Najeriya Ta Shiga Jerin Kasashe 3 da Za Su Samu Alheri sakamakon Yakin Iran da Amurka
- Rahoto ya nuna cewa duk da yakin Iran da Amurka/Isra'ila ba alheri ba ne ga tattalin arzikin duniya, amma wasu kasashen Afirka za su amfana
- A wani bincike da aka yi, Najeriya na daga cikin kasashen da lalitarsu za ta yi kauri saboda karuwar kudade shiga sakamakon tsadar gangar mai
- Sai dai binciken ya nuna cewa galibin kasashen nahiyar Afirka za su shiga matsin tattalin arziki ne sakamakon yakin da ake yi a Gabas ta Tsakiya
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Rahotanni sun nuna cewa tashin farashin danyen mai a kasuwannin duniya sakamakon yakin Amurka, Isra'ila da Iran zai amfani tattalin arzikin wasu kasashe.
Wannan na zuwa ne yayin da musayar wuta ke kara zafi a tsakanin kasashen, tun bayan barkewar yaki da safiyar ranar Asabar, 28 ga watan Fabrairun 2026.

Kara karanta wannan
Yakin Amurka da Iran: Matatar Dangote ta yi magana kan yiwuwar samun man fetur a Najeriya

Source: Getty Images
Jaridar The Cable ta tattaro cewa wannan yaki da ba shi da alamun karewa nan kusa, ya jawo tashin farashin gangar danyen mai a kasuwannin duniya.
Najeriya za ta samu karin kudin shiga
A cewar wani rahoto da Bloomberg Economics ta fitar ranar Alhamis, kasashen uku kacal a yankin Afrika ta kudu da Sahara za su samu karin kudaden shiga sakamakon wannan yaki.
Rahoton ya ce kasshen Angola, Nigeria da Ghana ne tattalin arzikinsu zai bunkasa ta fuskar kudaden shiga sakamakon tashin farashin mai.
Sai dai rahoton ya bayyana cewa yawancin sauran kasashen yankin za su fuskanci matsin tattalin arziki ne saboda yakin.
Tasirin karin farashin mai ga Afirka
Wata masaniyar harkokin tattalin arziki ta jairdar, Yvonne Mhango, ta ce idan farashin danyen mai ya tsaya a $85 a kowace ganga, kasashen Angola, Najeriya da Ghana za su samu sauki a bangaren hada-hadar kasuwanci da kasashen waje.
Sai dai ta ce kasashe kamar Jamhuriyar Dimokuradiyyar Congo, Afirka ta Kudu da Kenya za su fi shan wahala.
Ta kara da cewa mafi yawan kasashen Afirka za su iya fuskantar raguwar darajar kudinsu, karuwar hauhawar farashi da yiwuwar bankunan kasa su kara kudin ruwa.
Najeriya na iya cin gajiyar tsadar danyen mai
Rahoton ya bayyana cewa Angola na iya kara samun kusan kashi 3.3% na GDP daga karin farashin mai, yayin da Nigeria za ta amfana ba kawai daga sayar da danyen mai ba, har ma daga fitar da man fetur da aka tace.
A cikin rahoton, an ambaci attajirin Najeriya Aliko Dangote, wanda ya ce matatar man da ya gina mai karfin tace ganga 650,000 a rana na iya fara fitar da man fetur zuwa kasashen Turai idan farashin ya yi kyau.
Rahoton ya nuna cewa farashin gangar danyen mai na Brent crude ya tashi zuwa Dala 85 a ranar 3 ga Maris, daga dala 72 da ake sayarwa a ranar 28 ga Fabrairu, 2025.

Source: Getty Images
Litar fetur ta kara tsada a Najeriya
A wani rahoton, kun ji cewa yakin Iran da Amurka/Isra'ila ya fara shafar yan Najeriya yayin da aka ruwaito cewa farashin litar fetur ta kara tashi a gidajen mai.
Bayan tashin farashin danyen mai a kasuwar duniya, matatar mai ta Dangote , a ranar Litinin, ta kara N100 kan kowane lita, inda ta mayar da farashin sari daga N774 zuwa N874.
Sakamakon haka, gidajen mai a fadin kasar nan suka fara sauya nasu farashin litar fetur, lamarin da zai shafi talakawan Najeriya kai tsaye.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

