Shugaba Trump Ya Bayyana Sharadi 1 Tak da Zai Iya Kawo Karshen Yakin Amurka da Iran

Shugaba Trump Ya Bayyana Sharadi 1 Tak da Zai Iya Kawo Karshen Yakin Amurka da Iran

  • Shugaba Donald Trump na kasar Amurka ya bayyana cewa mika wuyan Iran ba tare da sharadi ba ne kadai zai kawo karshen yakin da ya barke
  • Trump ya yi wannan furuci ne yayin da aka shiga rana ta bakwai da fara musayar wuta tsakanin Amurka/Isra'ila da kuma kasar Iran
  • A gefe guda kuma, Ministan Yaki na kasar, Pete Hegseth, ya ce hare-haren da Amurka ke kai wa Iran za su ƙaru sosai a kwanaki masu zuwa

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

America - A yau Jumma'a, 6 ga watan Maris, 2026 aka shiga rana ta bakwai da fara yakin Jamhuriyar Musulunci ta Iran da kuma kasashe biyu da suka yi hadin gwiwa, Amurka da Isra'ila.

Yayin da musayar wuta ke kara zafi tsakanin kasashen, Shugaba Donald Trump na Amurka ya gindaya sharadi guda da zai iya warware wannan fada tsakaninsu da Iran.

Kara karanta wannan

Kasar Iran ta farmaki wani jirgin yaki, ta kara yi wa Amurka da Isra'ila babbar illa

Trump.
Shugaba Donald J Trump na kasar Amurka Hoto: @RealDonaldTrump
Source: Getty Images

Donald Trump ya bayyana abin da zai iya kawo karshen yakin a wani sako da ya wallafa a shafinsa mai suna Truth Social platform, yau Jumma'a.

Donald Trump ya gindaya sharadin sulhu da Iran

Shugaban ƙasar Amurka ya bayyana cewa abin da kaɗai zai kawo ƙarshen rikicin da ake yi da Iran shi ne ta miƙa wuya ba tare da gindaya wani sharaɗi ba.

A saƙon da ya wallafa kan yiwuwar tsagaita wuta a yaƙin, Shugaba Trump ya rubuta cewa:

“Ba za mu tsaya mu yi wata yarjejeniya da Iran ba face ta mika wuya ba tare da gindaya wasu sharudda ba."

Wannan furuci na Trump ya zo ne a lokacin da Isra’ila ke ci gaba da kai hare-hare kan wuraren gwamnati a birnin Tehran na Iran, tare da kai hari kan wuraren ƙungiyar Hezbollah a birnin Beirut na ƙasar Lebanon.

Amurka za ta zafafa hare-hare kan Iran

Kara karanta wannan

Yaki na kara zafi, Trump ya ja da baya, ya ki tura sojoji Iran

A gefe guda kuma, Ministan Yaki na kasar Amurka, Pete Hegseth, ya ce hare-haren da Amurka ke kai wa Iran za su ƙaru sosai a kwanaki masu zuwa.

Trump ya ƙara da cewa idan Iran ta amince da wannan sharadi na mika wuya, Amurka da ƙawayenta za su taimaka wajen farfaɗo da tattalin arzikin ƙasar, tare da mayar da ita cikin ƙasashen da ke da ƙarfi a fannin tattalin arziki.

Sai dai ya ce hakan zai faru ne kawai idan aka kafa sabon shugabanci da Amurka za ta amince da shi a Iran.

Shugaban kasar Iran.
Shugaban kasar Iran, Masoud Pezeshkian a wurin taro Hoto: Anadolu
Source: Getty Images

A ƙarshe, Trump ya ƙirƙiri wani sabon taken siyasa mai suna “Make Iran Great Again (MIGA)”, ma'ana manufar farfado da Iran, wanda ya yi kama da tsohon taken kamfen dinsa na “Make America Great Again (MAGA)”.

Iran ta yi iƙirarin kashe sojojin Amurka 500

A wani rahoton, kun ji cewa ƙasar Iran ta ce ta kashe sojojin Amurka a ƙalla 500 bayan shafe kwanaki suna gwabza yaƙin da ya shafi yawancin ƙasashen Gabas ta Tsakiya.

Babban jami'in gwamnatin Iran, Ali Larijani ne ya bayyana haka, inda ya ce za su cigaba da fafatawa da Amurka/Isra'ila kan harin da suka kai masu.

Wannan adadi ya zo ne duk da cewa gwamnatin Trump ta nuna hotunan sojoji hudu da suka mutu a rikicin da ke tsakanin Amurka da Isra’ila da Iran.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262