Malaman Addini Sun Yi Ruwan Addu'o'i ga Trump game da Yaƙin Iran da Isra'ila

Malaman Addini Sun Yi Ruwan Addu'o'i ga Trump game da Yaƙin Iran da Isra'ila

  • Malaman addinin Kirista da shugabannin addini sun taru a ofishin House White House a kasar Amurka domin yin addu'o'i
  • Fastocin sun gudanar da addu’o'i ga Shugaban Amurka Donald Trump yayin da ake yaƙin Iran da Isra'ila a yankin Gabas ta Tsakiya
  • Fastoci sun kewaye Trump a teburin ofishin suna neman Allah ba shi hikima, kariya da jagoranci yayin da yake shugabantar Amurka

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Washington DC, US - Wasu Fastocin Kirista da shugabannin addini sun gudanar da addu'o'i na musamman ga Shugaba Donald Trump.

Fastocin sun taru a ofishin Oval Office na White House domin yi wa Donald Trump addu’a yayin da ake yaƙi tsakanin kasar Iran da Isra'ila.

Fastoci sun yi addu'o'i ga Donald Trump
Shugaba Donald Trump a fadar White House a Amurka a. Hoto: Barry Moore.
Source: Facebook

An yi wa Donald Trump addu'o'i a Amurka

Kara karanta wannan

'Yan ta'adda sun kashe sojojin Najeriya, sun yi wa limamin masallaci yankan rago

A yayin taron, Fastocin Evangelical sun kewaye Trump a teburin 'Resolute Desk' inda suka yi addu’a suna neman Allah ya ba shi hikima, kariya da jagoranci, cewar Baptist New Global.

An gano Fastocin daga wajen taron sun nuna wasu shugabannin addini sun ɗora hannayensu a kan Trump yayin da suke yin addu’a.

An shirya taron ne tare da haɗin gwiwar ofishin White House Faith, inda fitattun Fastoci irin su Robert Jeffress da Samuel Rodriguez suka halarta.

Har ila yau, masanin tarihi David Barton ya halarci taron, wanda ya haɗa shugabannin addinin Evangelical domin yi wa shugaban ƙasa addu’a.

Bayan taron, Fasto Robert Jeffress ya ce abin girmamawa ne a gare shi jagorantar addu’ar da aka yi wa shugaban ƙasar Amurka.

Donald Trump ya sha ruwan addu'o'i daga Fastocin Amurka
Shugaban kasar Amurka, Donald Trump. Hoto: @RealDonaldTrump.
Source: Getty Images

An roka wa Trump samun nasara, hikima

Wasu shugabannin addinin da suka halarta sun bayyana taron a matsayin rana mai muhimmanci, suna cewa lokaci ne mai amfani na yin addu’a ga shugabancin ƙasa.

Wadanda suka halarci taron sun roƙi Allah ya ba shugaban ƙasa hikima, ya kare shi daga haɗari, kuma ya taimaka masa wajen aiwatar da manufofi masu tushe daga addini, cewar Punch.

Kara karanta wannan

Abin da Najeriya da jagororin Afrika ke fadi kan yakin Iran, Amurka da Isra'ila

Taron addu’ar ya nuna yadda gwamnatin Trump ke ƙara kusantar kungiyoyin Kiristocin Evangelical, waɗanda suke daga cikin manyan magoya bayansa a siyasa.

Gwamnatin Trump ta kuma ƙarfafa shirye-shiryen addini a gwamnati, ciki har da kafa ofishin ofishin White House Faith domin hulɗa da shugabannin addini.

Sai dai masu suka suna cewa irin waɗannan taruka na iya jawo damuwa kan raba addini da gwamnati da kuma tasirin addini a manufofin gwamnati.

Fasto ya yi hasashe kan yakin Iran-Isra'ila

A wani labarin, an ji wani fasto ya gargadi Amurka da Isra'ila cewa watakila ba za su yi nasara a yakin da suke yi da Iran ba, bayan kisan Jagoran Kolin Iran, Ali Khamenei.

Isra’ila da Amurka ne suka fara kai wa Iran hari, lamarin da limamin coci a Najeriya, Elijah Ayodele, ya yi hasashen zai iya janyo tangardar tattalin arzikin.

Ayodele ya fadi haka ne bayan tsohon hasashen marigayi babban limamim coci, TB Joshua ta sake bayyana a kafafen sada zumunta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.