Tana tsakiyar Karbar Wuta daga Amurka, Iran Ta Samu Taimako daga Kasar Indiya
- Gwamnatin Indiya ta ba sojojin ruwan Iran da suka kai kimananin 183 mafaka a birnin Kochi bayan jirginsu ya samu matsala
- Wannan na zuwa ne yayin da Amurka ta harba makamin da ya tarwatsa wani jirgin ruwan Iran, inda sojoji fiye da 80 suka mutu
- Sojojin Isra'ila sun yi ikirarin cewa makaman da suka harba sun sauka a wurare 400 a yammacin Iran ciki har da wuraren makamai
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Indiya - Gwamnatin Indiya ta sanar da cewa ta ba sojojin ruwan Iran guda 183 mafaka a birnin Kochi bayan da jirgina yaƙin su, IRIS Lavan, ya fuskanci matsaloli tun a ranar 28 ga Fabrairu, 2026.
Wannan mataki na zuwa ne a daidai lokacin da gwamnatin Narendra Modi ke fuskantar suka kan yadda ta yi shiru bayan da Amurka ta nutsar da wani jirgin Iran, IRIS Dena, wanda Indiya ta gayyata don shirin hadin gwiwa.

Source: Getty Images
Indiya ta taimakawa sojojin kasar Iran
Akalla mutane 80 ne suka mutu a cikin jirgin Dena bayan da wani jirgin ruwan yaƙi na Amurka ya harbe shi da makami mai linzami, in ji rahoton Aljazeera.
Duk da mutuwar gomman sojojin Iran, gwamnatin Indiya ta ki fitowa ta soki Amurka kan tarwatsa jirgin yakin Iran din da ta gayyata zuwa ruwanta.
A ranar Juma'a, gwamnatin Indiya ta ce ta taimaki wani jirgin yakin Iran na daban, wanda shi ma ya shiga atisayen hadin gwiwar da aka yi tare da Dena.
Wani jami'in gwamnatin Indiya ya sanar da cewa:
"Mun samu wani sako a ranar 28 ga Fabrairu, inda aka gabatar da bukatar taimakawa wani jirgin ruwa da ya samu matsalar na'ura. An amince da wannan bukata a ranar 1 ga watan Maris, kuma jirgin na a gabar tekunmu a Kochi tun ranar 4 ga Maris."
Gwamntin Indiya ta bayyana cewa ta samar da wurin kwana ga jami'an sojin da ke cikin jirgin har su 183 a cikin birnin Kochi.
Isra'ila na ci gaba da kai hari Tehran
Yayin da ake tsaka da wannan takaddama, rundunar sojin Isra'ila ta kaddamar da sababbin hare-hare ta sama a birnin Tehran da kuma kewayen Kermanshah.
Wadannan yankuna da Isra'ila ke farmaka su ne wuraren manyan masana'antun kera makamai masu linzami na Iran, kamar yadda rahoton The Times of Israel ya nuna.
Isra'ila ta yi ikirarin cewa makamanta sun sauka a fiye da wurare 400 a yammacin Iran, wadanda suka hada da wuraren harba makamai masu linzami da rumbun adana jiragee mara matuki.

Source: Getty Images
Iran ta yi gum kan ikirarin Isra'ila
Haka kuma, sojojin Isra'ila sun bayyana cewa sun lalata wata babbar mota dake jigilar na'urorin kariya daga hare-haren sama a yankin Shahroud dake yammacin Iran.
Rundunar sojin ta wallafa hotunan da suka nuna yadda aka lallata motar a kan wata hanya, kodayake har yanzu Iran ba ta mayar da martani kan waɗannan ikirari na Isra'ila ba.
Trump ya nemi taimakon Ukraine?
Kun dai ji cewa, Shugaban kasar Ukraine, Volodymyr Zelensky, ya ce gwamnatin Amurka ta nemi taimakon ƙasarsa a yaƙin da take yi da Iran.
Zelensky ya ce Shugaba Donald Trump na son Ukraine ta taimaka masa don kare ƙasashen da ke ƙawance da Amurka a yankin Gulf daga hare-haren jiragen Iran.
Ya ce abokan hulɗarsu na ƙasashen duniya, musamman Amurka, sun mika buƙatar samun gogewar Ukraine wajen kakkabo jiragen Shahed waɗanda Iran ke kerawa.
Asali: Legit.ng


