Bayan Amurka Ta Dora Mata Laifi, Isra'ila Ta Fadi Dalilin Kashe Ayatollah Khamenei
- Amurka ta fito ta gayawa duniya cewa kasar Isra'ila ce ke da alhakin kashe jagoran juyin juya hali na Iran, Ayatollah Ali Khamenei
- Isra'ila ta bayyana cewa kisan da ta yi wa Ayatollah Khamenei ya yi daidai da dokokkin kasa da kasa da suka shafi harkar yaki
- Harin da Isra'ila ta kai dai wanda ya yi sanadiyyar kashe Khamenei ya hada har da matarsa, surukinsa da wasu jikokinsa
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Tel Aviv, Isra'ila - Kasar Isra'ila ta bayyana cewa kisan da aka yi wa jagoran ƙoli na Iran, Ayatollah Ali Khamenei, ya bi ƙa'idojin dokokin ƙasa da ƙasa da suka shafi rigingimun yaki.
Isra'ila ta bayyana Ayatollah Ali Khomenei a matsayin babban kwamandan dakarun sojojin kasar Iran kuma halattaccen wanda ya kamata a farmaka.

Source: Twitter
Kakakin rundunar sojojin Isra'ila, Nadav Shoshani, ya bayyana hakan a shafinsa na X a ranar Alhamis, 5 ga watan Maris 2026.
Amurka da Isra'ila sun kaddamar da yaki kan Iran
Yaƙin Gabas Ta Tsakiya da aka fara a ranar Asabar ya ɓarke ne da hare-haren haɗin gwiwa na Amurka da Isra'ila kan Iran, ciki har da harin da ya yi sanadin mutuwar jagoran ƙasar.
Isra'ila ta yi iƙirarin cewa waɗannan hare-hare sun zama dole domin kare tsaron ƙasarta, musamman saboda zargin cewa Iran tana sake farfaɗo da shirinta na kera makaman nukiliya a wani sabon rami a ƙarƙashin ƙasa.
Meyasa Isra'ila ta kashe Khamenei?
Kakarin rundunar sojojin na Isra'ila ya bayyana cewa harin da ya kashe Khamenei "ya bi ƙa'idojin dokokin duniya."
Hakazalika, ya kwatanta Khamenei a matsayin mai yanke shawara ta karshe kan ayyukan sojojin Iran.
"A ƙarƙashin dokokin ƙasa da ƙasa na rigingimun yaƙi, kwamandojin soja da ke jagorantar dakarun sojoji a lokacin yaƙi za su iya zama halattattun wadanda za a iya farmaka."
"A matsayinsa na Jagoran Iran, Ali Khamenei ya kasance babban kwamandan dakarun sojojin Iran."
"Yayin wannan rikici da ake ciki, ya ba da umarnin amfani da ƙarfi kan Isra'ila, sannan ya sa ido kan samar da kuɗaɗe, makamai, da haɗin kan ƙungiyoyin ta'addanci."
“Kawar da babban kwamandan ya samar da gagarumar nasara ta fuskar soja ta hanyar raunana ikon Iran na tsara da kuma haɗa kan hare-hare kan Isra'ila."
- Nadav Shoshani

Source: Twitter
Isra'ila ta kashe iyalan Khamenei
Rahotanni sun nuna cewa matar Khamenei, surukamkinsa, da kuma jikoki biyu waɗanda ƙananan yara ne, duk sun mutu a harin da aka kashe Ayatollah.
Iran ta mayar da martani kan kisan nasa ta hanyar harba ɗunbin makamai masu linzami kan Isra'ila da sauran wurare a faɗin Gabas Ta Tsakiya, ciki har da sansanonin sojoji da ofisoshin diflomasiyya na Amurka.
Har yanzu dai Isra'ila da Amurka suna ci gaba da kai wa wasu wurare hari a cikin ƙasar Iran.
Kasar Iran ta kashe sojojin Amurka
A wani labarin kuma, kun ji cewa ta bayyana cewa ta kashe sojojin Amurka akalla 500 a yakin da ake gwabzawa a Gabas ta Tsakiya.
Daya daga cikin manyan jami’an tsaron kasar Iran, Ali Larijani, ya bayyana cewa sun kashe sojojin Amurka 500 a ‘yan kwanakin da suka gabata.
Lajarani ya kuma kara da cewa lamarin bai zo karshe ba, kuma ba za su bari kashe Imam Khamenei ya tafi a banza ba.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

