Iran Ta Ce Ta Kashe Sojojin Amurka 500 a Luguden Wuta da Ta Masu
- Kasar Iran ta ce ta kashe sojojin Amurka a kalla 500 bayan shafe kwana biyar suna gwabza yakin da ya shafi yawancin kasashen Gabas ta Tsakiya
- Babban jami'in gwamnatin Iran, Ali Larijani ne ya bayyana haka, inda ya ce za su cigaba da fafatawa da Amurka/Isra'ila kan harin da suka kai masu
- Iran ta fitar da bayanin ne a daidai lokacin da shugaba Donald Trump ke ikirarin cewa yana samun nasara a hadin gwiwar da ya ke da Isra'ila a yakin
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Iran - Yayin da Amurka ke ikirarin cewa tana samun nasara a yakin da take yi da Iran, Tehran ya sanar da cewa ya kashe sojojin Washington akalla 500.
Ikirarin ya zo ne duk da cewa gwamnatin Trump ta nuna hotunan sojoji hudu da suka mutu a rikicin da ke tsakanin Amurka da Isra’ila da Iran, wanda ya shiga rana ta biyar a ranar Laraba.

Source: Twitter
Iran ta kashe sojojin Amurka 500
Daya daga cikin manyan jami’an tsaron kasar Iran, Ali Larijani, ya yi ikirari a X cewa sun kashe sojojin Amurka 500 a ‘yan kwanakin da suka gabata.
A cikin wani sako da ya wallafa, Larijani ya ce:
“Trump da ya fada tarkon Benjamin Netanyahu, ya jefa al’ummar Amurka cikin wani yaki marar tsari da Iran.
"Ya kamata ya yi lissafi yanzu, idan sama da sojojin Amurka 500 sun mutu cikin ‘yan kwanakin nan, shin har yanzu Amurka yake karewa ko Isra’ila?”
Lajarani ya kuma kara da cewa lamarin bai kare ba, kuma kashe Imam Khamenei ba zai tafi a banza ba, inda ya ce za su dauki fansa.
Maganar Trump kan mutuwar sojojin Amurka
Yayin da ya ke magana kan kashe sojojin Amurka hudu da aka yi a farkon yakin, Shugaba Donald Trump ya bayyana cewa za a iya samun karin mutuwar dakaru a fafatawar da ke.
NDTV ta rahoto ya ce:
“Abin takaici ne, kuma akwai yiwuwar karin mutuwa kafin yakin ya kare. Haka abin yake.”
Wane ne Ali Larijani a kasar Iran?
Ali Larijani yana daga cikin manyan masu tasiri a siyasar Iran, na daga cikin ‘yan tsirarun mutanen da marigayi Ayatollah Ali Khamenei ya amince da su wajen tabbatar da dorewar tsarin mulkin kasar.
Bayan sa'o'i 24 kacal da fara hare-haren Amurka da Isra’ila a kan Tehran, Larijani ya bayyana a talabijin kasar da kafafen sada zumunta inda ya zargi Amurka da Isra’ila da kai harin.
Ya ce:
“Za mu kona zukatansu. Amurkawa marasa kunya za su yi nadamar abin da suka aikata.”

Source: Twitter
A tsawon rayuwarsa ta siyasa wadda ta dauki sama da shekaru 10, Larijani yana da tasiri a tsarin mulkin Iran, kuma gogaggen mai tattaunawa ne da kasashe irin su Rasha, China har ma da Amurka.
Mojtaba Khamenei na raye
A wani labarin, kun ji cewa wasu majiyoyi sun tabbatar da cewa dan marigayi Ayatollah Ali Khamenei mai suna Mojtaba yana nan da rai.
Iran ta sanar da cewa Mojtaba na raye yayin da aka fara rade-radin cewa ya mutu a harin da Amurka/Isra'ila suka kai gidansu.
An fara hasashen cewa zai iya maye gurbin mahaifinsa a matsayin sabon jagoran Iran, lamarin da ya sa hankula komawa kansa.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


