Kwana 4 da Fara Musayar Wuta, Amurka Ta Shiga Gagarumar Matsala a Yakinta da Iran
- Amurka ta fara fuskantar karancin wasu makamai, musamman irin wadanda ta yi amfani da su wajen taimakawa Ukraine a yakinta da Rasha
- Daga cikin makaman da aka ruwaito cewa sun fara karanci a wuraren ajiyar Amurka akwai makaman Tomahawk da na kariya SM-3
- Wannan na zuwa ne yayin da aka shiga rana ta hudu da fara musayar wuta tsakanin Amurka/Isra'ila da Jamhuriyar Musulunci ta Iran
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Amurka - Rahotanni sun nuna cewa kasar Amurka ta fara fuskantar matsala game da makamai masu linzami da take amfani da su a yaki da Jamhuriyar Musulunci ta Iran.
Wannan dai na zuwa ne yayin da aka shiga rana ta hudu bayan Amurka da Isra'ila sun yi hadin gwiwa, sun kai munanan hare-hare kan Iran.

Source: Getty Images
Makamai 2 da Amurka ta fara karanci
Tashar TRT World ta Turkiyya ta ruwaito cewa Amurka ta fara fuskantar karancin makamai masu linzami da take amfani da su a wannan yaki.
Daga cikin makaman da suka fara karanci a hannun Amurka har da makaman Tomahawk masu kai hari daga teku zuwa kasa da kuma makaman kariya na SM-3.
Rahoton CNN ya nuna cewa makaman sun kama hanyar karewa ne a yayin da Amurka ke ci gaba da kai hare-haren hadin gwiwar tsakaninta da Isra'ila kan Iran.
Rahoton da aka wallafa, wanda ya nakalto wani babban jami’in Amurka, na cewa Washington na sa ran “karuwar hare-hare sosai” cikin sa’o’i 24 masu zuwa, yayin da makamai masu linzami da na kariya ke raguwa.
Amurka na shirin sake farmakar Iran
Jami’in ya ce zagayen farko na hare-haren ya yi nasarar raunana kariyar Iran, kuma ana sa ran mataki na gaba zai mayar da hankali kan cibiyoyin kera makamai masu linzami na Iran, jiragen yaki marasa matuki da kuma karfin rundunar ruwanta.
Ma’aikatar tsaron Amurka na kuma fuskantar karancin makaman Patriot, saboda ta riga ta yi amfani da galibin wadanda take da su a kokarin taimakawa Ukraine a cikin shekaru hudu na yakin da take yi da Rasha.
Tun daga ranar Asabar, Amurka da Isra’ila suka bayyana cewa sun samu gagarumar nasara a hare-haren da suka kai na hadin gwiwa kan Jamhuriyar Musulunci ta Iran.

Source: Getty Images
Trump ya yi ikirarin kashe jagororin Iran 49
Shugaban Amurka, Donald Trump, ya yi ikirarin cewa an kashe jagororin Iran 49, ciki har da jagoran addini, Ayatollah Ali Khamenei.
Haka kuma, jiragen yaki masu boye kansu na B-2 na Amurka sun kai hare-hare kan wuraren ajiyar makamai masu linzami na Iran a daren Lahadi.
A gefe guda, akalla sojojin Amurka shida sun mutu yayin da 18 suka jikkata matuka tun bayan fara hare-haren ramuwar gayya daga Iran.
Amurka ya gaza kwashe yan kasarta a Isra'ila
A wani rahoton, kun ji cewa ofishin jakadancin Amurka a Isra'ila ya ce ba ya cikin halin da zai iya kwashe ko ya taimaka wa Amurkawa su bar Isra’ila a wannan lokaci.
'Yan Amurka na kokarin barin Isra'ila saboda hare-haren da ke kaiwa, amma kasar ta ce ba za ta dauki alhakin mayar da su gida ba a halin yanzu.
Hakan na zuwa ne yayin da Iran ke cigaba da harba makamai masu linzami a Gabas ta Tsakiya tun bayan harin da Amurka/Isra'ila suka kai mata.
Asali: Legit.ng

