Sabon Makirci: Ana Zargin Trump na Shirin Tura 'Yan Ta'adda Su Rikita Iran

Sabon Makirci: Ana Zargin Trump na Shirin Tura 'Yan Ta'adda Su Rikita Iran

  • An fara samun bayanai game da shirin da gwamnatin Amurka ke yi game da Iran yayin da kasashen ke cigaba da fafatawa a fagen daga
  • Wani rahoto ya yi zargin cewa gwamnatin Donald Trump na shirin tura makamai ga wasu kungiyoyi domin tayar da tarzoma a kasar Iran
  • Wasu majiyoyi sun ce tuni tattaunawa ta fara nisa tsakanin Trump da wadanda ya ke so su tayar da bore a kasar domin ruguza gwamnati

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

America - Ana zargin hukumar leƙen asirin Amurka ta CIA na aiki kan wani shiri na bai wa mayakan Kurdawa makamai da nufin tayar da bore a Iran, kamar yadda wasu majiyoyi da suka san da shirin suka shaida.

Majiyoyin sun ce gwamnatin Trump ta shiga tattaunawa kai tsaye da ƙungiyoyin adawa na Iran da shugabannin Kurdawa a Iraq kan yiwuwar ba su tallafin soji.

Kara karanta wannan

Kurji ya fito a wuyan Trump yayin yaki da Iran, ana jefa tambayoyi kan lafiyarsa

Shugaban kasar Amurka, Donald Trump
Shugaban Amurka, Donald Trump a wajen taro. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Tashar CNN ta bayyana cewa wani da ke da alaka da abubuwan da ake tattaunawa da mayakan Kurdawa ne ya sanar da ita halin da ake ciki.

Su wane ne Kurdawa a kasar Iran?

Ƙungiyoyin Kurdawan Iran masu ɗauke da makamai na da dubban mayaƙa da ke aiki a kan iyakar Iraq da Iran, musamman a yankin Kurdistan na Iraq.

Tun bayan fara yaƙin, wasu daga cikin ƙungiyoyin sun fitar da sanarwa a bainar jama’a suna nuni da yiwuwar ɗaukar mataki nan ba da jimawa ba tare da kira ga sojojin Iran da su sauya ɓangare.

Rundunar IRGC ta Iran ta kai hare-hare kan ƙungiyoyin Kurdawa, kuma ta ce ta kai hari da jirage marasa matuƙa da dama kan mayakan Kurdawa a kwanan nan.

Donald Trump: Shirin ta da tarzoma a Iran

An ce Shugaba Donald Trump ya yi waya da shugaban Kurdawan Iran (KDPI), Mustafa Hijri, a cewar wani babban jami’in Kurdawan kasar. KDPI na daga cikin ƙungiyoyin da IRGC ta kai wa hari.

Kara karanta wannan

Yaki ya rincabe a rana ta 4, Iran ta farmaki Amurkawa a Saudiyya

Wani babban jami’in Kurdawan Iran ya shaida cewa ana sa ran dakarun Kurdawa za su shiga wani farmaki ta ƙasa a yammacin Iran cikin kwanaki masu zuwa.

“Muna da babbar dama a yanzu,”

Inji majiyar, tana bayyana dalilin shirin daukar matakin a yanzu, ta kuma ƙara da cewa mayakan na sa ran samun goyon bayan Amurka da Isra’ila.

Rahoton Reuters ya ce Trump ya kira shugabannin Kurdawan Iraq a ranar Lahadi domin tattauna kai farmaki Iran da yadda Amurka da Kurdawa za su yi aiki tare yayin da shirin ke ci gaba.

Shugaba Donald Trump da jami'ansa a ofis
Donald Trump da wasu jami'ansa a Janairun 2026. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Me Trump ke so a Iran?

Wata majiya da ta san tattaunawar ta ce manufar ita ce dakarun Kurdawa su ɗauki nauyin fafatawa da jami’an tsaron Iran domin takaita su.

Ana haka ne fararen hula a manyan biranen Iran za su samu damar fita ba tare da sake fuskantar jami'an tsaro ba kamar yadda ya faru a tarzomar watan Janairun 2026.

Malami ya yi hasashen raba kan Iraniyawa

A wajen tafsirin da ya gabatar a karshen makon jiya, Sheikh Sani Rijiyar Lemu ya yi karin haske game da yadda ake neman raba kan kasar Iran.

Kara karanta wannan

Makaman Iran sun dura babbar matatar mai a Saudiyya, gobara ta tashi

Tun a ranar 11 ga watan Ramadan 1447, Sani Rijiyar Lemu ya yi hasashen za a ayi amfani da Kurdawa da sauran kabilun Iran domin kawo rikicin gida.

Idan aka samu wannan, shehin malamin ya nuna cewa za a iya samun irin abin da ya faru a Libya, matsalar ta kara kamari a kasashen gabas ta tsakiya.

Amurka ta musa kashe Khamenei

A wani labarin, kun ji cewa wani jami'i a Ma'aikatar yakin Amurka ya bayyana cewa ba su da hannu a kashe jagoran Iran, Ayatollah Ali Khamenei.

Ya yi maganar ne a gaban majalisar Amurka a lokacin da ake masa tambayoyi game da hare-haren da shugaba Donald Trump ya ce sun kai Iran.

Jami'in ya ce babu hannun Amurka a kashe Ayatollah Ali Khamenei, inda ya daurawa Isra'ila alhakin kashe shi a harin da ta kai Iran.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng