Abin da Muka Sani kan Jita Jitar Kashe Wanda Ake Sa Ran zai Gaji Khamenei a Iran
- Bayan kisan jagoran addinin Musulunci a Iran, Ayatollah Ali Khamenei, wasu sun fara yada jita-jitar karya game da magajinsa
- Wani mai amfani da kafofin sadarwa ya yi ikirarin cewa sabon shugaban rikon kwarya na Iran, Ayatollah Alireza Arafi
- Ya bayyana cewa mutumin ya mutu ne bayan harin Amurka da Isra’ila a birnin Tehran da ke Iran wanda aka yi a karshen makon jiya
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Tehran, Iran - Mutuwar Ali Khamenei bayan harin Amurka da Isra’ila a Tehran ya janyo tashin hankali da jita-jita da dama.
Bayan faruwar lamarin, Iran ta ayyana zaman makoki na kwanaki 40 sannan gwamnati ta sanar da kafa kwamitin rikon kwarya domin jagorantar kasar.

Source: Facebook
Kwamitin rikon kwaryar ya kunshi mutum uku: Shugaban kasa Masoud Pezeshkian, Shugaban bangaren shari’a Gholam-Hossein Mohseni-Ejei da kuma Babban malamin addini Ayatollah Arafi, cewar CNN.

Kara karanta wannan
Khamenei: An ɗage taron jana'izar jagoran addini a Iran yayin da ake harin magajinsa
Yadda aka yada rade-radin kashe Alireza Arafi
Bayan sanarwar, wani mai amfani da X mai suna @cryptorover ya yi ikirarin cewa Alireza Arafi, wanda ya kira sabon shugaban rikon kwarya, shi ma ya mutu.
Wasu masu amfani sun gaskata jita-jitar, inda wasu suka ce kujerar shugabancin Iran ta zama babu kowa, yayin da wasu suka nemi sanin wanda zai gaje shi.
Sai dai wasu kuma sun nuna shakku kan sahihancin ikirarin, suna cewa labarin ba gaskiya ba ne kuma yana yaudarar mutane da dama.
Ya ake zaben sabon jagoran addini a Iran?
Kundin tsarin mulkin Iran ta tanadi cewa idan jagoran koli ya mutu, za a kafa kwamitin rikon kwarya har sai an zabi sabon jagora.
Ikon jagoran koli na wucin gadi yana komawa ga wannan kwamitin wanda ya kunshi shugaban kasa, shugaban shari’a da kuma babban malami daga majalisar.
Rahotanni sun nuna cewa an nada Arafi cikin kwamitin rikon kwaryar tare da Pezeshkian da Mohseni-Ejei domin tafiyar da mulkin kasar.

Kara karanta wannan
Yaki na kara zafi da Amurka, an ji shirin da Iran take yi na nada magajin Ayatollah Khamenei

Source: Twitter
Bincike ya ƙaryata kisan Arafi a Iran
Sai dai Dubawa ta binciki manyan kafafen labarai na duniya amma ba ta samu wani rahoto daga Al Jazeera, BBC ko CNN da ke tabbatar da mutuwar Arafi ba.
Hakazalika, kafafen gwamnatin Iran kamar IRNA, Press TV da Tasnim News Agency ba su fitar da wata sanarwa da ke nuna cewa Arafi ya mutu ba.
A zahiri, a ranar 2 ga Maris 2026, kafafen Iran sun ruwaito jawabin da Arafi ya yi inda ya ce shahadar Khamenei za ta karfafa Iran.
Idan har Arafi ya mutu kamar yadda aka yi ikirari, ba zai yiwu ya fito fili ya gabatar da jawabi a bainar jama’a ba.
Saboda haka, duk da cewa Arafi na cikin kwamitin rikon kwarya, ba shi ne sabon jagoran koli na Iran ba kuma yana raye.
Babu wata kwakkwarar hujja da ke nuna cewa Ayatollah Arafi ya mutu, don haka ikirarin da aka yada a kafafen sada zumunta karya ne.

Kara karanta wannan
Yadda kisan Khamenei zai shafi 'yan Shi'a a Najeriya, rashinsa ya 'hada' kan Musulmi
Iran ta sake kai farmaki kan tankokin Amurka
A wani labarin, yakin Amurka/Isra'ila da Iran na cigaba da daukan sabon salo bayan shiga rana ta shida ana fafatawa tsakanin juna da kai hare-hare.
Amurka ta sanar da nutsar da wani jirgin ruwan Iran da ya dauko hanya daga Indiya zai dawo gida bayan gayyata da aka masa zuwa kasar.
Da safiyar Alhamis, 5 ga watan Maris, 2026 rundunar juyin juya hali ta Iran ta sanar da ramuwar gayya kan wani jirgin ruwa dauke da man Amurka.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng