna da bayanan sirri kan abubuwan da ke faruwa domin suna saurare

​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Birnin Washington, Amurka - Ministan tsaron Amurka, Pete Hegseth, ya yi magana kan batun taimakon da Rasha ke ba kasar Iran.

Pete Hegseth ya bayyana cewa Amurka ba ta damu ba game da rahotannin da ke cewa Rasha tana ba wa Iran bayanan sirri kan wuraren da dakarun Amurka suke da kuma yadda suke aikinsu.

Kara karanta wannan

Yadda Rasha ke taimakon Iran wajen ragargazar dakarun Amurka a fagen yaki

Amurka ta yi martani kan Rasha
Shugaba Vladimir Putin na Rasha, Shugaba Donald Trump na Amurka da Shugaba Masoud Pezeshkian na Iran Hoto: Sergey Fadeichev, Andrew Caballero-Reynolds
Source: Getty Images

Pete Hegseth ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa da tashar CBS News a ranar Juma'a, 6 ga watan Maris 2026.

Me Amurka ta ce kan taimakon Rasha ga Iran?

Yayin da yake kin tabbatar da ingancin rahoton, Hegseth ya bayyana cewa Amurka na bibiyar komai.

“Kwamandojinmu suna sane da komai. Muna da mafi kyawun dabarun tattara bayanan sirri a duniya. Muna sane da wanda ke magana da wane.”
"Ba mu damu da hakan ba. Muna ɗaukar matakan kariya duk lokacin da buƙata ta taso.”

- Pete Hegseth

Shin Amurka za ta yi wa Rasha magana?

Da aka tambaye shi ko al’ummar Amurka za su iya tsammanin tattaunawa da Rasha domin su daina tsoma baki a rikicin, Hegseth ya ce:

"Shugaba Trump yana da kyakkyawar dangantaka ta musamman da shugabannin duniya da dama, inda zai iya cimma abubuwan da sauran shugabannin ƙasa, musamman ma Joe Biden, ba za su taɓa iya yi ba."

Kara karanta wannan

Shugaba Trump ya bayyana sharadi 1 tak da zai iya kawo karshen yakin Amurka da Iran

Ya kara da cewa za a iya aika saƙonni ta hanyar tattaunawa kai-tsaye ko ta hannun wakilai.

Game da tambayar ko taimakon Rasha na jefa dakarun Amurka cikin haɗari, Hegseth ya ce:

"Mu ne muke jefa sauran mutanen (maƙiya) cikin haɗari, kuma hakan shi ne aikinmu. Don haka ba mu damu da hakan ba. Amma mutanen da kawai suke buƙatar su damu a yanzu su ne ’yan Iran ɗin da suke tunanin za su rayu."
Amurka ta tanka kan batun Rasha na taimakon Iran
Shugaba Donald Trump na Amurka Hoto: Donald J. Trump
Source: Facebook

Martanin Fadar White House

Fadar White House ma ta yi magana kan rahotannin da ke cewa Rasha tana ba wa Iran bayanan wuraren da za a farmaka na dakarun Amurka a Gabas Ta Tsakiya.

Kakakin White House, Karoline Leavit, ta bayyana cewa hakan ba ya da wani tasiri.

“A bayyane yake hakan ba ya yin wani tasiri game da ayyukan soja a Iran saboda muna ragargaza su gaba ɗaya."

- Karoline Leavit

Fasto ya yi hasashe kan yakin Iran da Amurka

A wani labarin kuma, kun ji cewa wani malamin addini daga kasar Ghana, fasto Telvin Adjei Sowah, ya yi hasashe kan yakin Amurka da Iran.

Kara karanta wannan

Yaki na kara zafi, Trump ya ja da baya, ya ki tura sojoji Iran

Fasto Sowah ya bayyana cewa ya ga Donald Trump yana kuka sakamakon rashin nasarar da ya samu a yakin.

Hakazalika, malamin addinin ya bayyana cewa yakin duniya na III aka fara sakamakon fadan da ake yi a yankin Gabas ta Tsakiya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng