Trump Ya Fadi Kasar da zai Fatattaki Shugabanta bayan Gama Yaki da Iran
- Shugaba Donald Trump ya nuna cewa zai cigaba da fafata yaki da kifar da gwamnatoci a fadin duniya yayin ya ke jagorantar yaki a kasar Iran
- A hira da aka yi da shi, Trump ya nuna cewa kasar da zai shiga a gaba bayan gama yaki da Iran ita ce Cuba, inda ya fadi matakan da zai dauka
- Tun bayan dawowar shi mulki karo na biyu, Trump ya kaddamar da hare-hare a kasashe da dama duk da ya nuna ba zai yi haka ba kafin zabe
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
America - Shugaban Amurka Donald Trump ya sake bayyana barazanar kifar da gwamnatin ƙasar Cuba, inda ya ce matakin Amurka kan ƙasar na iya biyo bayan kammala yakin da gwamnatinsa ke yi da Iran.
Da yake jawabi a Fadar White House ranar Alhamis yayin ziyarar ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Inter Miami CF, Trump ya yabawa ministan harkokin wajen Amurka, Marco Rubio.

Source: Getty Images
Trump zai shiga Cuba bayan Iran
Al-Jazeera ta wallafa cewa ya yabi Rubio kan abin da ya kira “kyakkyawan aiki” da yake yi kan batun Cuba, inda gwamnatinsa ta tsaurara takunkuman tattalin arziki.
Trump ya ce:
“Abin da ke faruwa da Cuba yana da kyau. Muna ganin cewa muna son mu gama wannan yaki da muke kai [wato Iran]. Amma mu jira lokaci kawai.”
Trump da abokan siyasarsa sun sha yin barazanar matsa lamba ga Cuba, inda suke ƙara tsaurara takunkumi da nufin kifar da gwamnatin ƙasar.
Barazanar Trump ga Cuba a baya
Bayan da Amurka ta kama shugaban ƙasar Nicolás Maduro na Venezuela a watan Janairun 2026, Trump ya ce za a katse gaba ɗaya man da Venezuela ke bai wa Cuba.
Trump ya kuma rungumi barazanar amfani da ƙarfi mai yawa na soji domin cimma manufofinsa a sassa daban-daban na duniya, ciki har da yankin Latin, inda a baya ya ce Cuba “na dab da rugujewa” nan gaba kaɗan.

Source: Getty Images
An soki wasu hare-haren sojin Amurka, ciki har da na Venezuela da kuma hare-hare kan wasu jiragen da ake zargin na safarar miyagun ƙwayoyi a yankin Latin, amma Trump ya nuna ko a jikinsa.
Trump ya yabi sojojin Amurka
Rahoto ya nuna cewa shugaba Donald Trump ya yaba wa dakarun Amurka, inda ya ce suna aiki yadda ya kamata bayan dawowarsa mulki karo na biyu.
CNBC ta rahoto Trump ya ce:
“Mun samu gagarumar nasara ta hanyoyi da dama. Na gina sojojin Amurka tare da sake inganta su a wa’adina na farko, kuma yanzu muna amfani da su fiye da yadda nake so a gaskiya."
Trump ya kai hari Ecuador
A wani labarin, kun ji cewa shugaban Amurka, Donald Trump ya kaddamar da hare-hare a kasar Ecuador kan zargin safarar miyagun kwayoyi.
Amurka ta ce ta hada kai da Ecuardor wajen kai hare-haren, duk da cewa kasashe biyun ba su yi karin bayani game da nasarar harin ba.
Amurka ta kai farmaki ne kwanaki kadan bayan shugaban Ecuardor ya gana da babban kwamandan sojojin da ke lura da dakarun yankin.
Asali: Legit.ng

