Khamenei: An Ɗage Taron Jana'izar Jagoran Addini a Iran yayin da Ake Harin Magajinsa

Khamenei: An Ɗage Taron Jana'izar Jagoran Addini a Iran yayin da Ake Harin Magajinsa

  • Ana ci gaba da jimami tun bayan kisan jagoran addini a Jamhuriyar Musulunci ta Iran, Ayatollah Ali Khamenei a karshen mako
  • Iran ta dage bikin bankwana da Ali Khamenei bayan harin hadin gwiwar Amurka da Isra’ila ya kashe shi tare da iyalansa a Tehran
  • Ministan tsaron Isra’ila, Israel Katz, ya yi barazanar kashe duk wanda aka zaba ya gaji Khamenei, yana mai razana Iraniyawa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Tehran, Iran - Kasar Iran ta sanar da dage bikin bankwana da marigayi Jagoran Addinin Musulunci, Ali Khamenei.

Hakan ya biyo bayan kashe shi a hare-haren hadin gwiwar kasashen Amurka da Isra’ila a Tehran a karshen mako.

An dage taron jana'izar Khamenei a Iran
Marigayi Ayatollah Ali Khamenei. Hoto: @khamenei_ir.
Source: Getty Images

Dalilin dage jana'izar marigayi Ali Khamenei

Rahoton Al Jazeera ya ce an dauki matakin ne saboda matsalolin tsaro da kuma bukatar jama’a daga larduna daban-daban su halarci taron.

Kara karanta wannan

Yaki na kara zafi da Amurka, an ji shirin da Iran take yi na nada magajin Ayatollah Khamenei

Tun farko, shugaban Majalisar Yada Addini ta Iran ya bayyana cewa za a fara bikin ne da karfe 10:00 na dare a masallacin Imam Khomeini.

Ya ce za a bude kofar masallacin na tsawon kwanaki uku domin bai wa al’umma damar halarta da nuna girmamawa ga marigayin.

Rahotanni sun ce ana sa ran taron zai jawo dimbin jama’a, duk da yiwuwar barazanar sababbin hare-hare daga Amurka da Isra’ila kan taron.

Yawan mutane da suka halarci jana'izar 1989

A shekarar 1989, kimanin mutane miliyan 10 ne suka halarci jana’izar Ruhollah Khomeini, wanda ya kafa Jamhuriyar Musulunci bayan juyin juya hali.

Khamenei, wanda ya rasu yana da shekaru 86, ya jagoranci Iran tun 1989 bayan maye gurbin Khomeini a matsayin jagoran koli, cewar The Times of Israel.

Dalilan da suka jawo dage jana'izar Khamenei a Tehran
Jagoran addinin Musulunci a Iran, Ayatollh Ali Khamenei. Hoto: @khamenei_ir.
Source: Twitter

An fara maganar magajin marigayi Khamenei

Babban jagoran na da cikakken iko kan bangarorin gwamnati, sojoji da shari’a, tare da kasancewa jagoran ruhaniya na kasar baki daya.

Malam Ahmad Khatami ya ce kasar na dab da cimma matsaya kan wanda zai gaji Khamenei, duk da yanayin yaki da ake ciki.

Kara karanta wannan

Yadda dan Khamenei da zai iya gadonsa, Mojtaba ya tsallake harin Amurka da Isra'ila

Majalisar Kwararru mai mambobi 88 ke da alhakin zaben sabon jagora, bayan tantance ‘yan takara ta hannun Majalisar Tsaro.

Rahotanni sun nuna cewa Mojtaba Khamenei, dan marigayin, na cikin manyan masu neman kujerar, kuma ya tsira daga hare-haren da aka kai.

A gefe guda, Ministan tsaron Isra’ila, Israel Katz, ya sha alwashin cewa duk wanda aka zaba zai kasance yana daga cikin manufarsu na kawo karshensa.

Isra'ila ta shirya kashe sabon jagoran addin Iran

Mun ba ku labarin cewa Ministan tsaron Isra’ila, Israel Katz ya yi barazana ga sabon Ayatollah, wato jagoran addini da Iran ke shirin nada wa bayan hallaka Ali Khamenei.

Israel Katz ya ce sun yi shiri na musamman domin a kawar da duk sabon shugaban da jamhuriyyar Musulunci ta Iran za ta nada.

Ya jaddada cewa Isra’ila za ta hada kai da Amurka domin lalata karfin Iran yayin da ake ci gaba da samun musayar wuta a tsakanin kasashen uku.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.