"Na ga Ana Kuka"; Malamin Addini Ya Yi Hasashen Wanda Zai Yi Nasara a Yakin Iran da Amurka
- Fasto Telvin Adjei Sowah ya yi hasashen dambarwar da ke gabatowa a duniya da kuma Yaƙin Duniya na III wanda ya haɗa da Amurka da Iran
- Sowah ya yi iƙirarin cewa ya hango wanda zai yi nasara a daidai lokacin da ake samun ƙaruwar tashe-tashen hankula da sauye-sauyen siyasa a Gabas Ta Tsakiya
- Faston na ƙasar Ghana ya bayyana cewa ƙasashe 10 ne ke fafatawa a rikice-rikice a faɗin duniya, tare da 'gagarumin sakamako da zai bayyana nan ba da jimawa ba'
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Washington, Amurka - Wani fitaccen malamin addini a ƙasar Ghana, Fasto Telvin Adjei Sowah, ya yi magana kan rikicin da ya shafi Iran, Isra'ila, da Amurka.
Sowah, wanda shi ne wanda ya kafa cocin Prophetic Life Embassy, ya yi hasashen wannan rikici na yanzu tun a shekarar 2025.

Kara karanta wannan
Babbar magana: Ana tsaka da yaki da Iran, 'dan Majalisar Amurka ya dauko batun Najeriya

Source: Facebook
Fasto ya yi hasashe kan yakin Iran-Amurka
Faston ya yi sabon hasashe kan yakin ne a cikin wani bidiyo da aka sanya a shafin Youtube a ranar Alhamis, 5 ga watan Maris 2026.
Malamin ya yi wani iƙirari mai ban mamaki cewa ya ga Shugaban Amurka Donald Trump cikin kuka saboda wannan yaƙin, kuma ya bayyana da ƙarfin gwiwa cewa yaƙin duniya na III ya riga ya fara.
Bayan haka, ya raba hasashensa game da abin da zai iya faru a cikin watanni biyu masu zuwa, gami da tashin hankali a duniya, sauye-sauyen siyasa, da fitattun abubuwan da za su faru a matakin ƙasa da ƙasa.
Wane hasashe malamin addinin ya yi?
“Yanzu, me zai faru? Na ga Donald Trump yana kuka. Ba ina maganar kukan boye ba ne. Yana kuka a zahiri. Donald Trump zai kasance yana kuka."
"Yayin da na ga Donald Trump yana kuka, sai na ga Larabawa, waɗannan mutanen Iran da komai, mutanen Madrasa, suna ɗauke da shebur, kuma suna tono su kamar duwatsu don su koma Amurka daga daukacin yankin Gabas Ta Tsakiya."

Kara karanta wannan
Shugaba Trump ya bayyana sharadi 1 tak da zai iya kawo karshen yakin Amurka da Iran
“Na fahimci cewa suna nutsar da jiragen ruwan Amurka, saboda na ga tutocin Amurka a kife kamar haka a tsakiyar ruwa a Gabas Ta Tsakiya. Ina kallon jiragen a ƙarƙashin ruwa."
"Ina kallonsa. Ina kallon bama-baman. Ina kallon waɗancan jiragen a tsaye a kife a can. Manyan jiragen ruwan dakon jiragen sama sun lankwasa rabi. Suna ƙoƙarin nutsewa. Suna ƙoƙarin farfaɗo da shi, suna ƙoƙarin amfani da jirage masu saukar ungulu don riƙe shi tare da komai."
"Na ga jiragen ruwan Amurka, injinan yaƙi da komai, suna komawa baya, suna gudu daga Iran. Su ma sun kashe wasu mutane. Za su lalata Iran zuwa wani mataki, amma duk da haka za su gudu a ƙarshe saboda yaƙin nasu ya zama daban."
“Wannan yaƙin, yaƙin duniya na III ya fara. Akwai ƙasashe kusan 10 da ke yaƙi a lokaci guda. Kawai dai har yanzu ba ku sani ba ne. Yana gab da kankama.”
- Fasto Telvin Adjei Sowah

Source: Facebook
Ga bidiyon a nan kasa:
Iran ta harba makamai kan Isra'ila
A wani labarin kuma, kun ji cewa Iran ta harba makamai masu linzami kan birnin Tel-Aviv na kasar Isra'ila yayin da ake ci gaba da gwabza fada.
Sabodan luguden na makaman masu linzami da Iran ta harba sun haddasa fashe-fashe a babban birnin na kasar Isra'ila.
Hasken makaman ya mamaye sararin samaniyar Netanya, wani birni da ke Arewacin Tel Aviv a gabar tekun Bahar Rum.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
