Yakin Amurka/Isra'ila da Iran: Muhimman Abubuwan da Suka Faru a Rana Ta 5

Yakin Amurka/Isra'ila da Iran: Muhimman Abubuwan da Suka Faru a Rana Ta 5

Yaƙin da ake yi tsakanin Amurka/Isra'ila da ƙasar Iran ya shiga rana ta biyar yau Laraba, inda rikicin ya bazu zuwa ƙasashen Lebanon, Iraƙi, da yankin Gulf.

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Rundunar sojin Amurka ta tabbatar da cewa ta nutsar da wani babban jirgin yaƙin Iran a kusa da gaɓar tekun Sri Lanka, inda akalla mutane 80 suka mutu yayin da Iran ta harba makamai masu linzami 40.

Yakin Amurka/Isra'ila da Iran ya shiga rana ta 5, inda aka rasa rayukan fiye da mutane 1,000.
Yadda makamai masu linzami da Iran ta harbo ke sauka a birnin Tel Aviv, kasar Isra'ila. Hoto: MENAHEM KAHANA / Contributor
Source: Getty Images

Kafar watsa labarai ta Aljazeera ta rahoto wasu muhimman abubuwa da suka faru a rana ta biyar ta yakin da ake yi a Gabas ta Tsakiya:

1. Ruwan wuta da barna a Iran

A ɓangaren Iran, Admirol Brad Cooper, shugaban rundunar sojoin Amurka ta CENCOM ya bayyana cewa Tehran ta harba akalla makamai masu linzami 500 da jirage mara matuƙi 2,000.

Kara karanta wannan

Ana tsakiyar musayar wuta, Iran ta yi maganar sulhu da Amurka a rana ta 5

Waɗannan hare-hare sun daki ofishin jakadancin Amurka a Saudi Arabia da kuma kusa da ofishin jakadancin dake Dubai.

Hukumar lura da matattu ta Iran ta tabbatar da cewa mutane 1,045 ne suka mutu sakamakon hare-haren Amurka da Isra'ila zuwa yanzu, in ji rahoton Turkiye Today.

Rahotanni sun kuma nuna cewa an farmaki birane daban-daban ciki har da Tehran, Karaj, da Isfahan inda hayaki ya mamaye sararin samaniya a yau.

2. Halin da ake ciki a Iran da Lebanon

Rikicin ya shafi ƙasashen yankin sosai a yau:

  • Turkiyya: Na'urorin kariya na NATO sun kakkabo wani makami mai linzami na Iran da aka harba zuwa cikin ƙasar Turkiyya. Wannan ya nuna yadda NATO ke shirin kare mambobinta yau.
  • Qatar: An kakkabo wasu makaman a sararin samaniyar Doha, sannan an kama mutane 10 da ake zargi da yi wa dakarun IRGC leƙen asiri, in ji rahoton Gulf News.
  • Lebanon: Isra'ila ta kai hari kan wurare 60 na ƙungiyar Hezbollah, inda aka kashe mutane 50. Gwamnatin Lebanon ta ba da umarnin haramta ayyukan soji na Hezbollah.
  • Oman: Ofishin jakadancin Amurka ya umarci ƴan ƙasarsa da su nemi wurin buya cikin gaggawa saboda fargabar harin ramuwar gayya na Iran.

Kara karanta wannan

Bidiyon yadda wuta ke ci gadan gadan a ofishin Amurka bayan Iran ta kai hari

3. Rigima tsakanin Trump da Birtaniya

Wani babban rarrabuwar kai ya faru a ɓangaren diflomasiyya yau, inda Shugaba Trump ya soki Firayim Ministan Birtaniya, Sir Keir Starmer, in ji rahoton Sky News.

Trump ya ce "Wannan ba Winston Churchill ba ne muke fuskanta," bayan da Starmer ya ƙi amincewa Amurka ta yi amfani da sansanin Diego Garcia domin kai hari kan Iran.

Wannan ya nuna yadda ƙawancen Amurka da Birtaniya yake fuskantar matsi mafi girma a tarihi yau. Biritaniya na fargabar cewa shiga yaƙin zai janyo mata hare-haren ta'addanci a cikin gida.

4. Siyasar gida a Amurka da fargabar yaƙi

Majalisar Amurka na shirin kada kuri'a kan ikon yaki don tantance ko ya cacanta Trump ya ci gaba da farmakar Iran.
Shugaban Amurka, Donald Trump lokacin da ya dura filin jirgin Palm Beach da ke Florida a ranar 27 ga Fabrairu, 2026. Hoto: Mandel NGAN / AFP via Getty Images
Source: Getty Images

A Amurka kuwa, jam'iyyar Democrat ta fara nuna fargabar cewa wannan yaƙi na sama na iya rikida zuwa yaƙin ƙasa, wanda zai iya shafe dogon lokaci ba a gama ba.

Majalisar Dattijai ta Amurka tana shirin kaɗa ƙuri'a kan dokar ikon yaƙi domin tantance ko Trump yana da izinin cigaba da wannan samame ko a'a.

Kara karanta wannan

Magana ta fito: Yadda aka tsara hallaka Khamenei yayin da yake ganawar tsaro

Sakataren Tsaro Pete Hegseth ya ce Amurka na samun nasara a yakin, yayin da Janar Dan Caine ya jaddada cewa za su cigaba da farmakar Iran ba kakkautawa.

Iran ta kashe sojojin Amurka 6

A wani labari, mun ruwaito cewa, sojojin Amurka shida ne aka tabbatar sun mutu sakamakon hare-haren ramuwar gayya da Iran ke kai wa.

Rahotanni sun nuna cewa sojojin da suka mutu suna bakin aiki ne yayin da makaman Iran suka dura kansu a ranar Lahadi bayan fara yaki.

Shugabanni da wasu mutanen Amurka sun nuna damuwa da mutuwar sojojin, yayin da wasu ke sukar gwamnatin Trump kan shiga yaki da Iran.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com