Yaki Ya Yi Zafi, Harin Hezbollah Ya Rutsa da Dan Babban Minista a Isra'ila
- Sojojin Isra'ila sun fafata da mayakan kungiyar Hezbollah a kasar Lebanon yayin da ake ci gaba da gwabza fada fada
- Mayakan Hezbollah sun samu nasarar raunata wasu sojojin Isra'ila a fadan da suka yi a tsakanin iyakar Lebanon
- 'Dan Ministan kudi na Isra'ila, Bezalel Smotrich, na daga cikin sojojin da mayakan Hezbollah suka raunata a artabun da suka yi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Tel-Aviv, Isra'ila - Dakarun sojojin Isra'ila sun gwabza fada da mayakan Hezbollah a kan iyakar kasar da Lebanon.
Rahotanni sun nuna cewa ɗan Ministan kuɗin Isra'ila, Bezalel Smotrich, ya ji rauni yayin wani aikin soja a iyakar kasar da Lebanon.

Source: Twitter
Tashar Aljazeera ta kawo rahoton cewa dan na Bezalel Smotrich na daga cikin sojojin da aka raunata yayin artabun a ranar Juma'a, 6 ga watan Maris 2026.
Hezbollah na fada da Sojojin Isra'ila
Raunata dan ministan na zuwa ne yayin da ake ci gaba da musayar wuta tsakanin dakarun Isra'ila da mayakan Hezbollah.
Fada dai ya barke tsakanin bangarorin biyu ne bayan da Isra'ila ta kaddamar da farmaki ta sama da kasa a kan Lebanon, inda ta ce tana farmakar mayakan Hezbollah.
Hezbollah dai tana fafatawa ne da Isra'ila biyo bayan hare-haren da kasar da Amurka ta kaddamar kan Iran wadanda suka yi sanadiyyar rasuwar Ayatollah Ali Khamenei.
Kwanaki kaɗan kafin tura shi fagen daga, an ɗauki wani bidiyo na Smotrich yana yi wa ɗan nasa ban-kwana tare da yi masa addu’o’in samun kariya.
Wannan lamari ya faru ne a daidai lokacin da ake samun ƙaruwar takaddama tsakanin Isra'ila da ƙungiyar Hezbollah, inda a baya Smotrich ya yi barazanar tsananta harin bama-bamai a unguwannin kudancin birnin Beirut.
An jajantawa Ministan kasar Isra'ila
Bayan samun labarin raunin nasa, wasu shugabannin Isra'ila sun fitar da sakonnin nuna alhini ga Ministan.
Ministan tsaron Israila, Israel Katz, ya rubuta a shafinsa na X cewa:
"Ina ƙarfafa Ministan kuɗi Bezalel Smotrich da iyalansa, kuma ina yi wa ɗansa jarumin soja fatan samun sauƙi cikin gaggawa, wanda ya ji rauni a Lebanon yayin gudanar da aikinsa na yaƙar ƙungiyar ta'addanci ta Hezbollah."
"Ina karfafa dukkan dakaru maza da mata na rundunar tsaron Isra'ila (IDF) waɗanda ke yaƙi cike da sadaukarwa a dukkan wurare domin tsaron ƙasar Isra'ila. Daukacin al'ummar Isra'ila suna bayanku kuma suna alfahari da ku."
- Israel Katz

Source: Twitter
An karfafa gwiwar Bezalel Smotrich
Shi ma shugaban jam'iyyar Yesh Atid mai adawa da Benjamin Netanyahu, Yair Lapid, ya aika da sakon jaje ga Bezalel Smotrich.
Yair Lapid ya rubuta a shafinsa na X cewa:
"Ina yi wa ɗan Minista Smotrich, jarumin dakarun rundunar Givati, fatan samun sauƙi da waraka cikin gaggawa, wanda ya ji rauni a yau a iyakar Lebanon. Ina aika saƙon ƙarfafa gwiwa ga mahaifinsa, Bezalel, da dukkan iyalansa."
- Yair Lapid

Kara karanta wannan
Iran ta harba makamai masu linzami kan babban birnin Isra'ila, an ji barnar da suka yi
Isra'ila ta fadi dalilin kashe Khamenei
A wani labarin kuma, kun ji cewa rundunar sojojin Isra'ila ta yi magana kan kisan da ta yi wa jagoran Iran, Ayatollah Ali Khamenei.
Mai magana da yawun rundunar, Nadav Shoshani, ya bayyana Ayatollah Ali Khomenei a matsayin babban kwamandan dakarun sojojin kasar Iran kuma halattaccen wanda ya kamata a farmaka.
Hakazalika, Nadav Shoshani ya kwatanta Khamenei a matsayin mai yanke shawara ta karshe kan ayyukan sojojin Iran.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

