An Ci Mutuncin Dan Takarar Sanata da Ya Soki Amurka saboda Hari kan Iran
- An kori wani tsohon sojan rundunar ruwa ta Amurka daga zaman majalisar dattawa bayan ya katse taro yana sukar aikin kasarsa
- Jami’an ‘yan sandan Capitol sun kama McGinnis bayan ya yi turjiya lokacin da ake ƙoƙarin fitar da shi daga ɗakin zaman sauraron rahoto
- ‘Yan sanda sun tuhume shi da kai hari ga jami’ai da kuma hana gudanar da taron majalisa yayin da bidiyon lamarin ya yaɗu sosai
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Washington DC, US - Wani tsohon soja a rundunar sojojin ruwa ta Amurka ya tayar da rigima yayin zaman majalisa a kasar Amurka.
Dan takarar majalisa a Carolina ta Arewa, Brian McGinnis, ya shiga hannun hukuma bayan an fitar da shi da ƙarfi daga majalisar dokokin Amurka saboda zanga-zanga kan yaƙin Iran.

Source: Getty Images
Bidiyon korar tsohon sojan daga Majalisar Amurka

Kara karanta wannan
Babbar magana: Ana ciki yaki da Iran, tsohon soja ya tayar da tarnaki a majalisar Amurka
A wani bidiyo da AdameMedia ya wallafa a shafinsa na X, an gano yadda aka fitar da McGinnis daga majalisar dattawa kan korafi game da dalilin ya sa suke shirin tura matasa zuwa yaƙi.
Rahotanni sun ce lamarin ya faru ne yayin zaman kwamitin Majalisar dattawa kan harkokin rundunar soji, inda manyan jami’an soja ke gabatar da bayani kan shirye-shiryen soji da ƙarfin runduna.
Kimani mintuna 30 bayan fara zaman, McGinnis wanda ya sanya kayan sojansa ya tashi tsaye yana ihu cewa:
“Babu wanda yake son ya yi yaƙi saboda Isra’ila,”
Sannan an kuma ji yana cewa,
“Amurka ba ta son tura ‘ya’yanta zuwa yaƙi.”

Source: Twitter
Yadda aka karya hannun 'dan siyasar Amurka
Jami’an ‘yan sandan Capitol sun yi ƙoƙarin fitar da shi daga ɗakin zaman, amma bidiyoyin da suka yaɗu sun nuna yana ƙoƙarin yin turjiya yayin da jami’an ke jan sa zuwa waje.
A yayin wannan ƙoƙari, an ce hannun hagun McGinnis ya makale tsakanin ƙofa da jikinta, inda wani ya yi zargin cewa an karya masa hannu.
Daga ƙarshe jami’an ‘yan sanda sun fitar da shi daga ɗakin zaman sannan suka kai shi waje, inda aka ji yana cewa hannunsa na hagu ya karye.
Manajan kamfen dinsa, Mark Elbourno, ya tabbatar cewa an kama McGinnis kuma an kai shi asibitin jami'ar George Washington domin kula da lafiyarsa.
Ya kuma musanta cewa McGinnis ya kai wa jami’an ‘yan sanda hari, yana cewa kawai yana son a ji muryarsa ne amma a maimakon haka shi ne aka kai masa hari har aka karya masa hannu.
Sai dai ‘yan sandan Capitol sun ce McGinnis ne ya jefa hannunsa cikin ƙofa domin ya hana jami’an fitar da shi tare da ƙoƙarin komawa cikin ɗakin taron, cewar Punch.
‘Yan sandan sun ce yanzu yana fuskantar tuhuma uku na kai hari ga jami’in ‘yan sanda, uku na hana kama shi, da kuma tuhumar hana wucewar jama’a bayan ya katse zaman kwamitin majalisar.
Rasha ta magantu kan yakin Iran, Isra'ila
An ji cewa Fadar Kremlin a Rasha ta yi magana game da rashin shiga yakin da ake yi tsakanin Iran da Isra'ila da aka fara a karshen makon jiya.
Kakakin Kremlin, Dmitry Peskov ya ce matsayin Rasha kan rikicin Iran bai sauya ba duk da ƙara tsanantar yaƙin Gabas ta Tsakiya.
Vladimir Putin ya yi alhinin kisan Ali Khamenei amma bai yi tsokaci kai tsaye kan hare-haren kasashen Amurka da Isra’ila ba.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
