Wata Sabuwa: Shugaban Amurka Ya Kawo Tarnaki a Shirin Nada Sabon Jagoran Addinin Iran
- Shugaban Amurka, Donald Trump na neman kawo hargitsi a shirin Iran na nada sabon jagora, wanda zai gaji Ayatollah Ali Khamenei
- A wata hira da aka yi da shi yau Alhamis, Trump ya bayyana cewa ya kamata a sanya shi a cikin wadanda za su zabi sabon jagoran Iran
- Ya kara da cewa ya samu labarin ana shirin nada dan marigayi, Mojtaba Khamenei, inda ya ce ba zai yarda da wannan zabi ba
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Amurka - Shugaba Donald Trump na neman a sanya shi a cikin wadanda za su zabi sabon jagoran addini na Jamhuriyar Musulunci ta Iran.
Wannan na zuwa ne yayin da Iran ke ci gaba da shirye-shiryen nada sabon jagora bayan kashe Ayatollah Ali Khamenei a hare-haren hadin gwiwar Amurka da Isra'ila.

Kara karanta wannan
Khamenei: An ɗage taron jana'izar jagoran addini a Iran yayin da ake harin magajinsa

Source: Getty Images
Trump na neman shiga harkokin Iran
Tashar Al-Jazeera ta ruwaito cewa Shugaba Donald Trump, ya bayyana cewa yana ganin ya kamata a ba shi damar shiga cikin zaɓen sabon jagoran Iran bayan rasuwar Khamenei.
Har yanzu dai Iran ba ta nada jagoran addini na kasar ba, amma rahotanni daga birnin Tehran sun nuna cewa dan marigayi, Mojtaba Khamenei ne a sahun gaba cikin wadanda ake ganin za su karbi ragamar kasar.
A wata hira da ya yi da kafar watsa labarai ta Axios, Trump ya ce Iran na “ɓata lokacinta” idan ta yi ƙoƙarin naɗa sabon jagora ba tare da sa hannun Amurka ba.
Trump ya yi fatali da shirin nada 'dan Khamenei
Shugaba Trump ya ce ya samu labarin cewa Mojtaba Khamenei, ɗan marigayi Ali Khamenei, shi ne wanda ake ganin zai iya gadon mahaifinsa a matsayin sabon jagoran Iran. Sai dai ya ce ba zai amince da hakan ba.

Kara karanta wannan
Yaki na kara zafi da Amurka, an ji shirin da Iran take yi na nada magajin Ayatollah Khamenei
“Ɗan Khamenei ba shi da ƙarfi, dole ne ni ma in kasance cikin waɗanda za su zaɓi sabon jagoran Iran," in ji Trump.
Wanda Amurka take son Iran ta nada
Ya ƙara da cewa duk wanda za a naɗa a matsayin sabon jagoran Iran idan ya ci gaba da manufofin tsohon shugabanci, hakan na iya janyo sabon rikici da Amurka nan da shekaru biyar.
Trump ya kuma jaddada cewa:
“Ɗan Khamenei ba abin karɓa ba ne a gare ni. Muna son wanda zai kawo zaman lafiya da haɗin kai a Iran.”
Wannan kalamai na Trump na zuwa ne bayan shiga rana ta 6 da fara yaki tsakanin Amurka/Isra'ila da Iran, wanda kawo yanzu ya jawo asarar rayukan mutane fiye da 1000.

Source: Getty Images
Tsohon sojan Amurka ta tada hayaniya a Majalisa
A wani rahoton, kun ji cewa wani tsohon sojan Amurka ya tayar da bore yayin zaman wani kwamitin majalisar dattawa kan batun yakin da kasar ta shiga da Iran.
Tsohon soojan, wanda aka ruwaito ya taba takarar sanata, ya tada hayaniya tare da katse zaman da ake yi a Capitol Hill domin nuna rashin amincewa da yaƙin Amurka da Isra’ila da ƙasar Iran.
Sanata Tim Sheehy na jam'iyyar Republican daga jihar Montana, ya taimaka wa jami'an 'yan sanda da dama wajen fitar da mutumin.
Asali: Legit.ng
