Luguden Wutar Iran Ya Jefa Amurkawa cikin Tsoro, Suna Korafi ga Trump
- Amurkawa sun nuna takaici yayin da suka makale a kasashen Gabas ta Tsakiya da Iran ke cigaba da kai hare-hare bayan fara yaki da Isra'ila/Amurka
- Wasu daga cikinsu sun bayyana cewa suna cikin matukar damuwa game da halin da suke ciki, inda suka bukaci taimakon gaggawa daga gwamnati
- Ministan harkokin wajen Amurka ya bayyana cewa 'yan kasar da dama na bukatar a ceto su daga kasashe kuma suna daukar matakan da suka dace
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Qatar - Amurkawan da suka makale a Gabas ta Tsakiya yayin da yaƙi ke ƙara ƙamari a yankin na bayyana takaicinsu da fargaba, yayin da gwamnatin Donald Trump ke ƙoƙarin kwantar musu da hankali.
Gwamnatin ta ce tana duba hanyoyi ceto su ciki har da amfani da jiragen soji da jiragen haya domin kwashe ‘yan ƙasar Amurka da ke Gabas ta Tsakiya.

Source: Getty Images
Wani dan Amurka da ya makale a Gabas ta Tsakiya ya shaidawa tashar CNN cewa yana ji kamar tsuntsun da aka zaunar ana sa ran a harbe shi.
Korafin ya zo ne kwanaki bayan Amurka da Isra’ila sun kaddamar da farmaki kan Iran, lamarin da ya sa Iran ta mayar da martani da kai hare-hare a wasu ƙasashen Gabas ta Tsakiya.
Amurkawa sun makale a kasashen ketare
Gwamnatin Trump na fuskantar suka mai yawa, musamman daga waɗanda suka makale, kan abin da suka ce rashin shirin taimakawa aka yi.
A ranar Talata, shugaban Amurka Donald Trump ya ce ba su da shirin kwashe jama’a kasancewar abubuwan sun faru cikin sauri ba tare da shiri ba.
“Akwai takaici matuka,”
Inji wani Ba’amurke da ke Hadaddiyar Daular Larabawa wanda ke ƙoƙarin barin ƙasar.
Ya kara da cewa:
“Shin mu nufi filin jirgi ne? Ko mu ci gaba da fakewa inda muke? Babu bayani daga gwamnatin Amurka kwata-kwata; suna cewa mu fake a inda muke amma kuma mu nemi jiragen haya, ba a mana gargaɗi ba cewa yaƙi na gab da ɓarkewa.”
Maganar ministan Amurka kan lamarin
Ministan harkokin wajen Amurka, Marco Rubio ya bayyana cewa dubban mutane na neman taimako kuma suna shirin su tallafawa mutanensu, inda ya ce yana da tabbacin za su iya taimaka wa kowane Ba’amurke.
Ya ce:
"Fiye da mutum 1,500 ne suka tuntuɓi gwamnati domin neman taimako,"
Reuters ta ce Rubio ya ce suna cigaba da neman jiragen haya, duba aiki da jiragen soji, da kuma jiragen kasuwanci ta hanyar aiki da kamfanonin jiragen sama domin tura manyan jirage masu kujeru da yawa dauko mutane.

Source: Getty Images
Karin korafin 'yan kasar Amurka
Sai dai ‘yan ƙasar Amurka da suka tuntuɓi ma’aikatar sun ce sun ji takaici kan ƙarancin shawarwarin da suka samu daga gwamnatin Trump.
“Wasa-wasa lamarin ya zama abin takaici,”
Inji Forrest Harrington, Ba’amurken da ya makale a Dubai yayin da yake dawowa Amurka daga tafiyar aiki a da ya je kasar Indiya.
Amurkawa sun makale a Isra'ila
A wani labarin, kun ji cewa gwamnatin Amurka ta yi magana game da 'yan kasarta da suka makale a kasar Isra'ila bayan fara yaki da Iran.
Ofishin jakadancin Amurka ya ce ba zai dauki alhakin dawo da kowa gida ba, inda ya bayyana cewa kowa ya yi ta kan shi domin tsira.
Ya kara da cewa akwai motocin haya da ake shiga domin barin kasar amma ba zai lamuncewa duk wanda ya shiga wata mota samun tsaro ba.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


