Bidiyon yadda Makamin Iran Ya Ratsa Garkuwar Isra'ila, Ya Tafka Barna a Tel Aviv

Bidiyon yadda Makamin Iran Ya Ratsa Garkuwar Isra'ila, Ya Tafka Barna a Tel Aviv

  • Makamai masu linzami na kasar Iran sun ratsa garkuwar Iron Dome da kasar Isra'ila take takama da ita, tare da fadawa a Tel Aviv
  • Wani bidiyo da Legit Hausa ta gani, ya nuna lokacin da makamin Iran ya rika ratsawa ta garkuwar Iron Dome, har ya dura a birnin
  • Sai dai kuma, ita ma Iran na fuskantar hare-haren Amurka da Isra'ila ba kakkautawa, kuma har ta rasa rayukan fiye da mutum 1000

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Isra'ila - Makamai masu linzami da ƙasar Iran ta harba sun yi nasarar ratsa shahararriyar garkuwar tsaron ta Isra'ila wato Iron Dome, inda suka sauka a birnin Tel Aviv.

Wannan hari ya yi sanadiyar mutuwar wata mata, yayin da wasu mutane 20 suka jikkata, kamar yadda rahotanni suka bayyana.

Kara karanta wannan

Ana tsakiyar musayar wuta, Iran ta yi maganar sulhu da Amurka a rana ta 5

Makamin Iran ya ratsa garkuwar tsaron Isra'ila na Irn Dome.
Yadda garkuwar tsaron Isra'ila, watau Iron Dome yake kokari tare wani makamin Iran a saman birnin Tel Aviv a ranar 1 ga Maris, 2026. Hoto: AHMAD GHARABLI / AFP via Getty Images
Source: Getty Images

Bidiyo: Makamin Iran ya ratsa Iron Dome

Kafar watsa labarai ta CBC News, ta wallafa a shafinsa na TikTok cewa ta samu bidiyon yadda makamin Iran ya keta garkuwar Iron Dome, ya daki wani bangare na Tel Aviv a Isra'ila.

CBC ta rahoto cewa:

"Wani bidiyo da wannan kafar watsa labaran ta samu ya nuna yadda makami mai linzami na Iran ya ratsa garkuwar tsaron Iron Dome ta Iran tare da tarwatsewa a Tel Aviv a ranar Asabar."

Kafar watsa labaran ta ce wannan harin ya yi sanadiyar mutuwar mutum daya, kamar yadda rundunar tsaron Isra'ila suka bayyana.

Kalli bidiyon yadda makamin ya ratsa kariyar Iron Dome a kasa:

Hare-haren Iran a Gabas ta Tsakiya

A hannu guda, rundunar sojin Isra'ila ta baza dakarunta zuwa sassa daban-daban na ƙasar domin neman mutanen da gine-gine suka ruguje a kansu.

Wannan hari ya zo ne a matsayin martani ga kashe Ayatollah Khamenei da Amurka da Isra'ila suka yi a ranar Asabar.

Kara karanta wannan

Rana ta 5: Iran ta zafafa hare hare kan Amurka, ta harba makamai masu linzami 40

Ba a Isra'ila kawai harin ya tsaya ba; Iran ta kai farmaki kan sansanonin sojin Amurka dake Gabas ta Tsakiya, har ma da wani babban otal ɗin alfarma mai suna Fairmont Palm dake birnin Dubai.

Hotuna sun nuna hayaki da wuta na tashi daga otal ɗin, inda ake kyautata zaton guntun makamin linzami ne ya faɗa kansa, cewar rahoton Aljazeera.

Makami mai linzami na Iran da ya keta garkuwar tsaron Isra'ila ya kashe wata mata a Tel Aviv.
Yadda garkuwar tsaron Isra'ila, watau Iron Dome yake kokarin tare wani makamin Iran a saman birnin Tel Aviv a ranar 1 ga Maris, 2026. Hoto: AHMAD GHARABLI / AFP via Getty Images
Source: Getty Images

Rugujewar gine-gine a Tehran da Qom

Yayin da yaƙin ya shiga rana ta biyar, jiragen yaƙin Amurka da Isra'ila sun tsananta kai hare-hare a birnin Tehran, Karaj, Isfahan, da kuma birni mai tsarki na Qom.

Kamfanin dillancin labarai na Tasnim ya ruwaito cewa an ji ƙarar fashe-fashe masu ƙarfi a sassa daban-daban na babban birnin Iran, inda gidaje da makarantu suka ruguje.

Zuwa yanzu, adadin mutanen da suka mutu a Iran ya kai 1,045 sakamakon rukunin hare-hare guda 10 da Isra'ila ta kira "Wave 10".

Iran ta harba makamai masu linzami 40

Tun da fari, mun ruwaito cewa, Iran ta bayyana cewa sun harba akalla makamai masu linzami guda 40 wadanda suka nufi sansanonin Amurka da Isra'ila.

Kara karanta wannan

Babbar magana: Yakin kasar Iran da Amurka, Isra'ila ya fara taba 'yan Najeriya

Wannan shi ne rukuni na 17 na hare-haren da Iran ta kai a matsayin martani ne ga kisan gillar da aka yi wa Ayatollah Ali Khamenei, a ranar Asabar.

Sanarwar, wadda aka karanta a gidan talabijin na kasar, ta jaddada cewa "guguwar daukar fansa" ba za ta taba kyale wadanda suka kashe 'Jagoran Al'umma' ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com