An Samu Matsala: Amurka Ta Yi Wa Iran Babbar Illa a cikin Teku
- Ana ci gaba da fafata yaki mai zafi bayan Amurka da Isra'ila sun kaddamar da hare-hare ta sama kan kasar Iran a yankin Gabas ta tsakiya
- Wani jirgin ruwan yaki na kasar Amurka da ke tafiya a karkashin ruwa ya harba makami mai hadari kan jirgin ruwan yaki na Iran a cikin teku
- Mahukunta sun bayyana cewa an tura masu aikin ceto bayan samun kiran neman daukin gaggawa daga jirgin ruwan da aka harbawa makamin
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Kasar Iran - Wani jirgin ruwan yaƙi na ƙasar Amurka wanda ke tafiya a ƙarƙashin ruwa ya harba makamin torpedo kan jirgin ruwan yakin Iran.
Makamin da aka harba ya nutsar da jirgin ruwan yaƙin Iran a ruwan ƙasa da ƙasa da ke kusa da gaɓar tekun Sri Lanka.

Source: Twitter
Tashar Aljazeera ta kawo rahoton cewa Ministan tsaro na Amurka, Pete Hegseth, ya bayyana hakan yayin ganawa da manema labarai a ranar Laraba, 4 ga watan Maris 2026.
Pete Hegseth ya bayyana cewa wannan harin da aka kai wa jirgin ruwan yaƙin na Iran shi ne irin hari na farko da aka kai wa maƙiyi tun bayan yaƙin duniya na biyu.
Shafin @DeptofWar a X ya sanya bidiyon yadda aka harba makamin da ya nutsar da jirgin ruwan yakin na Iran.
An samu asarar rayuka
Gwamnatin Sri Lanka ta bayyana cewa ta gano gawarwaki da dama sannan ta ceto sojojin ruwa 32 da suka jikkata bayan da jirgin yaƙin na Iran ya nutse a daidai wajen iyakokin ruwan tsibirin.
Mataimakin ministan harkokin wajen ƙasar ya bayyana cewa aƙalla mutane 80 ne aka kashe a wannan harin.
Hukumomi sun bayyana cewa jirgin ruwan yaƙin mai suna IRIS Dena, wanda ke nisan kusan mil 40 (kilomita 75) daga Galle a Kudancin Sri Lanka, ya aika da saƙon neman ɗauki tsakanin ƙarfe 6:00 na safe zuwa 7:00 na safe a ranar Laraba.
Jirgin ruwan yakin Iran na dauke da mutane
Jirgin yana ɗauke da kimanin ma’aikata 180 a cikinsa, kuma ana ci gaba da gudanar da aikin neman mutane da ceton rayuka, in ji jami’an Sri Lanka.
Ministan harkokin wajen Sri Lanka, Vijitha Herath, ya shaida wa majalisar dokoki cewa rundunar sojojin ruwa ta samu labarin cewa jirgin yana cikin mawuyacin hali, kuma gwamnati ta aika da jiragen ruwa da na rundunar sojojin sama domin aikin ceto.
Kakakin rundunar sojojin ruwan Sri Lanka ya ce ba a ga wani jirgin ruwa ko na sama a yankin da jirgin yaƙin na Iran ya nutse ba a lokacin da abin ya faru.

Source: Twitter
Ana gwabza fada tsakanin Amurka da Iran
Nutsar da jirgin ruwan yaƙin ya faru ne a daidai lokacin da Amurka da Isra’ila ke ci gaba da kai hare-hare ta sama kan Iran har tsawon kwanaki biyar, bayan kashe Ali Khamenei da wasu mutane kusan 800, ciki har da ɗumbin ɗalibai mata.
Iran ta mayar da martani da hare-haren jirage marasa matuƙi da makamai masu linzami kan Isra’ila da sansanonin sojojin Amurka a ƙasashen Gabas ta Tsakiya, wanda ya yi sanadiyar mace-mace da dama.
Sojojin Amurka shida ne aka kashe yayin da wasu da dama suka jikkata.
Amurka ta yi asara a yaki da Iran
A wani labarin kuma, kun ji cewa kasar Amurka ta tafka asara bayan fara yakin da ta yi da Iran tare da hadin gwiwar Isra'ila.
Amurka ta yi asarar kusan Dala biliyan biyu na kayan aikin soja tun bayan da rikici ya barke tsakaninta da Iran.
Hare-haren ramuwar gayya da Iran ta kaddamar sun janyo babbar asara ga kadarorin sojojon Amurka a yankin Gabas ta Tsakiya.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


