Yaki Ya Yi Zafi; Iran Ta Kashe Sojojin Kasar Amurka bayan Kai Farmaki
- Ana ci gaba da gwabza fada tsakanin Amurka da Iran bayan da aka fara fafatawa a ranar Asabar, 28 ga watan Fabrairun 2026
- A cikin hare-haren da Iran ke kai wa kan sansanonin sojojin Amurka da ke wasu kashen Gabas ta Tsakiya, an kashe dakarun tsaron Amurka
- Majiyoyi sun bayyana cewa harin da Iran ta kai kan sojojin ya jawo an samu asarar dakarun tsaron Amurka da ke aiki a kasar Kuwait
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Kasar Kuwait - Dakarun sojojin Amurka sun rasu sakamakon harin da Iran ta kai ta sama a kasar Kuwait.
Dakarun sojojin sun rasa rayukansu ne sakamakon harin kai-tsaye da Iran ta kai kan wata cibiyar gudanar da ayyuka ta wucin-gadi a wata tashar jiragen ruwa a ƙasar Kuwait a safiyar Lahadi, 1 ga watan Maris 2026.

Source: Twitter
Tashar CNN ta kawo rahoton cewa wata majiya mai masaniya kan lamarin ta tabbatar mata da zancen hallaka sojojin Amurkan.
Kasar Iran ta kashe sojojin Amurka
Adadin mutanen da suka mutu a harin da aka kai a tashar jiragen ruwa ta Shuaiba a kasar Kuwait ya karu zuwa shida.
Rundunar tsaron Amurka ta yankin Gabas ta Tsakiya (CENTCOM) ta sanar a shafinta na X a ranar Litinin, 2 ga watan Maris 2026 cewa adadin ya karu zuwa shida bayan an gano gawarwakin karin dakarun sojoji guda biyu.
A farkon ranar Litinin, Ministan tsaron Amurka Pete Hegseth ya bayyana cewa harin da ya kashe dakarun ya sauka ne a kan wata cibiyar gudanar da dabarun yaki.
Majiyar ta bayyana cewa harin ya bugi tsakiyar ginin ne da misalin ƙarfe 9:00 na safe agogon wurin, inda ta bayyana ginin a matsayin wani babban wuri mai faɗin gaske da ke da ofisoshi a ciki.

Kara karanta wannan
Iran ce ta kakkabo su? Amurka ta yi magana kan jiragen yakinta 3 da suka fado a Kuwait
Harin Iran ya shammaci sojojin Amurka
A cewar majiyar harin ya faru ne cikin sauri ba tare da wani gargaɗi da zai faɗakar da dakarun su fice ko su shiga wurin boyewa ba.
Rundunar CENTCOM da farko ta ce dakarun sojoji uku ne aka kashe amma ba ta bayyana takamaiman inda harin ya auku ba.
A cewar majiyar akwai mutane da dama a wurin, amma dakarun ƙarshe da aka tabbatar da mutuwarsu ba a san inda suke ba lokacin da kurar harin ta lafa.
Waɗannan mutane shida da suka mutu su ne dakarun farko da aka kashe a fafatawar soja da ake yi da Iran wacce aka fara a safiyar ranar Asabar (agogon Amurka), mai taken "Operation Epic Fury"

Source: Facebook
Trump ya hango asarar rayukan sojojin Amurka
Peter Hegseth da Shugaba Donald Trump duka sun bayyana cewa akwai yiwuwar a ƙara samun wasu asarar rayukan.
Kakakin rundunar CENTCOM ya bayyana a ranar Litinin cewa sojoji 18 ne suka samu munanan raunuka a fadan da ake gwabzawa.
Isra'ila ta farmaki garuruwan Iran
A wani labarin kuma, dakarun sojojin Arewa Sojojin Isra’ila sun kaddamar da sabbin hare-hare a biranen Tehran da Beirut na kasashen Iran da Lebanon.
Isra’ila ta ce dakarunta na kasa za su ci gaba da kutsawa cikin Lebanon domin kwace karin muhimman wurare don dakile hare-hare kan iyakarta.
Hare-haren dai na zuwa ne yayin da ake ci gaba da gwabza fada a tsakanin kasashen Amurka, Iran da Isra'ila.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

