Yakin Iran Amurka da Isra'ila: Ofishin CIA da ke Saudiyya Ya Sha Wuta

Yakin Iran Amurka da Isra'ila: Ofishin CIA da ke Saudiyya Ya Sha Wuta

  • Yayin da Iran ke ci gaba da kai hare-haren ramuwa a kan kadarorin soji da ofisoshin Amurka da ke sassan Gabas ta Tsakiya
  • Wani jirgi mara matuki ya kai hari zuwa ofishin jami'an leken asiri na CIA da ke ofishin jakadancin Amurka a Saudiyya
  • Wata majiya ta ce ana zargin jirgin Iran ne ya kai harin amma ba a tabbatar da hakan ba yayin da yakin ke ta'azzara

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Kasar Saudia - Rahotanni daga birnin Washington sun nuna cewa an kai hari kan ofishin hukumar leken asirin Amurka, wato 'Central Intelligence Agency' (CIA).

An kai harin da jirgi mara matuki a cikin ofishin jakadancin Amurka a kasar Saudi Arabia yayin da ake ci gaba yakin Iran Amurka da Isra'ila.

Kara karanta wannan

Bidiyon yadda wuta ke ci gadan gadan a ofishin Amurka bayan Iran ta kai hari

An kai hari ofishin CIA a Amurka
Sama ta haska a wani hari da aka kai a baya Hoto: Getty
Source: Getty Images

Reuters ta ruwaito wata majiya da ta san abin da ke faruwa ta shaida wmata cewa ana zargin jirgi mara matukin da ya kai harin na Iran ne.

An zargi Iran ta kai wa Amurka hari

Turkiye Today ta wallafa cewa Majiyar ta bayyana cewa babu wata shaida da ke nuna cewa ofishin CIA din shi ne aka nufa da kai wa harin tsaye.

Sai dai harin ya faru ne a daidai lokacin da ake ci gaba da musayar hare-hare a yankin Gabas ta Tsakiya bayan hare-haren da Amurka da Isra’ila suka kai kan Iran a ranar Asabar.

Ofishin jakadancin Amurka da ke babban birnin Saudiyya, Riyadh, na daga cikin wuraren Amurka ta fuskanci hare-hare tun bayan barkewar rikicin.ssasssssssssssssss5

CIA ta ki cewa komai a kan harin da aka kai ofishinta
Shugaban kasar Amurka Donald Trump Hoto: Donald J Trump
Source: Getty Images

Ma’aikatar tsaron Saudiyya ta ce jirage marasa matuki guda biyu ne suka afkawa ofishin jakadancin, lamarin da ya haddasa karamar gobara da kuma asarar dukiya.

Abin da CIA ta ce kan harin Saudiyya

Kara karanta wannan

Ronaldo ya lallaɓa ya bar Saudiyya saboda rikicin Isra'ila, Iran? an ji gaskiyar zance

Hukumar CIA ba ta ce komai ba dangane da lamarin, inda ta ki yin tsokaci lokacin da aka tuntube ta domin karin bayani.

Bayan harin, ofishin jakadancin Amurka a Saudiyya ya fitar da sanarwar tsaro ga ‘yan kasarsa da ke zaune a yankin.

Sanarwar ta gargade su da su guji zuwa ofishin jakadancin har sai an bayar da wata sanarwa ta gaba.

A ranar Talata, 5 ga watan Maris, 2026 ofishin jakadancin ya soke dukkannin alƙawuran da aka shirya na taimakon ‘yan kasar Amurka.

Hakan ya hada da dakatar da ayyukan ofishin jakadanci da ke kula da harkokin ‘yan kasa a yankin.

Harin Isra'ila ne ya kashe Khamenei - Amurka

A baya, mun wallafa cewa Ma'aikatar yakin Amurka ta yi karin bayani game da kashe jagoran addini na kasar Iran, Ayatollah Ali Khamenei yayin rikici ke rincabewa.

Bayanin da ma'aikatar ta bayar da ya yi daban da ikirarin Shugaban Amurka Donald Trumo da ya ce da tallafin kasarsa Isra'ila ta yi nasarar hallaka Ayatollah Khamenei.

A sabon bayanin da ta yi Amurka ta fadi wadanda ta ce su suka kashe jagoran inda ta ce babu hannunta a cikin harin Isra'ila da ya yi sanadin rasuwar Ayatollah Khamenei.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng