Kurji Ya Fito a Wuyan Trump yayin Yaki da Iran, Ana Jefa Tambayoyi kan Lafiyarsa

Kurji Ya Fito a Wuyan Trump yayin Yaki da Iran, Ana Jefa Tambayoyi kan Lafiyarsa

  • An hango wani kurji a wuyan shugaban kasar Amurka, Donald Trump yayin da ya fito zai gabatar da wani bayani ga 'yan kasarsa a White House
  • Ganin kurjin ya jawo ce-ce-ku-ce, inda aka yi wa fadar White House tambayoyi game da lafiyar shugaban kasar amma bata yi martani ba
  • A wani sako da ya fitar, likita na musamman da ke kula da Donald Trump, Dr Sean Barbabella ya yi magana kan dalilin ganin kurjin a wuyansa

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

America - Manema labarai sun fara tambayoyi game da ganin wani kurji a wuyan shugaban kasar Amurka, Donald Trump yayin wani bayani.

An yi wa fadar White House tambaya game da lafiyar shugaban kasa Trump, amma rahotanni sun nuna bata bayar da amsa kai tsaye ba.

Kara karanta wannan

Yaki ya rincabe a rana ta 4, Iran ta farmaki Amurkawa a Saudiyya

Shugaba Donald Trump bayan kurji ya fita a wuyansa.
Yadda kurji ya fito a wuyan shugaba Donald Trump. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Dalilin fitar kurji a wuyan Donald Trump

CNN ta wallafa cewa likitan Trump na musamman ya ce kurjin da ya bayyana a gefen daman wuyan shugaban kasar ya samo asali ne daga man shafawa da yake amfani da shi domin kare fatarsa.

A wata sanarwa da ya aikewa manema labarai a ranar Litinin, Dr Sean Barbabella ya ce:

“Shugaba Trump na amfani da wani man shafawa da ya saba aiki da shi a gefen dama na wuyansa, wanda ake amfani da shi a matsayin maganin kariya ga fata.
"Zai yi amfani da maganin na tsawon mako guda, kuma ana tsammanin kurjin zai ɗauki wasu makonni kafin ya gushe.”

Sai dai Barbabella bai bayyana dalilin da ya sa Trump ke bukatar wannan maganin ba, kuma Fadar White House ba ta yi martani nan take ba kan tambayoyin da aka yi game da lafiyarsa.

The Guardian ta wallafa cewa an ga kurjin a wuyan shugaban yayin da ya halarci bikin ba da lambar yabo, inda kurjin ya fito sama da wuyan rigarsa a ƙasa da kunnen sa.

Kara karanta wannan

Gaskiya ta fito: Trump ya fadi wasu dalilai 2 da suka sa ya kai hare hare Iran

Magana kan lafiyar Donald Trump

Trump da ke da shekara 79 kuma shugaban ƙasa mafi tsufa da aka rantsar a tarihin Amurka, ya taɓa fuskantar tabo da kumburi a bayan hannayensa biyu, lamarin da ya jawo tambayoyi kan lafiyarsa.

Ya danganta hakan da yawan musabaha da yake yi da kuma yadda yake shan wani magani kullum fiye da yadda aka ba shi shawara, wanda ke sa jikinsa ya yi sauƙin samun tabo.

Shugaban kasa Donald Trump
Donald Trump yana yi wa jama'a bayani. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

A bara ma, Trump ya yi gwaje-gwaje biyu a Cibiyar Kiwon Lafiya ta Sojin Kasa ta Walter Reed, ciki har da wani gwaji da daga baya Dr Barbabella ya ce an dauki hotunan zuciya da jijiyoyi.

Maganar Trump kan hari ofishin Amurka

A wani labarin, kun ji cewa shugaba Donald Trump ya yi magana game da wani hari da Iran ta kai ofishin jakadancin Amurka a Saudiyya.

Kasar Saudiyya ta tabbatar da faruwar harin, inda ta ce wasu jirage marasa matuka ne suka sauka a ofishin kuma sun jawo tashin wuta.

Gwamnatin Amurka ta nuna bacin rai game da harin, inda shugaba Trump ya ce a dakaci martanin da za su yi nan bada dadewa ba.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng