Yaki Ya Yi Kamari, Faransa Ta Tura Jirage UAE da Iran ke kai Hare Hare
- Faransa ta tura jiragen yaki zuwa Gabas ta Tsakiya yayin da Iran ke cigaba da harba makamai masu linzami kan kasashe a yakin da ta ke yi da Amurka/Isra'ila
- Ministan harkokin wajen kasar Faransa, Jean-Noel Barrot ne ya bayyana haka a ranar Talata, 3 ga watan Maris 2026 a wata hira da ya yi da manema labarai
- Rahotanni sun tabbattar da cewa Jean-Noel Barrot ya bayyana abubuwan da jiragen yakin za su a yankin da ke fama da hare-hare tun ranar Asabar da ta wuce
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
France - Gwamnatin Faransa ta shiga yankin Gabas ta tsakiya da jiragen yaki yayin da aka shiga rana ta hudu a yakin Iran da Amurka/Isra'ila.
Ministan harkokin wajen kasar Faransa, Jean-Noel Barrot ya tabbatar da cewa jiragen za su yi shawagi a sararin samaniyar UAE.

Kara karanta wannan
An ji duriyar Firaministan Isra'ila, Netanyahu ana tsaka da rade radin Iran ta tura shi lahira

Source: Getty Images
Tashar France 24 ta wallafa cewa Faransa na da sansanin sojoji daban-daban a kasashen Gabas ta Tsakiya, musamman ma UAE.
Faransa ta tura jiragen yaƙi a UAE
Faransa ta tura jiragen yaƙi na Rafale a sararin samaniyar Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa (UAE) domin kare sansanonin rundunar ruwanta da ta sama daga hare-haren Iran.
Rahoton RFI ya nuna cewa ministan harkokin wajen ƙasar, Jean-Noel Barrot ne ya fitar da sanarwar hakan a ranar Talata, 3 ga Maris 2026.
Faransa na da ɗaruruwan jami’an rundunar ruwa, ta sama da ta ƙasa da ke jibge a Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa. Jiragen yaƙin Rafale nata na ajiye ne a sansanin Dhafra da ke kusa da Abu Dhabi.
“An shirya waɗannan jiragen Rafale tare da matukansu domin tabbatar da tsaron cibiyoyinmu,”
Inji Barrot yayin da yake amsa tambaya kan matakin da Faransa ta ɗauka a karshen mako domin dakile jirage marasa matuƙa na Iran.
Barrot ya ce a ranar Lahadi wani jirgi mara matuƙi ya bugi wani bangare na sansanin Faransa da ke Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa:
“Sun gudanar da ayyuka domin tabbatar da tsaron sararin samaniya a sama da sansanoninmu.”
Matakin da Faransa za ta dauka nan gaba
Ya ƙara da cewa ana ci gaba da tattaunawa domin tantance yadda ƙasar za ta kare kanta daga hare-haren gaba da kuma yadda Faransa za ta kare muradunta a can.
A ranar Asabar ne dai Amurka da Isra’ila suka kai hare-hare kan Iran, inda aka kashe Jagoran Addini na Iran, Ayatollah Ali Khamenei, lamarin ya ya jawo yaki mai zafi.

Source: Getty Images
Babban kamfanin fasaha na Amazon ya ce jirage marasa matuƙa sun bugi cibiyoyinsa biyu na bayanai a Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa kai tsaye wanda hakan ya kawo masa tangarda.
Amurkawa sun makale a Isra'ila
A wani labarin, kun ji cewa Gwamnatin Amurka ta bayyana cewa ba za ta dauki nauyin ceto 'yan kasarta daga Isra'ila zuwa gida ba.
Ofishin Jakadancin Amurka a Isra'ila ya ce akwai tsari fita daga kasar da Tel Aviv ya samar, amma kowa zai iya yanke shawarar shiga tsarin ko akasin haka.
Amurka ta fadi haka ne yayin da jama'a ke tururuwar barin Gabas ta Tsakiya saboda hare-haren da Iran ke kaiwa da makamai daban-daban.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
