Ana tsakiyar Musayar Wuta, Iran Ta Yi Maganar Sulhu da Amurka a Rana Ta 5

Ana tsakiyar Musayar Wuta, Iran Ta Yi Maganar Sulhu da Amurka a Rana Ta 5

  • Gwamnatin Iran ta bayyana cewa ba ta da niyyar tattaunawar sulhu da Amurka kuma za su ci gaba da fafatawa "har illa Masha Allahu"
  • Babban jigon siyasar Iran, Mohammad Mokhber ya ce kasarsa na da karfin ci gaba da wannan yaki, wanda ya shiga rana ta biyar
  • Rundunar sojin Isra'ila ta amince har yanzu kasar Iran tana da karfin makaman linzami duk da barnar da aka yi mata a kwanakin nan

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Iran - Wani babban jigon siyasar Iran, Mohammad Mokhber, ya bayyana cewa ƙasarsa ba ta da niyyar yin kowace irin tattaunawa da Amurka.

Ya jaddada cewa a halin yanzu, babu wani teburin sulhu da Iran za ta iya zauna wa da Amurka, yayin da yakinsu ya shiga rana ta biyar.

Kara karanta wannan

Yaki na kara zafi da Amurka, an ji shirin da Iran take yi na nada magajin Ayatollah Khamenei

Iran ta ce ba za ta yi sulhu da Amurka ba
Ministan harkokin wajen Iran, Abbas Araghchi yana jawabi a wani taro da aka gudanar a Tehran. Hoto: ATTA KENARE / AFP via Getty Images
Source: Getty Images

Iran ta yi maganar sulhu da Amurka

Mohammad Mokhber wanda ya taɓa zama Mataimakin shugaban ƙasa kuma shugaban ƙasa na riƙo, ya jaddada cewa "ba su da wani sauran amana ga Amurkawa," in ji rahoton Aljazeera.

Ya shaida cewa Tehran tana da ƙarfin ci gaba da wannan yaƙi a Gabas ta Tsakiya "muddin muna so," lamarin da ke nufin cewa ba lallai a samu zaman lafiya nan kusa ba.

Wata hukumar gwamnatin Iran, ta sanar a yau cewa adadin mutanen da suka mutu a Iran sakamakon yaƙin da Amurka da Isra'ila ya kai akalla mutane 1,045.

Wannan adadi ya haɗa da gawarwakin da aka tantance kuma aka shirya domin binne su, kamar yadda hukumar ta bayyana.

Majalisar Dinkin Duniya ta soki Amurka

Masana na Majalisar Ɗinkin Duniya sun nuna matuƙar damuwa game da harin da Iran ta ce Amurka da Isra'ila ne suka kai kan wata makarantar ƴan mata a birnin Minab.

Kara karanta wannan

Isra'ila ta fadi wani babba da ta ke shirin hallaka wa a kasar Iran

Harin, wanda aka kai ranar Asabar, ya yi sanadiyar mutuwar akalla yara 165, kamar yadda rahoton Reuters ya nuna.

Kwamitin kare haƙƙin yara na MDD ya fitar da sanarwa yana kiran matakin da "abin bakin ciki," tare da jaddada cewa wajibi ne a kare yara da makarantu daga yaƙe-yaƙe.

Jakadan Iran a Majalisar Ɗinkin Duniya dake Geneva, Ali Bahreini, ya bayyana harin a matsayin "babban laifi" wanda Amurka ta aikata ba tare da wata hujja ba.

Amurka da Isra'ila na ci gaba da kai hare-hare a sassan kasar Iran
Shugaba Donald Trump da Benjamin Netanyahu a fadar White House. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Makaman Iran: Har yanzu da sauran kallo

Duk da cewa Amurka da Isra'ila sun ruguza rumbun makaman Iran da dama, rundunar sojin Isra'ila ta amince cewa har yanzu Iran tana da "gagarumin ƙarfi" na harba makamai masu linzami.

Kakakin rundunar sojin Isra'ila, Birgediya Janar Effie Defrin, ya bayyana cewa sun lalata wuraren harba makamai da dama, amma hakan ba yana nufin Iran ta durkushe ba.

Ya yi gargaɗin cewa koda yake suna da garkuwar kariya, amma "garkuwarmu ba za ta iya tare kowane makami ba," don haka ya yi kira ga mutanensa da su zauna cikin shiri yau.

Kara karanta wannan

Bidiyon yadda wuta ke ci gadan gadan a ofishin Amurka bayan Iran ta kai hari

Iran ta zafafa hare hare kan Amurka

A wani labari, mun ruwaito cewa, dakarun Iran (IRGC) sun sanara da cewa sun harba akalla makamai masu linzami guda 40 wadanda suka nufi sansanonin Amurka da Isra'ila.

Wannan shi ne rukuni na 17 na farmakin da suka kira "Honest Promise 4," wanda martani ne ga kisan gillar da aka yi wa tsohon jagoran addinin kasar, Ayatollah Ali Khamenei.

A daidai lokacin da farashin makamashi ke tashi a fadin duniya sakamakon fadadar yakin, dakarun IRGC sun yi ikirarin cewa suna da "cikakken iko" a kan mashigar ruwa ta Hormuz.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com