Yadda Rasha ke Taimakon Iran wajen Ragargazar Dakarun Amurka a Fagen Yaki
- An fara zargin cewa Rasha na cikin wadanda ke tallafawa kasar Iran da kayan aiki wajen kakkabo kadarorin Amurka a Gabas ta Tsakiya
- Taimakon da wata majiya ta ce Rasha na ba Iran sun hada da bayanan sirri game da yadda sojojin Amurka ke motsi a kasashe yankin
- Majiyar ta yi magana game da kasar China, sai dai an alakanta ta da fatan ganin yakin ya kare da wuri ba tare da ya dauki dogon lokaci ba
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Russia - Wata majiya ta ce Rasha na bai wa Iran bayanan sirri game da wurare da sojojin Amurka ke yawo da sauransu a yakin da ake a Gabas ta Tsakiya.
Hakan na zuwa ne bayan shafe mako guda ana kai hare-hare tsakanin juna bayan barkewar yakin Iran da Amurka/Isra'ila da ya yi sanadiyyar Ayatollah Ali Khamenei.

Kara karanta wannan
Akwai matsala: Kasar Qatar ta samu sabani da Iran a yakin da ya barke da Amurka da Isra'ila

Source: Getty Images
Rahoton tashar CNN ya nuna cewa an tuntubi hukumar leken asirin Amurka game da zargin cewa Rasha ta shiga yakin ta bayan fage.
Taimakon da Rasha ke ba kasar Iran
NBC ta rahoto wata majiya ta ce kasar Rasha na ba Iran taimako game da bayanan mostin sojoji, jiragen ruwa da jiragen saman Amurka a Gabas ta Tsakiya.
Ɗaya daga cikin mutanen da suke da masaniya kan lamarin ya ce yawancin bayanan da Rasha ta bai wa Iran hotuna ne da aka ɗauka ta tauraron dan adam na musamman da ke kewaya sararin samaniya.
Wasu rahotanni sun bayyana cewa wannan shi ne karon farko da aka samu alamar cewa Moscow na ƙoƙarin shiga cikin wannan yaƙi.
Me Rasha ke samu daga Iran?
Duk da bayani kan irin agajin da Moscow ke ba Iran, har yanzu ba a bayyana abin da Rasha ke samu a madadin wannan taimako ba.
Sai dai wata majiya ta ce a tabbatar ko akwai wani hari na Iran da aka kai wanda za a iya danganta shi kai tsaye da bayanan da Rasha ta bayar ba.
Amma a kwanakin baya wasu jiragen sama marasa matuka na Iran sun kai hare-hare a wuraren da sojojin Amurka suke, lamarin da ya jawo mutuwar sojoji.

Source: Twitter
Ɗaya daga cikin majiyoyin da aka sanar da su bayanan sirrin ta ce:
“Wannan yana nuna cewa har yanzu Rasha tana matuƙar goyon bayan Iran.”
Me China ke yi game da yakin?
A gefe guda kuma, wata majiya ta ce Amurka na da bayanan sirri da ke nuna cewa China na iya shirye-shiryen ba Iran tallafin kuɗi, kayayyakin gyara da kuma sassan makamai masu linzami.
Mutane uku da suka san batun ne suka bayyana haka, duk da cewa Beijing har yanzu ba ta shiga wannan yaƙi kai tsaye ba.
China na dogaro sosai da man fetur daga Iran, kuma an ruwaito cewa tana matsa wa Tehran lamba domin tabbatar da jiragen ruwa na iya wucewa lafiya ta mashigar Hormuz.
Trump zai tura sojoji zuwa Iran?
A wani rahoton, kun ji cewa Shugaba Donald Trump ya bayyana cewa ba zai tura sojojin kasa Tehran ba a yakin da ya ke da Iran.
Trump ya bayyana haka ne jim kadan bayan ganawa da 'yan kwallon Inter Miami da suka hada da Lionel Messi a fadar White House.
Tun da farko dai Iran ta bayyana cewa duk sojan Amurka da Trump ya tura Tehran saboda yaki zai hadu da balbalin bala'i a rayuwarsa.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

