Adadin Mutanen da Aka Kashe a Iran, Isra'ila da Kasashe 7, Amurka Ta Rasa Sojoji 6

Adadin Mutanen da Aka Kashe a Iran, Isra'ila da Kasashe 7, Amurka Ta Rasa Sojoji 6

  • Akalla mutane 1,045 ne suka mutu a kasar Iran sakamakon hare-haren Amurka da Isra'ila, yayin da wannan yaki ya shiga rana ta shida
  • Sojojin Amurka shida sun riga mu gidan gaskiya a kasar Kuwait yayin da mutane 10 suka mutu a Isra'ila sakamakon hare hare daga Iran
  • Legit Hausa ta tattaro adadin mutanen da suka mutu a Gabas ta Tsakiya kamar yadda hukumomin ƙasashen suka tabbatar

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Yayin da yaƙin Gabas ta Tsakiya ya shiga rana ta shida yau Alhamis, alkaluman da hukumomin ƙasashe daban-daban suka fitar sun nuna yadda aka yi asarar rayuka masu yawa tun bayan harin ranar 28 ga Fabrairu.

Ƙasar Iran ce ta fi fuskantar mummunar asara, inda mutane 1,045 suka riga mu gidan gaskiya zuwa yanzu.

Kara karanta wannan

Yakin Amurka/Isra'ila da Iran: Muhimman abubuwan da suka faru a rana ta 5

Adadin mutanen da aka kashe a Gabas ta Tsakiya ya haura 1,000.
Akwatunan gawa da aka shirya lokacin jana'izar dalibai mata da hare-haren Amurka/Isra'ila suka kashe a Iran ranar 28 ga Fabrairu, 2026. Hoto: Handout/Getty Images
Source: Getty Images

Cikin wannan adadi, akwai ƴan makarantar firamari 175 da malamansu waɗanda makami mai linzami ya fada masu a birnin Minab tun a ranar farko ta yaƙin, in ji rahoton Reuters.

Har yanzu ba a tantance ko dakarun kare juyin juya halin Musulunci (IRGC) suna cikin wannan adadi na mutanen da suka mutu a Iran ba.

Rayukan da aka rasa a Gabas ta Tsakiya

Ga jerin adadin mutanen da suka mutu kamar yadda hukumomin ƙasashe da ƙungiyoyin agaji suka tabbatar:

  • Iran - Mutane 1,045: Adadin ya haɗa da ƴan makaranta 175 da aka kashe a makarantar Minab a ranar farko ta yaƙin.
  • Lebanon - Mutane 77: Ma'aikatar lafiya ta tabbatar da mutuwar su sakamakon hare-haren Isra'ila.
  • Iraƙi - Mutane 13: Sun haɗa da dakarun sa-kai 11, soja guda ɗaya, da farar hula ɗaya.
  • Isra'ila - Mutane 10: Fararen hula ne da makaman Iran suka kashe a kusa da Kudus.
  • Sojojin Amurka - Mutane 6: Sun mutu ne a wani hari da aka kai wani sansani a ƙasar Kuwait.
  • Syria - Mutane 4: Makami mai linzami na Iran ne ya daki wani ginin zaman mutane a birnin Sweida.
  • Kuwait - Mutane 3: Sun haɗa da sojojin ƙasar biyu da aka kashe a harin Iran.
  • UAE -Mutane 3: Ma'aikatar tsaron ƙasar ta tabbatar da mutuwar mutane uku yau.
  • Oman - Mutum 1: Wani makami ne ya daki jirgin ruwa mai ɗaukar mai a gaɓar Muscat, ya yi ajalin mutumin.
  • Bahrain - Mutane 1: Gobarar da ta tashi bayan kakkabo wani makami mai linzami ce ta yi ajalin mutumin.

Kara karanta wannan

Luguden wutar Iran ya jefa Amurkawa cikin tsoro, suna korafi ga Trump

Amurka/Isra'ila na ci gaba da kai hare-hare a Iran da Lebanon
Hayaki na tashi a Beirut bayan harin da Isra'ila ta kai garin a ranar 2 ga Maris, 2026. Hoto: IBRAHIM AMRO / AFP via Getty Images
Source: Getty Images

Sababbin hare-haren Isra'ila a Iran

A jiya Laraba, rundunar sojin Isra'ila ta tsananta kai hare-hare a babban birnin Iran, Tehran, da kuma birni mai tsarki na Qom.

Rahotanni daga Al Jazeera sun nuna cewa bama-baman sun daki yankuna daban-daban har zuwa lardin Isfahan.

Isra'ila ta bayyana cewa hare-haren nata sun nufi gine-ginen dakarun sa-kai na Basij da kuma hedkwatar rundunar tsaro ta cikin gida ta Iran.

Iran ta zafafa hare-hare a Isra'ila

A wani labari, mun ruwaito cewa, dakarun IRGC na Iran sun da cewa sun harba akalla makamai masu linzami guda 40 kan sansanonin Amurka da Isra'ila.

Wata sanarwar dakarun juyin juya halin Musuluncin ta jaddada cewa "guguwar daukar fansa" ba za ta taba kyale wadanda suka kashe 'Jagoran Al'umma' ba.

A daidai lokacin da farashin makamashi ke tashi a fadin duniya, dakarun IRGC sun yi ikirarin cewa suna da "cikakken iko" akan mashigar ruwa ta Hormuz.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com