Babbar Magana: Ana tsaka da Yaki da Iran, Dan Majalisar Amurka Ya Dauko Batun Najeriya

Babbar Magana: Ana tsaka da Yaki da Iran, Dan Majalisar Amurka Ya Dauko Batun Najeriya

  • 'Dan Majalisar dokokin Amurka, Riley Moore ya sake dauko batun zargin musgunawa kiristoci a Najeriya yayin da kasarsa ke yaki da Iran
  • Moore ya koka kan wasu sababbin hare-hare da aka kai kwanan nan, inda ya yi zargin cewa 'yan ta'adda na ci gaba da kashe kiristoci a Najeriya
  • Ya ce rahoton binciken da aka gudanar na gaban gwamnatin Amurka amma suna tsammanin gwamnatin Najeriya za ta kara kaimi

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

America - Ɗan majalisar wakilai ta Amurka, Riley Moore, ya nuna damuwa kan rahotannin hare-haren da ake kai wa Kiristoci a Najeriya a daidai lokacin da kasarsa ke yaki da Iran.

Moore ya ambaci wasu sababbin hare-hare da suka haɗa da ƙone wani coci a Wukari da kuma tashin hankalin da ‘yan ta’adda ke kara haifarwa a Arewa maso Gabashin Najeriya.

Kara karanta wannan

An nemi Na'ibin limami da wasu mazauna Katsina an rasa bayan hare haren yan ta'adda

Moore.
Dan Majalisar dokokin Amurka, Filey Moore yana magana a taron kasa Hoto: @RepRileyMoore
Source: Twitter

'Dan Majalisa Moore ya bayyana hakan ne a cikin wasu saƙonni da ya wallafa a shafinsa na sada zumunta na X a ranar Juma’a.

An ƙona cocin St. Mary’s a Wukari

Yayin da yake mayar da martani kan rahotannin da ke cewa an ƙone cocin St. Mary’s Catholic Cathedral Wukari a ranar 4 ga Maris, ɗan majalisar ya fara sakonsa da wata aya daga Littafi Mai Tsarki.

Ya ce halin da Kiristoci ke ciki a Najeriya yana da matuƙar tayar da hankali, kuma akwai bukatar da dakatar da hakan cikin gaggawa.

Moore ya ce:

“Albarka ta tabbata ga waɗanda ake zalunta saboda adalci. A irin wannan lokaci babu abin da ya fi sanyaya zuciya kamar kalaman Ubangiji. Har yanzu ana kai wa Kiristoci hare-hare a Najeriya saboda addininsu.”

Matsayar Amurka kan kisan kiristoci

Moore ya kuma tunatar da matsayar gwamnatin Amurka kan batun ‘yancin addini a Najeriya, inda ya ce Amurka ta ayyana ƙasar a matsayin wacce ake da damuwa kan tauye ‘yancin addini.

Kara karanta wannan

Lissafi zai kwabewa Trump, mayakan Kurdawa sun ki taya shi yaki da Iran

Ya ce:

“Amurka ta ayyana Najeriya a matsayin ƙasar da ke da babbar damuwa, kuma ba za mu tsaya mu zuba ido muna kallon yadda ake kai wa Kiristoci hari ba.”
Shugaba Tinubu.
Shugaban kasar Najeriya, Bola Ahmed Tinubu a fadar gwamnati Hoto: @aonanuga1956
Source: Twitter

An mika rahoto ga Fadar White House

Moore ya ce an riga an gabatar da rahoto ga fadar gwamnatin Amurka White House kan lamarin, inda aka bukaci ƙarin matakan kare rayukan kiristoci daga gwamnatin Najeriya.

Ya ce:

“Ana kai wa Kiristoci hari kai tsaye saboda addininsu a Najeriya. ISWAP na kashe Kiristoci tare da tilasta wa wasu su musulunta ko su mutu.”

A cewarsa, Amurka na sa ran gwamnatin Najeriya da ke Abuja za ta ƙara ƙaimi wajen kare Kiristoci da sauran al’ummomin da ke fuskantar hare-hare.

An yabi Tinubu kan batun kisan Kiristoci

A wani rahoton, kun ji cewa Shugaban cibiyar nazarin harkokin kwadago ta Michael Imodu (MINILS) da ke Ilorin, Issa Aremu, ya yabawa Tinubu kan yadda ya hana Amurka mamaye Najeriya.

Kara karanta wannan

Iran ta faɗi halin da ƴan Najeriya ke ciki a kasar yayin da ake ci gaba da ɓarin wuta

Aremu ya yaba da irin rawar da Shugaba Bola Tinubu ya taka yayin takaddama da Amurka kan zargin kisan Kiristoci a Najeriya.

Ya bayyana cewa Shugaba Bola Tinubu ya yi amfani da dabarun diflomasiyya wajen shawo kan takwaransa na Amurka, Donald Trump kan zargin yi wa kiristoci kisan kare dangi.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262