An ji Duriyar Firaministan Isra'ila, Netanyahu Ana tsaka da Rade Radin Iran Ta Tura Shi Lahira

An ji Duriyar Firaministan Isra'ila, Netanyahu Ana tsaka da Rade Radin Iran Ta Tura Shi Lahira

  • Benjamin Netanyahu ya bayyana cewa yakin Isra'ila da hadin gwiwar Amurka da ta fara da Iran ba zai dauki dogon lokacin da za a kira shekaru ba
  • Firaministan na Isra'ila ya yi wannan magana ne awanni bayan Iran ta yi ikirarin harba makamai da nufin farmakar ofishin Netanyahu
  • A yau Talata, 3 ga watan Maris, 2026, yakin ya shiga rana ta hudu tun bayan hare-haren farko da Isra'ila, Amurka suka kai da safiyar ranar Asabar da ta wuce

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Isra|'ila - Firaministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu, ya bayyana cewa yana sa ran yaƙin da ake yi da Iran “ba zai ɗauki shekaru ba,” a daidai lokacin da rikicin ke ƙara faɗaɗa.

Kalaman Benjamin Netanyahu na zuwa ne awanni kalilan bayan Iran ta yi ikirarin kai hari ofishinsa da ke Tel Aviv, babban birnin Isra'ila da hedkwatar sojojin kasar ta yahudawa.

Kara karanta wannan

Yaki ya yi kamari, Faransa ta tura jirage UAE da Iran ke kai hare hare

Benjamin Netanyahu.
Firaministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu yana jawabi Hoto: Getty Images
Source: Facebook

Yakin Isra'ila da Iran ya kara fadada

Kafar Reuters ta tattaro cewa yakin da ya barke tsakanin kasashen a ranar Asabar da ta wuce, na ci gaba da fadada, inda Isra’ila ta fara kai wa dakarun Hezbollah hari a Lebanon hari.

Ita kuma Iran na ci gaba da harba makamai zuwa ƙasashen Gulf da ke karɓar baƙuncin sansanonin sojin Amurka a Gabas ta Tsakiya.

A nasa ɓangaren, Shugaban Amurka Donald Trump ya yi hasashen cewa yaƙin zai ɗauki mako huɗu zuwa biyar, amma tun daga lokacin yake ƙoƙarin kare dalilin yin babban yaƙi mai faffadan gaske da Iran.

Firaministan Isra'ila ya tabo batun yaki da Iran

Netanyahu ya yi watsi da ra’ayin cewa rikicin zai yi shekara da shekaru kamar sauran yaƙe-yaƙen da aka yi a yankin a baya.

"Na faɗa cewa yaƙin zai iya zama na gajeren lokaci, zai dauki lokaci amma ba zai shekara ba. Wannan ba yaƙi ne da ba shi da ƙarshe ba," in ji Netanyahu.

Kara karanta wannan

Iran: Amurka ta yi magana kan Najeriya bayan zanga zangar 'yan Shi'a

Firaministan ya yi wadannan kalamai ke a shirin "Hannity" na gidan talabijin na Fox News ranar Litinin, 2 ga watan Maris, 2026.

Halin da ake ciki bayan fara yakin

Yayin da yaƙin ya shiga rana ta huɗu a ranar Talata, ƙarar fashe-fashe ta girgiza gine-gine a faɗin birnin Tel Aviv sakamakon na’urorin kariya na Isra’ila da suka kakkabo makaman linzami da Iran ta harba.

Isra’ila ta kai hari kan rukunin gine-ginen gidan talabijin na gwamnatin Iran (IRIB) da ke Tehran, sannan ta kai wa mayakan Hezbollah hari a garuruwa daban-daban na Lebanon.

Hare-haren sama.
Yadda ake harba makamai masu linzami a sararin samaniya a yakin Iran da Isra'ila Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

A safiyar Talata, wasu jirage marasa matuƙa guda biyu, waɗanda ake kyautata zaton daga Iran suke, sun afka wa ofishin jakadancin Amurka da ke Riyadh na ƙasar Saudiyya, inda suka yi ɓarna tare da haddasa gobara.

Ma'aikatar Tsaron Saudiyya ta ce an kakkabo wasu jirage takwas kafin su ƙaraso cikin birnin na Riyadh.

Isra'ila ta maida jirgin Netanyahu Jamus

A wani rahoton, kun ji cewa Isra’ila ta mayar da jirgin gwamnati zuwa Jamus bayan Iran ta rike wuta wajen kai harin ramuwar gayya ƙasar Yahudawa.

Kara karanta wannan

Yadda harin ramuwar Iran ya tilastawa Isra'ila ɓoye jirgin Netanyahu a Jamus

Mai magana da yawun Firaministan Jamus, Friedrich Merz, ya ce an ba Isra’ila damar ajiye jirgin ne bayan sun nemi hakan a hukumance.

Matakin mayar da jirgin zuwa Jamus na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da tashin hankali tsakanin Isra’ila da Jamhuriyar Musulunci ta Iran.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262